21/09/2025
Idan ma da gaske ne Aliens din ne s**a danno zuwa wannan duniyar tamu, yadda zasu zo haka nan dai zasu gaji su tattara komatsansu su koma, mu yan Nigeria wanne kalar Aliens ne bamu gani ba...
Wasu daga cikin turawan yamma suna can cikinsu su ɗuri ruwa suna ta fargaba sakamakon hango wani katoton sunduki da aka yi wanda ya danno zuwa wannan yankin namu na solar system, ana kyautata zaton zai karaso kusa da Rana (Sun) a ranar 29 ga watan Oktoba 2025, a nisan kimanin kilomita miliyan 203 tsakaninsa da ita rana (Sun) sannan zai karaso kusa da wannan duniyar tamu ta Earth a ranar 19 ga Disamba, 2025, inda zai kasance a tazara mai nisan kilomita miliyan 270, ance ana kyautata zaton shigewa zaiyi, amma wasu masana suna bayyana cewa alamu sunfi nuna cewa zai karaso zuwa cikin wannan duniyar tamu a farkon shekarar 2026...
An fara hango sundukin ne tun a ranar 1 ga watan July 2025, ta cikin wani telescope maisuna ATLAS wanda yake a dakin binciken sararin samaniya na Río Hurtado dake kasar Chile, an lura da cewa Sundukin yana tsala gudun Hypersonic inda yake tafiyar kilometers 58 a duk second daya, an kuma gano yana da girma da fadi wanda yakai tazarar kilomita biyar zuwa shida, masanan sun bayyana cewa an hango alamun ana amfani da ruwa a cikin sundukin har ma da kankara sannan akwai sinadarin Carbon Dioxide tare da sauran sinadaran da aka tabbatar halitta mai jiki ce ke amfani dasu...
A turance suna kiran sundukin da sunan 3I/ATLAS ...
To Madallah ni dai bana tsoronsu idan sunga dama su karaso zuwa duniyar idan sun so suyi zamansu acan sararin samaniya, Allah ya kaimu December lafiya...
Har akwai wani Aliens da zai tsorata yan Nigeria, wanne kalar wahala ce baa gani ba a Nigeria....