G2 Times Media

G2 Times Media A WANNAN SHAFI ZAKU SAMI SAHIHAN LABARAI DA SHIRIN BINCIKE (FACT-CHECKING) CIKIN HARSHEN HAUSA

28/07/2025

Wasu rahotannin na bayyana cewa Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi musu yankan rago, daga cikin mutum 56 da s**a yi garkuwa da su sakamakon gaza biyan kuɗin fansa da ƴanbindigar suke nema.

Mutanen da aka kashe ɗin sun kasance ƴan ƙauyen Banga da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar ƙauran Namoda da ke jihar Zamfara.

kafara BBC ta rawaito yadda Shugaban ƙaramar hukumar, Manniru Haidara Ƙaura wanda ya shaida mata yadda al'amarin ya faru, ya ce yawancin waɗanda aka yi wa yankan ragon matasa ne.

"Bayanin da muka samu shi ne sun yi musu yankan rago ne. Abin da ya faru shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa kuma aka harhaɗa aka ba su kamar yadda s**a nema, inda kuma s**a saki mutum 18 da s**a haɗa da mata 17 da ƙaramin yaro guda ɗaya, a ranar Asabar,"in ji Haidara.

Kimanin watanni huɗu ne dai ƴan fashin daji s**a far wa ƙauyan na Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar ta Zamfara inda s**a yi garkuwa da mutum 56.

"Bayanan da s**a zo mana shi ne ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 50 kuma an ba su amma duk da haka s**a zaɓi su kashe mutum 38. Su s**a san dalilin kashe su. Mutane ne da ba su da tunani da ba su da hankali. Sun manta ƴanuwansu ne suke kashewa kuma za mu haɗu a gaban Allah."

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma ƙara da cewa kawo yanzu mutum 16 da s**a dawo da su ranar Asabar na asibiti inda ake kula da lafiyarsu, inda gawar su kuma mutum 38 da aka kashe na wurin ƴanbindigar "kamar yadda s**a saba ai ba sa bayar da ita."

Dangane kuma da abin da ya shafi jami'an tsaro a yankin, Manniru Haidara Ƙaura ya ce duk da a wasu wuraren yana jin labarin irin ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi amma a yankinsa labarin ya sha banban.

"Alal haƙiƙanin gaskiya jami'an tsaro ba sa ba mu irin tallafin da ya kamata mu samu daga ɓagarensu ba ma samu....illa dai askarawa na jihar Zamfara su ne kawai suke taimakon mu."

Jami'an tsaron Najeriya dai musamman sojoji sun sha musanta zarge-zargen da ake yi musu na rashin ka ɗauki a wuraren hare-hare, inda suke cewa jama'a ne ba sa sanar da su da wuri sannan a mafi yawancin lokuta mutane ba su san irin koƙarin da suke yi ba.

Kwamitin zartarwa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda  a matsayin sabon s...
24/07/2025

Kwamitin zartarwa na Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya amince da naɗin Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa.

An haifi Farfesa Yalwanta 8 ga watan Agustan 1968 dan siyasa ne da ya fito daga jihar Filato a Tsakiyar kasar, wanda masani ne a fannin Electrical engineering.

Wanda kafin wannan matsayi shine ministan jinƙai da kare aukuwa bala'oi a Nijeriya.

Wata kotun tarayya a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya ta yanke wa Abubakar Ibrahim G. Fresh hukuncin daurin ...
24/07/2025

Wata kotun tarayya a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya ta yanke wa Abubakar Ibrahim G. Fresh hukuncin daurin wata biyar a gidan gyaran hali ko kuma biyan tarar Naira 200,000, bayan samunsa da laifin wulakanta takardun kudi na Naira.

An gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya mai lamba 1 da ke Kano, bisa zargin watsa takardun kuɗi yayin wata huldar nishadi a shagon Rahama Sa’idu da ke unguwar Tarauni.

Bayan karanta masa tuhumar, G. Fresh ya amsa laifinsa, inda kotun ta yanke hukunci nan take.

22/07/2025

Ko me ya sa Shugaban Ƙasa waɗannan kalamai?

Hukumar dake lura da zirga-zirga ababan hawa ta jihar Kano KAROTA ta ci tarar wani direban motar kurkura da ya take sabb...
21/07/2025

Hukumar dake lura da zirga-zirga ababan hawa ta jihar Kano KAROTA ta ci tarar wani direban motar kurkura da ya take sabbin Shukokin ado da gwamnatin Kano ke yi a tsakiyar tituna domin kawata birnin.

Wannan na cikin wata sanarwa da ta fito daga hukumar wadda ta ce hukumar ta ci tarar direban ne bisa umarnin Kwamishinan Muhalli na jihar Kano, Dr. Dahiru M. Hashim, tare da tilasta masa ya maye gurbin bishiyun da ya lalata.

Mataimakin shugaban hukumar, Auwal Aranposu, ya yi gargaɗi ga direban da masu amfani da ababan hawa a jihar da su kiyaye dokokin muhalli domin kauce wa hukunci.

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci a dauki matakai masu tsauri kan masu aikata cin zarafin mata a Jihar Kano, y...
21/07/2025

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci a dauki matakai masu tsauri kan masu aikata cin zarafin mata a Jihar Kano, yana mai cewa babu musulmi nagari da ke dukan matarsa.

Muhammadu Sanusi ya yi wannan kiran ne a yau Litinin yayin da ya karɓi tawagar cibiyar bincike da aiwatar da aiyukan ci bgaba (DRPC) da kuma Cibiyar Musulunci da Tattaunawar Addinai ta Jami’ar Bayero (CICID) a fadarsa da ke Kano.

Khalifan na Tijjaniyya ya koka kan yadda laifukan fyade da na dukan mata daga mazajensu ke kara yawaita a jihar, yana mai cewa malamai da limamai na da rawar da za su taka wajen sauya dabi’un al’umma domin kawo karshen wannan barna.

A cewar Sarkin: “Ni ban yarda da dukan mace ba kuma wadanda suke yi ba don gyara suke yi ba. Abin da muke gani yanzu shi ne duka mai tsanani da jikkata mata da sunan gyara.

"Addinin Musulunci ya girmama mata fiye da kowanne addini, kuma duk wanda ke fakewa da addini domin cin zarafi ko dukan mace, bai fahimci addinin ba.

"Duk wanda ke dukan matarsa har ya jikkata ta, ba mutum nagari ba ne. Ni ban fada ba, Annabi Muhammadu (SAW) ne ya fada. Masu karatu ne kadai za su fahimta," in ji Sarkin.

Wani matashin Dan siyasa a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ya yi mafarki Peter Obi ya zama shugaban Nijeri...
21/07/2025

Wani matashin Dan siyasa a Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ya yi mafarki Peter Obi ya zama shugaban Nijeriya a kakar zaben 2027.

Matashin mai suna Dr. Bello Sulaiman Kano, ya bayyana mafarkin matsayin wani mabuɗi ga al'ummar Nijeriya don su fahimci hanya da zata bulle samu a zaɓen dake tafe.

Yace: "Nayi mafarki Peter Obi ya zama shugaban ƙasa saboda haka ya kamata kowa ya shiga OBIDIENT movement kafin lokaci ya ƙure."

NNPP Kwankwasiya PDP Governors' Forum

16/07/2025

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP.

Hakan na kunshe ne cikin wata Wasika da ya sanyawa hannu da kansa kuma aka aikawa Shugaban jam’iyyar PDP na mazabarsa ta Jada dake jihar Adamawa.

Ya ce ya fice daga jam’iyyar ne saboda mawuyacin halin da take cikin na rashin Tabbas.

Ya godewa Shugabannin jam’iyyar bisa gudunmawar da s**a ba shi tun lokacin da ya shige tun a shekarun baya.

16/07/2025

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar da ambaliya a kasar Mexico kamar yadda kafar yada labarai ta ta ruwaito.
BBC Hausa TRT Afrika Hausa RFI Hausa DW Hausa Hikima Radio and TV

13/07/2025

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammad ya Rasu

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shi ne mutumin da aka fi ''ɓata wa suna'' a lokacin mulkin tsohon sh...
11/07/2025

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce shi ne mutumin da aka fi ''ɓata wa suna'' a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.

Yayin da yake jawabi a lokacin ƙaddamar a littafin tsohon ministan shari'ar ƙasar, Mohammed Bello Adoke da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, Shettima ya ce Jonathan ya taɓa kawo shawarar cire shi daga muƙaminsa na gwamnan jihar Borno.

Amma sai tsohon ministan ƙasar, kuma babban lauyan gwamnati, Mohammed Bello Adoke ya ba shi shawarar kauce wa yin hakan.

Shettima ya ce Adoke ya nuna jarumta wajen faɗa wa Jonathan cewa kundin tsarin mulki bai ba shi damar cire ko da zaɓaɓɓen kansila, b***e gwamna sukutum.

Sai dai kuma ina kallon Mataimakin shugaban kasar na wannan kalami ne matsayin shaguɓe ga shugaban kasa Bola Tinubu.

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin aikin da ta ƙudiri aniyar farawa a yau saboda rashin biyan ...
08/07/2025

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin aikin da ta ƙudiri aniyar farawa a yau saboda rashin biyan mambobinta albashin watan Yuni.

Tun da farko ƙungiyar ta yi barazanar daina shiga azuzuwan ɗalibai saboda rashin biyansu albashin watan Yunin da ya gabata.

Ƙungiyar ta bayar da wa'adin cewa idan har ba a biya albashin watan a jiya Litinin ba, to za ta dakatar da shiga azuzuwan ɗalibai.

Jaridar Leadership a ƙasar ta ambato, shugaban ƙungiyar reshen Abuja, Dakta Sylvanus Ugoh na cewa an janye matakin ne saboda tuni gwamnati ta fara biyansu albashi.

“Mambobinmu sun fara samun albashinsu na watan Yuni tun a jiya kafin 12:00 na dare, wanda kuma shi ne wa'adin da muka bayar'', in ji shi.

Address

NO. 80 ALI SHUGABA Street
Kano

Telephone

+2349027620636

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when G2 Times Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to G2 Times Media:

Share