12/10/2026
Ya bayyana hakan ne a shafinsa na facebook, inda ya ce ya dakatar da dukkan wani goyon baya da da ya shirya bawa wasu 'yan takarar dake Jam'iyyar APC a baya.
Bisa yadda s**a nuna jin dadinsu kan yadda aka zalunce shi da tawagarsa a gangamin da s**a shirya gudanarwa ranar lahadi a jihar Kano.
"Jama’a assalamu alaikum. Ni Abba Hikima, ina sanar da dakatar da dukkan wani goyon baya da na shirya bawa wasu yan takarar APC a baya. Wannan ya biyo bayan farin ciki da na kula suna yi da zaluncin da ake yiwa mutane daga sama da kuma taimakawa azzaluman. Duk mai taimakon azzaluman shugabannin al’umma azzalumi ne, kuma makiyinmu ne. Allah yayi riko da hannayenmu. Ameen."