Lumana Radio International

Lumana Radio International A Broadcast Media Channel page that shares the content of Lumana Radio International, owned by Yakubu Musa Fagge
(1)

04/10/2026

Taron bayyana ayyukan da Sanata Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ofr PhD, ya yi wa Al'ummar yankin Kano ta Kadu.

Taron Ga da Ga da haɗin Giwa da Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa NUJ reshe Jihar Kano.

02/10/2026

Mawuyacin Halin da El-Rufa'i ya Sake Faɗawa a Hannun ICPC...!

02/10/2026

Labarin Lalurar da ta samu El-Rufa'i a Kotu Wannan makon...!

Ma'aikatan gwamnati a faɗin Najeriya sun fara yajin aikin gargaɗi na kwana uku, lamarin da ke ƙara matsin lamba kan gwam...
02/10/2026

Ma'aikatan gwamnati a faɗin Najeriya sun fara yajin aikin gargaɗi na kwana uku, lamarin da ke ƙara matsin lamba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tashin farashin fetur, ƙarancin albashi da kuma tsadar rayuwa.

Yajin aikin, wanda ya fara yau Juma'a, zai ci gaba har zuwa Lahadi. Majalisar Tattaunawa ta Ƙungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati ta Ƙasa (JNPSNC) ce ta kira yajin aikin. Ƙungiyar ta ƙunshi ƙungiyoyin ma'aikatan gwamnati guda takwas, ciki har da ma'aikatan gwamnati, ma'aikatan lafiya, ma’aikatan jinya da ma'aikatan kamfanoni da sauran hukumomin gwamnati.

JNPSNC na cikin gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya, kuma tana aiki tare da manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu na ƙasar, wato NLC da TUC.

Yayin da NLC da TUC ke wakiltar ma'aikata daga sassa daban-daban, JNPSNC ta fi mayar da hankali kan ƙungiyoyin ma'aikatan gwamnati da batutuwan da s**a shafi aikinsu da walwalarsu.

Ƙungiyoyin na neman a rage farashin fetur zuwa naira 500 kan kowace lita, a bai wa ma'aikata tallafin kuɗi domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa, sannan a fara tattaunawa tun da wuri kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.

Shugaban JNPSNC, Kwamared Benjamin Anthony, ya shaida wa BBC cewa ma'aikata na fama da matsananciyar rayuwa sakamakon halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.

Ya ce lokacin da aka fara aiwatar da mafi ƙarancin albashin da ake amfani da shi yanzu, ana sayar da litar fetur kan naira 600, amma a yanzu farashin ya kai naira 1,430. Ya ce farashin ya ninka fiye da sau biyu, abin da ya haifar da gagarumar matsala ga ma'aikata, musamman ganin cewa albashinsu ba ya iya biyan buƙatunsu nay au da kullum.

Anthony ya kuma ce tashin farashin man fetur ya haifar da ƙarin farashin kayan abinci, kuɗin haya da sauran abubuwan buƙatun gida.

Ana sa ran yajin aikin zai iya kawo cikas ga ayyukan gwamnati a faɗin ƙasar, ciki har da ma'aikatu da hukumomin gwamnati a matakan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.

01/10/2026

Su Sarkin Kano Aminu sun Fusata akan Hana su Hawa abar Sunusi...!

01/10/2026

Zazzafan Martanin su Sarkin Kano Aminu akan Hawan da Su ka ce Sunusi Lamiɗo ya yi...!

01/10/2026

Kai Tsaye Jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na Ranar 'Yancin Kai.

Bidiyo daga gidan talabijin na ƙasa NTA.

30/09/2026

Kalaman Gwamna Abba da su ka Tsokano Hayaƙi...!

30/09/2026

Gwamna Abba ya Tsokano Wani Zance da ke Neman Zame Masa Jangwangwan...!

Address

Kano

Telephone

+2348022828280

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lumana Radio International posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category