
10/10/2025
PRESS RELEASE. 10/10/2025
HISBAH TA KARRAMA SHUGABAN HUKUMAR KAROTA Hon. FAISAL MAHMOUD, SABODA HAZAKAR SA A AIKI...
Hukumar Hisbah ga karrama Shugaban Hukumar kula da zirga zirgar ababan hawa ta jihar kano (KAROTA), Hon. Faisal Mahmoud Kabir, saboda kwazon sa da jajircewa wajen gudanar da ayyuka tare da ingantaccen haɗin gwiwa da hukumar Hisbah da kuma KAROTA.
Babban Kwamandan Hisbah, Mal. Aminu Ibrahim Daura, ne ya mika lambar yabon ta hannun Darakta Janar na hukumar Hisbah.
A cikin jawabin sa, ya bayyana cewa sun lura da yadda KAROTA ke aiki kafada da kafada da Hisbah wajen tabbatar da doka da oda a cikin jahar nan.
Ya kuma yaba da irin kokarin da Shugaban KAROTA yake a kullum, musamman a ranakun Juma’a da Jimma’i wajen tabbatar da tsari a manyan hanyoyi.
A nasa jawabin, Permanent Secretary na Ma’aikatar Sufuri ta jiha, Alhaji Abdulmumini Babani, ya bayyana farin cikinsa da wannan karramawa. Ya ce da ace ba KAROTA aka karrama ba, hakan zai nuna rashin adalci, domin hukumar ta cancanci yabo bisa irin rawar da take takawa wajen inganta harkokin sufuri a jihar Kano.
Shima a nasa jawabin Babban mataimaki na musamman ga gwabna a KAROTA, Alhaji Yahuza Adamu, yankaba ya bayyana cewa wannan karramawa ba ta tsaya ga MD kawai ba, an karrama hukumar KAROTA gaba ɗaya ne bisa jajircewarta da haɗin kai da sauran hukumomi.
Ya yaba da wannan girmamawa tare da jaddada cewa za su ci gaba da aiki tukuru.
A karshe, MD KAROTA, Hon. Faisal Mahmoud Kabir, ya gode wa hukumar Hisba bisa wannan abin kirki, inda ya bayyana cewa akwai kyakkyawar alaƙa mai ƙarfi tsakanin ayyukan KAROTA da na Hisbah, kuma wannan haɗin gwiwar ce ke kawo nasarori masu kyau.
> Daga: Abubakar Ibrahim Sharada Anipr
Jami’in Hulɗa da Jama’a, na KAROTA Kano State.