10/10/2025
Wani Matashi ne ya gama karatunsa na Jami'a inda yayi Degree a fannin Zoology amma ya dade yana ta neman aiki bai samu ba.
Wata rana kawai sai yaga advert ana neman aiki a wani gidan ZOO, sai kawai ya dauki CV dinsa yaje interview, A wajen interview din sai Manager yake gaya masa cewa Gwaggwon birin gidan Zoo din ne ya mutu kuma yanzu ba su da Kudin da zasu siya wani, shine suke neman wanda zai maye gurbinsa, idan ya yarda za'ayi masa shiga irinta ta birin a saka shi a Keji, kuma za'a bashi albashi N200k a wata.
Matashin da yaji albashin da za'a bayar sai yace ya yarda zaiyi........., Washe gari yaje aiki, a ka yi masa shiga irin ta Gwaggwon biri aka saka shi a Keji, ya fito sak kamar birin gaske, yana ta tsalle-tsalle yana hawa kan bishiya yana saukowa........
Yana cikin tsalle-tsallen nan, bai sani ba, har ya fada wani Keji, dubawarsa ke da wuya kawai sai s**ayi Ido biyu da wani Katon Zaki, yana ganin zakin nan kawai ya fara ihu yana neman taimako.
Zakin ya biyoshi a guje ya kamashi ya danne shi a kasa....., yana cikin ihun nan kawai sai yaji Zakin yana masa rada a kunnensa yana cewa "Kai dalla chan yi shiru, ba Zaki bane, nine Abokinka Aliyu, nima aiki na rasa shine nazo na fara wannan last week. Kaga waccen Damisar da take cikin Kejin chan? Ba Damisa bace, Tanko ne Monitan ajinku"😂😂😂