Al- Ganza News Hausa

Al- Ganza News Hausa Al-Ganza News Hausa, kafar yaɗa labarai ce da ke samar da sahihan labarai, rahotanni da bayanai cikin harshen Hausa.

Muna aiki da gaskiya, amana da ƙwarewa domin sanarwa, ilmantarwa da wayar da kan al'umma.

Ba Za Mu Janye Kalaman Da Muka Yi Akan Lakurawa Ba, Kuma Ko Kaɗan Ba Mu Yi Nadama Kan Kalaman Ba, Inji GwamnatinnJihar N...
23/07/2026

Ba Za Mu Janye Kalaman Da Muka Yi Akan Lakurawa Ba, Kuma Ko Kaɗan Ba Mu Yi Nadama Kan Kalaman Ba, Inji GwamnatinnJihar Neja

Gwamnatin Jihar Neja ta bakin Babban Darakta mai kula da harkokin Adinai tace babu nadama akan kalaman da Gwamna Umaru Mohammed Bago yayi na s**ar lakurawa.

A yau Alhamis ne Gwamnan ya gana da Komitin Shura na Malamai wanda ya kunshi dukkanin aƙidu dake Jihar a fadar Gwamnati dake Minna, Jim kaɗan bayan ganawar ne Ɗan Jarida Abokin Kowa Nuruddeen Isyaku Daza ya zanta da Sheikh Imam Umar Faruk, Babban Daraktan kula da harkokin Adinai na Jihar.

Da yake bayani Sheikh Umar Faruk yace babu wani kuskure a kalaman Gwamnan kuma ba zasu taɓa janyewa ba, A cewar sa duk Malaman dake ta tsokaci suna s**ar Gwamnan suna yi ne kawai akan rashin adalci da Jahilci. Inda yace k**ata yayi suyi bincike kamin su tsoma baki kuma bama dole bane ace komai Malami ya gani sai yayi tsokaci akai.

Babban Daraktan ya ce Lakurawa sun yi mummunar ɓarna a Masarautar Kagara inda Gwamnan ya kai ziyara da ya haɗa da yiwa Yan ɗarika yankan rago a Masallaci a lokacin da suke yin wazifa.

Sannan yace su a Jihar Neja kan Malaman su a haɗe yake shiyasa basu biyawa shiriritar da ake tayi a Soshiyal Midiya kan batun ba.

Cikakken bayani na nan tafe a DAZA TV da Tsalle Daya !

Wani Matashi Ya Kashè Kansa Ta Hanyar Faɗowa Daga Saman Gadar Gadon Ƙaya Dake Kano.
22/07/2026

Wani Matashi Ya Kashè Kansa Ta Hanyar Faɗowa Daga Saman Gadar Gadon Ƙaya Dake Kano.

Yadda Ake Neman Lamunin Gwamnatin Tarayya Domin Samun Laptop, Wayar Salula da Sauran Na’urorin FasahaGwamnatin Tarayya t...
22/07/2026

Yadda Ake Neman Lamunin Gwamnatin Tarayya Domin Samun Laptop, Wayar Salula da Sauran Na’urorin Fasaha

Gwamnatin Tarayya ta fara karɓar buƙatun neman lamunin sayen na’urorin fasaha ta hanyar sabon shirin Credit for Laptops, Internet, Connectivity and Knowledge Digital Devices (C.L.I.C.K.D.), wanda ke bai wa ‘yan Najeriya damar mallakar laptop, wayar salula (smartphone), tablet da sauran na’urorin dijital ta hanyar biyan kuɗi a hankali.

Shirin na gudana ne ƙarƙashin Nigerian Consumer Credit Corporation (CREDICORP) tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital ta Tarayya.

An ƙaddamar da shirin a Abuja, inda Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital, Dakta Bosun Tijani, tare da Manajan Darakta kuma Babban Jami’in CREDICORP, Uzoma Nwagba, s**a bayyana cewa manufar shirin ita ce bai wa ‘yan Najeriya damar mallakar na’urorin fasaha ba tare da biyan cikakken kuɗinsu lokaci guda ba.

A matakin farko, shirin ya fi mayar da hankali kan kwamfutocin laptop da ake haɗawa a cikin Najeriya domin ƙarfafa masana’antun cikin gida.

Yadda ake neman rancen

Masu sha’awar shiga shirin za su bi waɗannan matakai:

* Ziyarci shafin yanar gizon credicorp.ng/clickd.
* Danna “I’m Interested” domin buɗe fom ɗin neman rancen.
* Cika bayanan da ake buƙata, ciki har da:
* Jihar da kake zaune.
* Matsayinka (ma’aikaci, mai sana’a, ɗan kasuwa, ɗalibi, mai neman aiki ko memban NYSC).
* Adadin kuɗin shiga na wata (idan ana so a saka).
* Shirin horon fasaha da kake ciki, k**ar 3MTT, Andela Learning Community, Learn2Earn, ALX, HNG Internship, AltSchool Africa, Genesys Tech Hub ko wani daban.
* Na’urar da kake son samu (laptop, smartphone, tablet ko wata).
* Dalilin da yasa kake buƙatar na’urar, k**ar karatu, aiki, kasuwanci, shirye-shiryen kwamfuta, ƙirƙirar abubuwan intanet da sauransu.
* Yadda ka samu labarin shirin.

Bayan haka, mai neman lamunin zai tabbatar da cewa bayanan da ya bayar daidai ne, ya amince a tuntube shi game da buƙatarsa, sannan ya ba CREDICORP da abokan hulɗarta izinin tantance cancantarsa kafin ya tura buƙatarsa.

Su waye s**a cancanta a yanzu?

A halin yanzu, matakin farko na shirin ya taƙaita ne ga mambobin shirin Three Million Technical Talent (3MTT) na Gwamnatin Tarayya.

A cewar CREDICORP, an ware laptop 1,000 domin wannan gwaji, inda aka fara rabawa a Abuja tare da bai wa mutum 77 na farko na’urorinsu, yayin da za a ci gaba da rabawa sauran waɗanda s**a cancanta a jihohi daban-daban.

Sai dai fom ɗin neman lamunin ya kuma ba da damar zaɓen wasu shirye-shiryen horaswa irin su ALX, Andela Learning Community, HNG Internship, AltSchool Africa, Learn2Earn da Genesys Tech Hub, abin da ke nuna cewa a nan gaba masu shiga waɗannan shirye-shiryen na iya amfana da tsarin.

Duk Wanda Yake Ganin Dokar Da Na Saka Na Hana Ƙungiyoyi Wa'azin Tayar Da Rikici Bai Yi Masa Ba, To Ya Fitar Ya Bar Min D...
21/07/2026

Duk Wanda Yake Ganin Dokar Da Na Saka Na Hana Ƙungiyoyi Wa'azin Tayar Da Rikici Bai Yi Masa Ba, To Ya Fitar Ya Bar Min Daga Jiha Ta, Kuma Wallahi Duk Wanda Ya Yi Min Rashin Kunya Sa Na K**a Shi, Inji Gwamna Umar Bago Na Jihar Neja.

ICPC ta gayyaci Gbajabiamila kan badakalar hukumar bogi ta PFIPCHukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta yi wa Sh...
20/07/2026

ICPC ta gayyaci Gbajabiamila kan badakalar hukumar bogi ta PFIPC

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta yi wa Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, tambayoyi kan zargin alaƙarsa da badakalar hukumar bunƙasa zuba jari ta kasashen waje (PFIPC), wadda gwamnatin tarayya ta ce ba ta da sahihanci.

Lauyan Gbajabiamila, Jiti Ogunye, ya bayyana cewa ya amsa gayyatar ICPC a ranar Litinin, inda ya ba da bayanansa tare da amsa tambayoyin masu bincike kafin ya koma bakin aikinsa.

A ranar 2 ga Yuli, Shugaba Bola Tinubu ya umarci ICPC ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.

Ana zargin Adeniyi Adeyemi, wanda ake cewa ya jagoranci PFIPC, da ikirarin cewa Gbajabiamila ne ya ba shi takardar naɗi, zargin da shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban kasar ya musanta. Adeyemi ya kuma zargi Gbajabiamila da karɓar Naira miliyan 400 ta hannun wani da kuma neman ƙarin Naira miliyan 200 domin tabbatar da naɗinsa.

Sai dai 'yansanda sun gurfanar da Adeyemi kan zargin jabun takardu da kwaikwayon jami'in gwamnati, tare da k**a shi bayan kotu ta bayar da umarnin cafke shi saboda rashin halartar shari'a. Duk da cewa PFIPC ba ta da wata kafa ta doka, an ce ta yi aiki k**ar hukuma ta gwamnati, har ma aka ware mata kuɗi a kasafin kuɗin 2026.

Gombe 2027: Magoya bayan Bayero Nafada sun ayyana goyon baya ga PantamiWasu jagorori da mambobin tafiyar siyasar tsohon ...
20/07/2026

Gombe 2027: Magoya bayan Bayero Nafada sun ayyana goyon baya ga Pantami

Wasu jagorori da mambobin tafiyar siyasar tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Sanatan Gombe ta Arewa, Bayero Nafada, sun bayyana goyon bayansu ga ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Sun bayyana hakan ne bayan wata ganawa da s**a yi da Pantami, inda s**a jaddada cewa ba za su bi Nafada zuwa jam'iyyar APC ba bayan sauya sheƙarsa.

Jagoran tawagar, Malachi Karfe Kanadi, ya ce sun yanke shawarar ci gaba da kasancewa a jam'iyyar PDP tare da yin aiki domin tabbatar da nasarar Pantami a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Ya ce duk da irin jagorancin da Bayero Nafada ya yi musu tsawon shekaru, sun zaɓi ci gaba da biyayya ga PDP, wadda s**a ce ita ce jam'iyyar da za ta iya samar da ingantaccen shugabanci a jihar.

A nasa jawabin, Farfesa Pantami ya gode musu bisa amincewa da goyon bayan da s**a nuna masa, yana mai alƙawarin gudanar da shugabanci na haɗin kai tare da bai wa kowa dama a cikin harkokin jam'iyyar.

Ya kuma yi kira ga mambobin PDP da su haɗa kai domin ƙarfafa jam'iyyar da kuma ƙwato mulkin Jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027.

Sojoji Sun K**a Wani Ɗan Sudan Da Ake Zargi Da Tà'addanci Tare Da Cafke Masu Haɗa Kai A ISWAP A Arewa Maso GabasDakarun ...
20/07/2026

Sojoji Sun K**a Wani Ɗan Sudan Da Ake Zargi Da Tà'addanci Tare Da Cafke Masu Haɗa Kai A ISWAP A Arewa Maso Gabas

Dakarun Operation HADIN KAI sun k**a wani ɗan ƙasar Sudan da ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci, tare da cafke wasu mutum uku da ake zargi masu haɗa kai da ƙungiyar ISWAP da kuma samar mata da kayan aiki a hare-haren da s**a gudanar a jihohin Borno da Yobe.

Rahotannin ayyukan soji da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya samu a ranar Litinin sun bayyana cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da dakarun s**a samu, wanda ya kai ga gudanar da farmaki a wurare daban-daban na yankin Arewa maso Gabas.

Rahoton ya ce dakarun Bataliya ta 115 sun k**a wani ɗan Sudan mai suna Musa Fashir, mai shekara 32, a yankin Lassa-Dille da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin Fashir na da alaƙa da wasu 'yan ta'adda, lamarin da ya ƙara nuna yiwuwar shigowar mayaƙan ƙasashen waje domin taimaka wa ayyukan ta'addanci a yankin.

Haka kuma, dakarun sun k**a wata mata mai suna Mary Florence, mai shekara 36, wadda ta ce ita baƙuwa ce daga ƙasar Ghana ba tare da takardun izini ba. Jami'an tsaro na ci gaba da bincike domin tabbatar da asalinta da kuma ko tana da wata alaƙa da ayyukan ta'addanci ko wasu laifuka.

A wani samame daban, dakarun Brigade ta 27 tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun k**a wani da ake zargin mai haɗa kai ne da ISWAP a yankin Shishiwaji da ke ƙaramar hukumar Gulani ta jihar Yobe.

Rahoton ya ce ana zargin mutumin mai haƙar ma'adinai ne ba bisa ƙa'ida ba, kuma yana da alaƙa da ISWAP. An k**a shi da wayoyin hannu guda uku.

Har ila yau, yayin sintirin kare manoma a yankin Kasabalari da ke ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, dakaru sun k**a wasu mutum biyu da ake zargin suna samar wa ISWAP kayan aiki.

Kayan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da kekuna biyu, wayar hannu guda ɗaya, katin shaida, magungunan kashe kwari, magunguna, kayan gyaran keke, na'urar hasken rana (solar panel), fitilar hannu da kuma wuƙaƙe.

Jami'an sojin sun bayyana cewa waɗannan nasarori sun nuna yadda amfani da bayanan sirri ke taimakawa wajen dakile shigowar mayaƙan ƙasashen waje, rushe hanyoyin samar da kayan aiki ga 'yan ta'adda da kuma karya cibiyoyin masu mara musu baya a yankin Arewa maso Gabas.

Gwamna Adeleke ka iya shan kayi a zaɓe saboda nuna goyan baya ga Tinubu - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Accord ...
20/07/2026

Gwamna Adeleke ka iya shan kayi a zaɓe saboda nuna goyan baya ga Tinubu - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Accord

Kungiyar Gbenga Hashim Solidarity Movement (GHSM) ta gargadi gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, cewa zai iya fuskantar shan kaye a zaɓen gwamna na 2026 idan ya ci gaba da nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu maimakon fifita muradun jam'iyyarsa.

A cikin wata sanarwa da mai kula da ƙungiyar ta GHSM na Kudu maso Yamma, Alhaji Abass Olaniyi, ya fitar, ƙungiyar ta ce goyon bayan da Adeleke ya bai wa Tinubu ya faru ne tun kafin ya shiga jam'iyyar Accord, don haka bai k**ata a ɗauke shi a matsayin matsayar jam'iyyar ba.

GHSM ta bayyana cewa shugabannin jam'iyyar PDP a Osun sun amince da marawa Tinubu baya a wa'adi na biyu tun a watan Yulin 2025, amma ita ta yi watsi da wannan matsaya saboda ta saɓa da manufofinta.

Ƙungiyar ta kuma ce shugabancin jam'iyyar Accord ne ya gayyaci Dr. Gbenga Olawepo-Hashim ya shiga takarar shugaban ƙasa, inda daga bisani ya zama ɗan takarar jam'iyyar ta hanyar zaɓen fidda gwani kai tsaye.

GHSM ta yi gargaɗin cewa idan ba a mutunta tsarin jam'iyya da yanke shawara tare ba, Accord na iya fuskantar irin matsalolin da s**a raunana PDP. Ta kuma ce shugabannin jam'iyyar a jihohi 24 sun amince da takarar Olawepo-Hashim, yayin da ta ƙi yin ƙarin bayani kan rikicin shari'ar zaɓen fidda gwani da ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Address

Kano

Telephone

+2348106404299

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al- Ganza News Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Al- Ganza News Hausa:

Shortcuts

Share