01/09/2025
Sojojin Najeriya sun ceto mata da yara a Sokoto, sun halaka ‘yan ta’adda a Zamfara
Sojojin OPERATION FANSAN YAMMA (OPFY) sun samu nasarar ceto mutane tara da s**a haɗa da mata uku da yara shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Garin Bature, karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
Rahoton ya ce, aikin ceton ya wakana ne a daren 31 ga Satumba 2025, bayan samun sahihin bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda a kan hanyar Isa–Shinkafi–Kaura Namoda, wadda ke haɗa Jihar Sokoto da Zamfara.
Sojojin sun yi kwanton bauna, sai dai ‘yan ta’addan da zarar sun fahimci kasancewar dakarun, sun yi ƙoƙarin amfani da mutanen da s**a yi garkuwa da su a matsayin garkuwa. Wannan bai yi nasara ba, domin dakarun sun kai musu farmaki inda s**a halaka da dama daga cikinsu, wasu kuma s**a tsere da raunukan harbi.
An garzaya da mutanen da aka kubutar zuwa Asibitin Gwamnati na Shinkafi don samun kulawar lafiya. Bugu da ƙari, sojojin sun kwato bindigar AK-47 ɗaya da majinyoyi biyu masu ɗauke da harsasai 20, babur, wayoyi hannu guda uku da kuma kayan sanye na hamada daga wurin da aka yi kwanton baunar.
An mika waɗanda aka kubutar ga jami’an karamar hukumar Shinkafi, inda aka sha alwashin haɗa su da iyalansu nan gaba kaɗan.
A cikin sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Aikin FANSAN YAMMA, Kyaftin David Adewusi, ya fitar, ya tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da manyan ayyukan soji a Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya har sai an kawar da ta’addanci da ‘yan bindiga baki ɗaya.