12/08/2026
Sabon tsarin zai maye gurbin tsarin da ake amfani da shi a baya, wanda ke tilasta wa kamfanoni yin yarjejeniya daban-daban da Gwamnatin Tarayya kafin su fara gudanar da manyan ayyukan hako man fetur da iskar gas.
Ana sa ran sabon tsarin zai taimaka wajen jawo sabbin jarin kuɗi har dala biliyan 50 zuwa fannin mai da iskar gas na Najeriya, tare da farfaɗo da wasu manyan ayyukan hako mai a teku da aka dakatar tsawon shekaru. Daga cikin ayyukan da ake sa ran za su amfana da wannan mataki akwai aikin Bonga South West na kamfanin Shell, wanda darajarsa ta kai kusan dala biliyan 10.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce sabon tsarin zai samar da ƙa’idoji da sharuddan da za su kasance iri ɗaya ga kamfanonin da s**a cancanci zuba jari, maimakon a bar kowane kamfani ya sake yin shawarwari da gwamnati kan nasa yarjejeniyar.
A cewar Onanuga, tsarin da ake amfani da shi a baya ya sanya harkokin zuba jari a ayyukan hako mai da iskar gas daga zurfin teku yin tafiya a hankali, tare da haifar da rashin tabbas, wanda hakan ya sa wasu manyan ayyuka s**a tsaya na tsawon shekaru.
Ya ce matakin na yanzu ya biyo bayan ganawar da Shugaba Tinubu ya yi da Babban Daraktan Kamfanin Shell, Wael Sawan, inda shugaban ya bayar da umarnin samar da hanyoyin da za su buɗe sabon shafin zuba jari a wannan fanni.