AREWA

AREWA This is my page

Akwai yiwuwar Ministar al'adu Hannatu Musa Musawa, ta rasa mukaminta na Minista, bayan an gano yanzu take yin NYSC.Hukum...
26/08/2023

Akwai yiwuwar Ministar al'adu Hannatu Musa Musawa, ta rasa mukaminta na Minista, bayan an gano yanzu take yin NYSC.

Hukumar NYSC ta bayyana cewa Hannatu Musa Musawa ta saba dokarta na hana masu yin bautar kasa rike mukamin Gwamnati, k**ar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Darektan hulda da jama'a na hukumar ya tabbatar da cewa hukumar za ta dauki mataki a kan laifin da ministar ta yi. Darektan ya tabbatar da cewa yanzu haka ministar tana yin bautar kasarta ne a birnin tarayya Abuja, inda yanzu take cikin wata na takwas.

Yanzu haka an zauna a teburin sulhu tsakanin tawagar ECOWAS da sojojin Nijar game da juyin mulkin kasar.Tsohon shugaban ...
03/08/2023

Yanzu haka an zauna a teburin sulhu tsakanin tawagar ECOWAS da sojojin Nijar game da juyin mulkin kasar.

Tsohon shugaban kasar Najeriya Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmi Muhammad Abubakar Sa'ad, da kuma Alieu Touray, suke jagorantar tawagar sulhun.

Muna Addu'ar Allah yasa sasancin yayi kyau, a kawo karshen wannan rikicin.

Daga karshe dai kungiyar ECOWAS ta tura tawagar sasanci zuwa kasar Nijar.Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Abduls...
02/08/2023

Daga karshe dai kungiyar ECOWAS ta tura tawagar sasanci zuwa kasar Nijar.

Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Abdulsalami Abubakar ne zai jagorantar tawagar, domin tattaunawa da sojojin da s**a kifar da gwamnatin Bazoum.

Yanzu dai ECOWAS ta dakatar da batun yakar sojojin kasar Nijar kenan?

Shugaban ƙasar Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi ga al'ummar ƙasar a daren ranar Litinin.Mai mag...
31/07/2023

Shugaban ƙasar Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai gabatar da jawabi ga al'ummar ƙasar a daren ranar Litinin.

Mai magana da yawun shugaban, Dele Alake ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Litinin, sai dai bai bayyana musabbabin abinda shugaban zai yi jawabi akansa ba.

ECOWAS na shirin kwace mulki da karfin tuwo daga hannun sojoji a NijarKaron farko a tarihi kungiyar ECOWAS na shirin amf...
30/07/2023

ECOWAS na shirin kwace mulki da karfin tuwo daga hannun sojoji a Nijar

Karon farko a tarihi kungiyar ECOWAS na shirin amfani da karfin tuwo wajen kwace gwamnati daga hannun sojojin da s**a yi juyin mulki.

Kungiyar ta ECOWAS ta yi wannan yunkuri bayan juyin mulkin da sojoji s**a yi wa Mohammed Bazoum a matsayin shugaban Nijar.

Sojojin bayan hambarar da gwamnatin Bazoum sun ayyana Janaral Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaba na riko.

Sai dai a wani taron da kungiyar ECOWAS ta gudanar a Abuja babban birnin Nijeriya, ta gindaya wasu matakai a kan sabuwar gwamnatin ta sojoji a Nijar.

Matakan guda 9 sun hada da rufe iyakokin Nijar na sama da na kasa, rufe sarari samaniyar kasar son hana zirga-zirgar jiragen sama da kuma dakatar da duk wasu huldatayya ta kudi tsakanin mambobin ECOWAS da Nijar.

Kazalika, ECOWAS ta rufe asusun ajiya na Nijar da ke a babban asusun kungiyar da dai sauransu.

Yanzu haka masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da s**a yi juyin mulki a kasar Nijar, sun cinnawa ofishin jakadancin Fa...
30/07/2023

Yanzu haka masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da s**a yi juyin mulki a kasar Nijar, sun cinnawa ofishin jakadancin Far*ansa dake birnin Niamey wuta.

A yanzun nan sabuwar Gwamnatin sojojin kasar Nijar ta nemi agajin gaggawa daga kasar Ra*sha, tare da neman kasar Faransa da sauran kasashen Yamma da ke kasar da su tattara su fice daga kasar Nijar cikin gaggawa.

A yanzu haka kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Bola Tinubu, suna gudanar da zama na musamman a Abuja, don bin hanyoyin da s**a dace na ganin sun dawowa da Bazoum mulkin kasar, inda har s**a bawa sojojin kasar wa'adin sati guda domin su gaggauta dawo da mulkin kasar, k**ar yadda s**a same shi.

Akwai abunda ya k**ata mu kara lura sosai musamman a wurin zanga-zangar masu goyon bayan sojojin kasar da s**a gudanar a yau, za kuga talakawan kasar rike da tutotin kasar Ra*sha sannan suna rike da allunan kira ga sojojin kasar da, kada su yarda su kara aminta da kasar Far*ansa.

Hakika hankalina ya fara karkata akan lallai sojojin kasar Nijar da s**a yi juyin mulki ba suda alaka da kasar Faransa, domin koda wasan kwaikwayo ne suke yi mana to lamarin da bazaika haka ba, musammanma yadda naga talakawan kasar masu yawan gaske suke fitowa suna bata lokacin su wurin gudanar da zanga-zangan nuna goyon baya a gare su.

Lallai ya zamar mana dole mu cigaba da yiwa al-ummar Nijar Addu'a, wata kila wannan juyin mulkin ya zama irin na kasar Ma*li.

Allah ka zaunar mana da kasar Nijar lafiya, da Najeriya baki daya.

Yanzu haka da sanyin safiyar nan dubunnan mutanen Nijar ne s**a fito zanga-zanga a kofar dandalin Toumo dake birnin Yama...
30/07/2023

Yanzu haka da sanyin safiyar nan dubunnan mutanen Nijar ne s**a fito zanga-zanga a kofar dandalin Toumo dake birnin Yamai, domin nuna goyon bayansu ga juyin mulkin da sojojin kasar s**a yi.

Me kuka fahimta akan wannan lamarin?

Lamarin Jami'o'in Najeriya Ya Fara Zama Abun TsoroYadda jami'ar Tarayya da ke Jos (UNIJOS) ta karawa sabbin daliban aji ...
29/07/2023

Lamarin Jami'o'in Najeriya Ya Fara Zama Abun Tsoro

Yadda jami'ar Tarayya da ke Jos (UNIJOS) ta karawa sabbin daliban aji daya da DE kudin ragista daga Naira dubu 45,000 zuwa Naira dubu 213,000. Returning Students kuma Naira dubu 160,000.

Idan kuka lissafa za kuga an karawa dalibai kudin ragista da sama da kashi hudu, anya talakan Najeriya zai iya cigaba da karatun jami'a kuwa?

Sannan bashin da ake cewa za'a bawa daliban, na tabbata fiye da kashi 60 na daliban kasar ba za su iya cika sharudan karbar shi ba, saboda tsaurin da aka saka mishi yayi yawa.

✍️ Comr Abba Sani Pantami

Yaki da cin hanci a Kano Barrister Muhuyi Magaji da ke shugabantar yaki da cin hanci a Kano ya k**a mutum 4 bisa zargin ...
29/07/2023

Yaki da cin hanci a Kano

Barrister Muhuyi Magaji da ke shugabantar yaki da cin hanci a Kano ya k**a mutum 4 bisa zargin batan kudi Naira Biliyan 4 a kamfanin samar da kayan noma na jihar Kano, (KASCO)

DCL Hausa

Address


Telephone

+2348133881705

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AREWA:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share