13/05/2026
Lauyan kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju, ya yi Allah-wadai da zargin cire kuɗaɗe daga rabon kuɗin jihohi na FAAC domin tallafawa yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana lamarin a matsayin babban laifi da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Pen Press TV ta rawaito cewa, Adeyanju ya ce sashe na 162 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa kuɗin da ake rabawa jihohi daga Asusun Tarayya mallakin jama’a ne, kuma dole ne a yi amfani da su wajen ci gaban al’umma ba domin muradun siyasa ba.
Lauyan ya ƙara da cewa idan har an karkatar da kuɗaɗen gwamnati domin kamfen, hakan na iya zama karya doka, badaƙalar kuɗi da kuma amfani da ofis wajen cin zarafin dukiyar jama’a. Ya kuma yi kira ga EFCC da ICPC da su gudanar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Sai dai zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban ƙasa ko gwamnatin tarayya da ta tabbatar da zargin da ake yi, yayin da wasu masu goyon bayan gwamnati ke kallon batun a matsayin zargin siyasa da ke bukatar sahihan hujjoji kafin ɗaukar matsaya.
Adeyanju ya jaddada cewa amfani da dukiyar jama’a wajen fafutukar siyasa na iya raunana dimokuraɗiyya da rage amincewar jama’a ga hukumomin gwamnati, yana mai kira da a tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen tafiyar da kuɗin ƙasa.