20/09/2025
Kungiyar Matasan Arewa Ta Yabi Ministan Tsaro Matawalle Kan Inganta Tsaro a Arewacin Najeriya Da Kasa baki daya.
Kungiyar matasan Arewacin Nijeriya, Northern Youth Concert Citizen, ta bayyana jin daɗinta da salon diflomasiyyar tsaro da Ministan Kasa a Ma’aikatar Tsaro, Dr. Bello Muhammad Matawalle ya bullo da shi, tana mai bayyana shi a matsayin jagoran aiki tukuru ba tare da uzurorin ƙarya ba.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Ibrahim Garba, ya ce ƙoƙarin Ministan wajen samo kayan aiki, fasaha da horo daga ƙasashen waje kamar Turkiyya, China, Pakistan da Amurka, ya kawo gagarumin ci gaba, musamman sabbin jiragen sintiri masu nisan zango don kare ƙasar.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan jagoranci ya dawo da fata da kwarin gwiwa a zukatan matasan Arewa da ke fuskantar matsalolin tsaro, tare da tabbatar da cikakken goyon baya ga Ministan Matawalle bisa jajircewar sa wajen tabbatar da Nijeriya mai tsaro, ƙarfi da ci gaba.