DTR youth vanguard for change

DTR youth vanguard for change � D.T.R Youth Vanguard for Change
Ƙungiyar matasa daga Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado masu kishin kawo sauyi a siyasa da cigaban yankinsu.

Muna goyon bayan shugabanci na gaskiya da haɗin kan al’umma.

22/05/2026

DTR 2027 Hon Ibrahim Maisalla muke fata In Sha Allahu 🤲

Muna mika sakon Barka da Juma’a gaHon Ibrahim Maisalla tare da fatan Allah Maɗaukakin Sarki ya karɓi ibadu, ya ƙara lafi...
22/05/2026

Muna mika sakon Barka da Juma’a ga
Hon Ibrahim Maisalla
tare da fatan Allah Maɗaukakin Sarki ya karɓi ibadu, ya ƙara lafiya, hikima da dacewa.

Allah Ya sanya wannan rana mai albarka ta zama alkhairi gare ka da daukacin al’ummar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado.

Muna addu’ar Allah Ya buɗe maka ƙofofin nasara, Ya sanya ka zama zabin al’umma, kuma Ya baka ikon zama Dan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar waɗannan ƙananan hukumomi cikin nasara da ɗaukaka.

Ya Allah, kasa alkhairi a cikin wannan tafiya ta shugabanci, Ka tabbatar da ita cikin sauƙi, aminci da yardar jama’a.
Ka sanya ya zama jagora mai gaskiya, adalci da tausayi ga al’umma. 🤲

Barka da Juma’a. 🕌

Musa Muhammad Sani ✍️

22/05/2026

Hon Ibrahim Maisalla
Allah yasa muji Alkhairi 🤲

Ya Allah Mai girma, Mai buɗe ƙofofin alheri, Mai ɗaukaka wanda Ka so, muna roƙonKa cikin sunayenKa masu tsarki da rahama...
21/05/2026

Ya Allah Mai girma, Mai buɗe ƙofofin alheri, Mai ɗaukaka wanda Ka so, muna roƙonKa cikin sunayenKa masu tsarki da rahamarKa mara iyaka, Ka dubi bawanka
Hon Ibrahim Maisalla
da idon rahama da dacewa a takarar Majalisar tarayya da yake nema.

Ya Allah Ka sanya masa alkhairi a wannan tafiya ta neman takarar kujerar majalisar tarayya mai wakiltar
Dawakin Tofa,
Tofa
Rimin Gado.

Ya Allah kasa wannan kujera ta zama alkhairi a gare shi da al’ummar DTR, Ka buɗe masa ƙofofinta cikin sauƙi da karɓuwa.
Ka sanya masa soyayya a zukatan jama’a, Ka haɗa masa kalma da goyon baya, Ka nesanta shi daga hassada, sharri da makircin maƙiya.

Ya Allah Ka sanya shi jagora mai tausayi, mai gaskiya, mai riƙon amana, mai tsoronKa a boye da bayyane.

Ka ba shi ikon kare martabar al’umma, taimakon matasa, kula da marasa ƙarfi da cigaban yankunanmu.

Ya Allah Ka albarkaci DTR baki ɗaya, Ka kawo haɗin kai, zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa a tsakanin al’umma.
Ka sanya wannan tafiya ta zama sanadin ci gaba, haɗin kai da ɗaukakar jama’ar mu.

Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad ﷺ, fitilar shiriya, shugaban masu gaskiya da amana.
آمين يا رب العالمين.

Musa Muhammad Sani ✍️

20/05/2026

Hon Ibrahim Maisalla
DTR 2027 DA IZININ ALLAH

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhuSako daga Hon Ibrahim Maisalla  Dan takarar Majalisar tarayya na Dawakin t...
14/05/2026

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu

Sako daga
Hon Ibrahim Maisalla Dan takarar Majalisar tarayya na Dawakin tofa. Tofa. Rimin Gado.

Na taso cikin al’umma, na ga ƙalubalen rayuwar jama’a da idona, kuma na fahimci irin wahalhalun da matasa, mata, manoma da ‘yan kasuwa suke ciki. Wannan ne ya sa na shiga wannan tafiya ta siyasa — ba domin suna ko anfani na kai ba, sai domin hidimtawa al’umma da kawo canji na gaskiya.

A matsayina na ɗan kasuwa kuma mai ayyukan tallafawa al’umma, na yi imani cewa idan aka samu shugabanci nagari mai hangen nesa, za a iya sauya rayuwar jama’a cikin kankanin lokaci.

Kudirina ga al’ummar DTR shi ne:

* Samar da ayyukan yi da damar dogaro da kai ga matasa.
* Bunƙasa noma da samar da ingantattun hanyoyin ban ruwa na zamani
* Tallafawa ƙananan ‘yan kasuwa domin ƙarfafa tattalin arzikin gida.
* Inganta ilimi da kiwon lafiya ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa.
* Gina hanyoyi da samar da ingantaccen tsarin sufuri da kasuwanci.
* Samar da shirye-shiryen ci gaba da za su amfani al’umma na dogon lokaci.

Na yi imani cewa siyasa ba faɗa ba ce, siyasa amanar jama’a ce. Wakilci ba zama a kujera ba ne, wakilci shi ne sauraron koke-koken jama’a da nemo mafita.

Lokaci ya yi da za mu haɗa kai domin gina sabuwar makoma mai cike da ci gaba, adalci da damar rayuwa ga kowa.

Ina kira ga matasa, mata, dattawa da daukacin al’ummar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado da mu haɗa hannu domin gina DTR mai ƙarfi, mai ci gaba, kuma abin alfahari ga kowa.

In sha Allahu, tare za mu kawo cigaba na gaskiya.

Nagode ƙwarai.
Allah Ya albarkaci Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado.
Allah Ya albarkaci Jihar Kano.
Allah Ya albarkaci Najeriya.”

Hon Ibrahim Maisalla DTR In Sha Allah
13/05/2026

Hon Ibrahim Maisalla DTR In Sha Allah

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DTR youth vanguard for change posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share