
26/09/2025
Hukumomin NAIC Da BPP Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Don Ƙara Ƙarfafa Gaskiya A Harkar Noma
Hukumar kula da Inshorar Noma ta Nijeriya NAIC ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya, inganci da kuma karfafa hadin gwiwa da muhimman hukumomin gwamnati domin kare martabar fannin noma a kasar.
Shugaba NAIC, Rt. Hon. Yazeed Shehu Danfulani (Turakin Zamfara), a ranar Alhamis ya jagoranci tawagarsa a ziyarar ban girma zuwa ga Darakta-Janar na Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnati BPP, Dr. Adebowale Adedokun, a Abuja babban birnin Nijeriya.
Ziyarar ta mayar da hankali kan yadda za a karfafa hadin gwiwar hukumomi, inganta gaskiya da bin ka’ida a tsarin saye-saye na gwamnati, tare da nufin bunkasa ingantaccen aiki a tsarin inshorar noma.
Danfulani, tare da rakiyar manyan daraktocin hukumar Rt. Hon. Abubakar Jarengol na ayyuka da fasaha da Mr Ayandayo Babaranti na kudi da gudanarwa ya jaddada kudirin hukumar NAIC na daidaita ayyukanta su zamo tsara a idon duniya.
Ya ce: “A hukumar NAIC mun yi imani cewa hadin gwiwar hukumomi shi ne ginshikin dorewar cigaba. Yin aiki tare da hukumar BPP zai tabbatar da bin ka’ida yadda ya k**ata tare da karfafa gaskiya da adalci, wadannan su ne ginshikan ci gaban inshorar noma a Nijeriya."
A nasa jawabin, Dr. Adedokun ya yaba da irin himmar hukumar NAIC karkashin jagorancin Dr Danfulani wajen tafiyar da ayyuka cikin gaggawa, tare da alkawarin cewa hukumar BPP za ta goyi bayan shirin da ke karfafa shugabanci nagari da tsaftace ayyukan gwamnati.
Ya jaddada cewa irin wadannan hadin gwiwa suna da matukar muhimmanci wajen tafiyar da ajandar gwamnatin Nijeriya ta fadada hanyoyin inganta tattalin arziki, musamman ta fannin noma.
Wannan sabon hadin gwiwar ya zama muhimmin mataki a kokarin NAIC na zurfafa hulda tsakanin hukumomi, karfafa tsarin aikinta da kuma goyon bayan hangen nesa na Gwamnatin Tarayya na tabbatar da shugabanci mai gaskiya kuma mai dorewa.