14/08/2025
AREWA NA BUƘATAR MANUFA KAMAR YADDA INYAMURAI DA YARBAWA SUKE DA MANUFA
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
A fahimtata, matakin farko na samun mafita da ci gaba a Arewa shi ne samar wa yankin manufa kamar yadda Yarbawa da Inyamurai suke da manufa.
Yarbawa da Inyamurai ba sa tafiya kara zube irin yadda muke tafiya kara zube a Arewa. A tsarinsu duk shugaban ƙasar da ya zo sai sun ɗauki kundin manufofi da buƙatunsu sun ba shi, amma mu ko shugaban ƙasa za a gani a Arewa sai dai a kai masa s**a da gulmace-gulmacen su wane ba sa sonka ko su wane maƙiyansa ne. Ba wai buƙatun yankin ba.
Ko lokacin da aka yi jin ra'ayin ƙasa kan gyaran kundin tsarin mulki lokacin Jonathan, Yarbawa da Inyamurai sun gabatar da manufofinsu amma mu Arewa ba mu yi hakan ba saboda ba mu da wata manufa a kasa.
Idan muka yi duba da ayyukan tituna da ake mana, Yarbawa da Inyamurai ba za su yarda da irin wannan jinkiri kan ayyukansu ba. Namu ya shafe shekaru 8 ba a iya kammala mana aikin titin Kaduna, Kano, Abuja ba. Ba a kammala aikin ruwa na Baro ba, ba a kammala aikin wuta na Mambila ba. Tare da rufe boda, Yarbawa ba za su yarda da wannan tsari ba.
Amma mu Arewa ba manufa babu haɗin-kai, matasa ba haɗin-kai malamai, ƴan siyasa, sarakuna, duk ba haɗin-kai. Sai hassada, kin juna da rigingimu. Yau a matsayinka na matashi ko kai ne ba ka da manufa ba ka da tsari ba wanda zai kula ka ko ya karɓi abin da kake yi.
Dole idan ana son a ga daidai a Arewa sai an samu haɗin-kai da tsari, da manufa da kuma jagora wanda in ya ce a yi Gabas za a yi gabas, in ya ce a yi Yamma za a yi Yamma, in ya ce a yi Kudu za a yi Kudu, in ya ce a yi Arewa za a yi Arewa, kamar yadda Yarbawa suke da hakan.