
22/07/2025
Jaridar Blueprint ta karrama shugaban Hukumar wasan kwallon kafa ta Abuja F.A, Alhaji Abba Mouktar Mohammed (Mai Nasarar Bwari), da lambar yabo ta 'Sport ICON' sakamakon yadda yake taimaka wa al'umma, musamman matasa tare da basu gudunmawa a bangarori da dama.