21/09/2025
Ita Wannan Fitalar Da Kuke Gani, Allah Ne Mahaliccinsa Ya Gwangwaje Shi Da Ita, Don Shima Ya More Rayuwarsa, A Cikin Zurfin Teku Inda Ba'a Bawa Haske Ikon Isa Wurin Ba.
A can ƙasan zurfin teku mai duhu, yankin da ake kira midnight zone, tsakanin 200m – 2,000m, akwai wani kifi mai ban mamaki, da ake kira anglerfish.
Kamar yadda kuke gani a saman kansa yana ɗauke da yar fitilarsa gwanin sha'awa, kai kace, irin fitilar nan ce ta masu tono ma'adanai a ƙarƙashin ƙasa. Amma kuma ba ita bace, wannan fitila ce ta musamman daga ubangijin haske, ya samarwa wannan kifi na anglerfish domin ya samu sauƙin rayuwar da zata dace da bigiren da aka ajiye shi.
Sai dai wannan hasken ba yana fitowa kai tsaye daga jikinsa bane, wasu ƙananan ƙwayoyin bacteria da ke rayuwa a cikin wata yar jaka dake ɗeshin kan tsinken fitilar suke samar da hasken cikin wani yanayi na fahimtar juna dake wanzuwa tsakin kifin dasu ƙwayoyin bacteria ɗin, Eh mana hakan dai nake nufi, Anglerfish ɗin shine yake samar musu da abinci da kuma mafaka, su kuma sai su dinga biyansa ta hanyar samar masa da haske wannan haɗin gwiwa shi ake kira da symbiosis.
To amma amfanin wannan yar fitila mai haske yasha bambam da abinda kake tunani ya zu da kake karanta wannan maƙala, domin kuwa shi ba don ya haskaka hanya ya sayi fitilarsa ba, ya saye ta ne domin ya jawo hankali tare da yaudarar ƙananan kifaye da sauran halittu, domin su kusanto gareshi a zatonsu sun samu abinci ne ko kuma wata mafaka mai aminci.
Amma ina abin ba haka yake ba, wani katon baki ne cike da haƙora masu lanƙwasa ciki, waɗanda ke k**a duk abin da ya kuskura ya kusanto.
Allahu Akbar - kunji yadda mai duka ya tsara wata rayuwa da baka sani ba, to ai dama ya faɗa mana cewa : "yana ma halittar abinda bama sani".
Lallai Mulkin Sarki Allah baida iya cikin faɗin sama da zurfin teku da abinda ke tsakaninsu da wanda ke cikinsu duk na Allah ne kuma yana sane dasu komai ƙanƙantarsa.
Miye ya ɗaure maka kai dangane da wannan kifi mai torchin yaudara ?