11/09/2025
Shettima ya buƙaci a hanzarta rabon tallafin Naira biliyan 250 ga manoma
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya umurci Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Daidaita Harkokin Abinci wato Presidential Food Systems Coordinating Unit (PFSCU) da ya hanzarta rabon tallafin bashin gwamnati na Naira biliyan 250 ga ƙananan manoma.
Shettima ya ce kuɗin za a bayar da su ne ta hannun Bankin Manoma da ruwa mai sauƙi, inda ya jaddada cewa dole a samar da tsari na musamman domin tabbatar da cewa manoman da ake nufi da tsarin, su ne za su amfana da rancen.
Ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a taron kwamitin jagoranci na PFSCU karo na shida da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa.
Shettima ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa matakan da ya ɗauka wajen sassauta harkar sinadaran taki da kafa asusun samar da iri na shugaban ƙasa. Ya ce hakan ya bai wa hukumar PFSCU damar aiki cikin sauri don tallafa wa manoma.
A wajen taron, gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya bukaci a samar da tsari mai inganci domin tabbatar da cewa rancen ya kai ga manoma. Ya kuma ce jiharsa za ta tallafa wa hukumar PFSCU da kuɗi a duk wata.
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yaba da kokarin Bankin Manoma, tare da bayyana cewa akwai buƙatar a ci gaba da tallafa wa manoman cikin gida.
Shi kuwa Gwamnan Cross River, Bassey Otu, ya ce ya dace a ƙarfafawa manoma da karin tallafi da rangwamen kudi.
Ko’odinetan PFSCU, Marion Moon, ta ce hukumar na ci gaba da aiki da hukumomi a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi don karfafa samar da abinci a Najeriya.