Manoma TV.

Manoma TV. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Manoma TV., Media/News Company, Zoo Road, Kano.

04/02/2026

Kiwon Kaji...

Tawagar jami'an gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamnan jihar Malam Umar Namadi suna ci gaba da ziyarar aiki...
04/02/2026

Tawagar jami'an gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin gwamnan jihar Malam Umar Namadi suna ci gaba da ziyarar aikin nemo tsarin noman ciyarwa alfalfa a kasar Argentina, don kyautata noma da kiwo a jihar.

Manufar wannan ziyara itace ƙarfafa samar abinci da bunƙasa ɓangaren kiwo a Jihar Jigawa ta hanyar kafa tsarin samar da ingantaccen abincin dabbobi mai ɗorewa.

04/02/2026

MAHAUTAR ZAMANI

Kuntaba shiga mahautar zamani, inda ake yanka nama da inji? Ku kalli wannan bidiyo.

🎥🎥🎥 DW Hausa

RASHIN INGANTACCEN IRIN SHUKA NA RAGE YAWAN AMFANIN GONA A NAJERIYA - MASANIHarkar noma a Najeriya na ci gaba da fuskant...
24/01/2026

RASHIN INGANTACCEN IRIN SHUKA NA RAGE YAWAN AMFANIN GONA A NAJERIYA - MASANI

Harkar noma a Najeriya na ci gaba da fuskantar koma baya sakamakon yadda manoma da dama ke shuka irin shuka marasa dacewa, saboda rashin samun sahihin bayani, inji wani kwararre a fannin noma.

Daraktan Gudanarwa na Gidauniyar Foundation for Sustainable Smallholders Solutions (FSSS), Isaiah Gabriel, ya ce ci gaba da amfani da irin shuka marasa dacewa na daga cikin manyan matsalolin da ke shafar samar da abinci a ƙasar nan, duk da cewa ana yawan yin watsi da batun.

Gabriel ya bayyana cewa manoman kananan gonaki da dama ba tare da sani ba suna shuka irin da bai dace da nau’in ƙasarsu, yanayin ruwan sama, ko kuma halin sauyin yanayi da ke yankunansu, lamarin da ke haddasa ƙarancin amfanin gona, lalacewar shuka, da asarar kuɗi.

“Manoma da dama a Najeriya har yanzu suna dogaro da tsofaffin irin shuka ko kuma irin da bai dace da yankunansu na noma ba. Hakan ya samo asali ne daga raunin ayyukan jami’an wayar da kan manoma da kuma ƙarancin samun ingantaccen bayani na noma,” in ji shi.

A cewarsa, matsalar ta fi tsananta a tsakanin kananan manoma da su ne ginshiƙin tsarin samar da abinci a Najeriya, amma ba su da isassun damar samun sahihan irin shuka ko shawarwarin kwararru. Ya ƙara da cewa sauyin yanayi ya ƙara tsananta matsalar, domin canjin yanayin ruwan sama da hauhawar zafin rana na buƙatar irin shuka masu jure yanayi.

24/01/2026

The statement quoted the Director-General of the Kebbi State Investment Promotion Agency, Dr. Muhammad Kabir Kamba, as saying that foreign investors from Europe and Asia have already indicated interest in attending the festival, following Governor Idris’ recent overseas engagements.

“We are expecting a large turnout of investors who are keen to explore the state’s abundant natural resources and forge partnerships with the government and people of Kebbi State,” Dr. Kamba said.

Read full story in the comment section!!!

Shettima Ya Yi Kira Da A Farfaɗo Da Kungiyoyin Noma A Makarantu A NajeriyaMataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ...
24/01/2026

Shettima Ya Yi Kira Da A Farfaɗo Da Kungiyoyin Noma A Makarantu A Najeriya

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yi kira da a sake dawo da koyar da noma a matsayin babban darasi tare da farfaɗo da ƙungiyoyin noma a makarantu a faɗin Najeriya, yana mai bayyana hakan a matsayin muhimmin mataki wajen tabbatar da wadatar abinci, ƙarfafa tattalin arziki, da bunƙasa ƙasa gaba ɗaya.

Shettima ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar a Abuja yayin Babban Taron Manoma, inda Babbar Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Kiwon Lafiyar Jama’a, Uju Rochas-Anwukah, ta wakilce shi.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce dole ne noma ya koma makarantu ba kawai a matsayin darasi na ilimi ba, amma a matsayin al’ada da za ta gina tunani da burin matasan Najeriya.

“Dole ne noma ya koma makarantu. Dole ne mu dawo da shi a matsayin al’ada, ba wai a matsayin tsarin karatu kawai ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewa kowace makaranta ya kamata ta mallaki gonaki masu aiki tare da farfaɗo da ƙungiyoyin noma, domin bai wa ɗalibai damar koyon samar da abinci, amfani da ƙasa, da harkokin kasuwancin noma tun suna ƙanana.

“Ya kamata yaranmu su tashi suna sane da cewa abinci arziki ne, ƙasa iko ce, noma kuma kasuwanci ne. Noma ba hukunci ba ne; dama ce,” Shettima ya ƙara da cewa.

KSADP za ta yi wa dabbobi miliyan 5.5 rigakafi a KanoA wani yunkuri na ƙara habbaka samar da dabbobi, Shirin Ci gaban No...
05/01/2026

KSADP za ta yi wa dabbobi miliyan 5.5 rigakafi a Kano

A wani yunkuri na ƙara habbaka samar da dabbobi, Shirin Ci gaban Noma da Kiwo na Jihar Kano (KSADP) ya yi wa dabbobi sama da miliyan 4.5 rigakafi cikin shekaru uku da s**a gabata.

A wata hira da jaridar Daily Trust, shugaban shirin, Ibrahim Garba Muhammad, ya ce burinsu shi ne yi wa dabbobi miliyan 5.5 rigakafi, inda ya bayyana cewa aikin rigakafin na ci gaba da gudana.

Ya ce, “Ban tsammanin akwai wata jiha a wannan ƙasa da za ta yi alfahari da yi wa dabbobi har miliyan 2 rigakafi cikin shekaru uku ba, amma Kano ta yi hakan da ma wasu abubuwa da dama, ciki har da zuba sama da naira biliyan 1 wajen horas da makiyaya kan sarrafa nono.”

Muhammad ya bayyana cewa KSADP ta samar da cibiyar kula da lafiyar dabbobi a sansanin kiwo na Danshosiya, inda aka shuka ciyawar fiddler a fadin hekta 2,000 domin ƙara wadatar abincin dabbobi.

Haka kuma, an bunƙasa wasu hekta 1,000 na ƙasa a wurare 20, inda aka ware hekta 20 a kowanne wuri, domin bai wa ‘yan kasuwa masu harkar samar da ciyawar kiwo.

A ɓangaren ƙara darajar kiwo da samun damar kasuwa, KSADP ta inganta kasuwar Fura da Nono ta Kofar Wambai tare da samar da ɗakin ajiyar sanyi (cold room), wanda fiye da mambobi 3,000 za su amfana da shi.

Haka zalika, an kammala cibiyoyin tara nono guda 98, daga cikinsu 40 suna da cikakken kayan aiki tare da ingantaccen ɗakin ajiyar sanyi.

Manoma TV

Rick Wood captured the north and west faces of 1 WTC as the collapse began. The same man previously seen waving a towel ...
16/11/2025

Rick Wood captured the north and west faces of 1 WTC as the collapse began. The same man previously seen waving a towel from the Windows on the World observation floor 107 is circled in red.

Gwamnatin Tarayya ta ce farashin kayan abinci ya sauka ne sakamakon manufofin karfafa kasuwa da nufin farfado da nomaGwa...
09/11/2025

Gwamnatin Tarayya ta ce farashin kayan abinci ya sauka ne sakamakon manufofin karfafa kasuwa da nufin farfado da noma

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa raguwar farashin kayan abinci da ake gani a kasuwanni a ‘yan kwanakin nan, na da nasaba da manufofi da matakan musamman da aka dauka domin gyara harkar kasuwa da karfafa samar da abinci a cikin gida.

Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a yayin taron majalisar noma ta kasa karo na 47 da aka gudanar a Kaduna, ranar Alhamis 6 ga Nuwamba, 2025.

A cewar ministan, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki alkawarin tabbatar da ikon cin gashin kai a fannin abinci, inda Najeriya za ta rika samar da abincin da take ci, tare da tabbatar da wadatar kayayyaki a farashi mai sauki.

Ya ce, “Mun riga mun fara ganin sakkowar farashin wasu muhimman kayan abinci a kasuwa, wanda hakan ke nuna tasirin matakan da gwamnati ta ke dauka. Ko da yake ba mu kai inda muke so ba tukuna, amma wannan alamar tana tabbatar da cewa muna tafiya a madaidaiciyar hanya.”

Kyari ya bayyana cewa shirin National Agricultural Growth Scheme–Agro-Pocket (NAGS–AP), wanda ake aiwatarwa tare da hadin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka (AfDB) da jihohi, shi ne ginshikin inganta samar da kayayyakin noman da kuma bunkasa amfanin gona.

Ya ce yawan jahohin da ke noma alkama ya karu daga 15 a zangon damina na 2023/2024 zuwa karin jihohi a zangon 2024/2025. Haka kuma, a watan Oktoba da ya gabata, an kaddamar da noman Alkama na rani (rainfed wheat) a Kuru, Jihar Filato, wani sabon salo da Cibiyar Binciken Tafkin Chadi ta kirkiro domin ba da damar noman alkama ba tare da dogaro da ban ruwa ba.

Ministan ya kara da cewa, “Wannan sabuwar fasaha za ta bai wa Najeriya damar yin noman alkama a ko’ina cikin shekara, musamman a yankunan Filato, Taraba da Kuros Riba, wanda zai taimaka wajen cimma burin wadatar alkama a gida.”

Don rage asarar amfanin gona bayan girbi da daidaita farashin kayayyaki, gwamnati ta kaddamar da Nigeria Postharvest Systems Transformation Programme (NiPHaST) tare da Alliance for a Green Revolution in Africa (AGRA).

Kyari ya kuma bayyana cewa gwamnati ta amince da Naira tiriliyan 1.5 domin sake karfafa Bankin Noma (Bank of Agriculture), tare da karin Naira biliyan 250 da za a ware domin tallafawa kananan manoma.

Haka kuma, an kaddamar da shirin national mechanisation programme tare da hadin gwiwar Heifer Nigeria domin taimakawa matasa da mata su kafa cibiyoyin injinan noma a dukkan yankunan kasar.

A nasa bangaren, Karamin Ministan Noma da samar da Abinci, Sanata Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, ya bukaci a rungumi climate-smart agriculture, wato dabarun noma masu jituwa da yanayi domin dorewar samar da abinci.

Ya bayyana wasu muhimman shirye-shirye kamar shirin noman damina mai fadin hekta dubu 500, shirin samar da ruwa ta hasken rana, da kuma “Every Home a Garden” da uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ke jagoranta, domin karfafa noman gida.

A jawabinsa na bude taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce, “A wannan lokaci da muke ciki, batun samar da abinci ya wuce batun manufa kawai, ya koma batun rayuwa da dorewar kasa.”

Ya bayyana cewa karkashin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu, gwamnati ta sanya noma a matsayin jigon tattalin arzikin kasa, ta hanyar inganta sarkar samar da kayayyaki, da sabunta kayan more rayuwa a karkara.

Gwamnan ya ce, a Kaduna, gwamnati ta mayar da noma “ba wai sana’a kawai ba, amma ginshikin cigaba da tushe na walwala.”

Kafin bude taron, ministoci da jami’an ma’aikatar sun kai ziyarar gani da ido zuwa wasu cibiyoyin noma kamar De-Branch Farmers, Afrexim Bank Quality Assurance Centre, Olam Agri, Tomato Jos, da TMDK Agro Park, inda s**a yaba da irin ci gaban da ake samu wajen kirkire-kirkire da samar da ayyukan yi a karkara.

An kammala taron da bayar da lambar yabo ga manoma da ‘yan kasuwa da s**a nuna bajinta a fannin noma da bunkasa abinci a kasar.

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Kano Hon. Abdullahi Abbas Ya Angwance Da Tsaleliyar Sabuwar Amaryarsa A Ya...
17/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Jam'iyyar APC Na Jihar Kano Hon. Abdullahi Abbas Ya Angwance Da Tsaleliyar Sabuwar Amaryarsa A Yau Juma'a

Wane fata kuke yi musu ?

Address

Zoo Road
Kano
700222

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Manoma TV. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Manoma TV.:

Share