13/04/2026
Fiye da mutane 100 ne s**a rasu rayukansu, mafi yawansu ƴan kasuwa yayin wani harin kuskure da rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar akan kasuwar Jilli da ke kan iyakar Borno da Yobe a arewacin Najeriya.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da mutuwar fiye da mutane 100 a harin na kasuwar mako mako ta Jilli, yayin da wasu ke cewa adadin ya kai 200.
A tattaunawar RFI Hausa da wasu da s**a shaida faruwar lamarin, sun ce a halin yanzu mutanen yankin na cikin mawuyacin hali da kuma fargaba.
Haka zalika, wani da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce harin ya faru ne da tsakar ranar jiya Asabar ana tsaka da cin kasuwa, inda mutane s**a ji saukar bama-bamai kwatsam.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta tabbatar da mutuwar fiye da mutane 100, inda ta yi Allah wadai da wannan hari.
Daraktan Amnesty a Najeriya, Malam Isa Sunusi ya ce abun takaici ne yadda sojojin ƙasar ke kai hari da sunan kuskure, duk da cewa sun sha kai makamancinsa a baya amma basa gyara kuskurensu.
Rundunar sojin saman Najeriya dai ta ce ta yi nasarar halaka ƴan ta’adda a harin da ta kai yankin na Jilli, kodayake ba ta ce komai ma dangane da fararen hular da s**a mutu.
Ba wannan ne karon farko da sojojin Najeriya ke kai makamancin wannan hari ba da suke kira na kuskure, kan fararen hular da basu ji ba basu gani ba.
RFI Hausa