Jannat Online TV

Jannat Online TV Domin samun labarai da dumi duminsu ziyarci shafin Jannat Online TV

Mai Girma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Gidaje da Sufuri, His Excellency Engr. Abdullahi Tij...
02/06/2026

Mai Girma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Gidaje da Sufuri, His Excellency Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo, ya kai ziyara ta musamman gidan sahibinsa kuma amininsa,
Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi NIM,
domin gaisuwar Sallah.

A yayin ziyarar, Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya bayyana godiyarsa ga Dr. Baffa Babba Dan’agundi bisa amana, girmamawa da kuma kyakkyawar alakar da yake cigaba da riƙewa a tsakaninsu. Ya yabawa DG ɗin bisa kauna, aminci da biyayya da ya nuna tun farkon haɗuwarsu har zuwa yau.

Tsohon Mataimakin Gwamnan ya kuma gode masa bisa kulawa da yake baiwa ‘yan jam’iyya, ‘yan uwa da abokan arziki, tare da bayyana shi da cewar samun mutum irin Dr. Baffa Babba Dan’agundi babban alheri ne ga al’umma baki ɗaya da kuma jam’iyya. Ya ƙara da cewa yana alfahari da dangantakarsa da Baffan, yana kuma addu’ar Allah Ya tabbatar da wannan zumunci na har abada.

Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya tuna da dadaddiyar alakar dake tsakaninsu, wadda ta samo asali tun daga mahaifin Dr. Baffa Babba Dan’agundi, ta wuce zuwa ga ɗan’uwansa, Sarkin Dawaki Babba Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, har tazo kansa Baffan. Ya bayyana cewa idan har maganar gado ce, to Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya gajeshi.

Yace bai yi mamakin irin girmamawa, biyayya da karamcin da Baffan yake nuna masa ba, domin ya san irin kyakkyawar alakar data kasance tsakaninsa da mahaifinsa da kuma sauran yan uwansa. Haka kuma ya yabawa Dr. Baffa bisa tsayuwa kan akida da ra’ayi tun daga gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau har zuwa yau.

A cewarsa, “Baffa abokin tafiya ne, Baffa ɗan amana ne, Baffa mai alheri ne. Ina yi masa fatan alheri tare da cewa Sky is your limit, Insha Allah. Inda bamu jeba sai kaje, Insha Allah.”

A nasa jawabin, Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana matuƙar godiyarsa ga tsohon Mataimakin Gwamnan, yana mai cewa irin ni’imar da yake ciki a yau ba za'a rasa gudummawar Engr. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo a cikinta ba, domin ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarsa da tafiyarsa ta siyasa.

Dr. Baffa ya jaddada cewa alakar da ke tsakaninsa da T. Gwarzo ta wuce siyasa, domin alaka ce ta mutuntaka, amana da zumunci. Ya bayyana cewa babu wani abu da zai iya raba su, domin dangantakarsu ba ta siyasa kaɗai ba ce.

Ya kuma yi masa fatan alheri tare da sake jaddada biyayyarsa da girmamawarsa gare shi a kowane lokaci, yana addu’ar Allah Ya ƙara ɗorewar wannan kyakkyawar alaka da zumunci a tsakaninsu.

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO THE DG NPC
Tuesday 2nd Jun 2026.

01/06/2026
24/05/2026

Kaji wata jaraba wai ko laumar tuwo kabashi Amana sai yaci

Ashe su Fa'izu Alfindiki fa Andade ana tafka abin kunya 🤣 a cikin Birni

Kaji wata rashin kunya mutumin da ya cinye kudin Islamiyyar gidansu har yanada wata gaskiya da zai fada jama'a su saurar...
22/05/2026

Kaji wata rashin kunya mutumin da ya cinye kudin Islamiyyar gidansu har yanada wata gaskiya da zai fada jama'a su saurare shi ko gani kake mun manta

Address

Kano

Telephone

8135460004

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jannat Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share