AMC HAUSA

AMC HAUSA Amon Gaskiya Multimedia Concepts, domin karin bayani Whatsapp 08028934564.

28/09/2026

Dan Gwagwarmaya Abdallah Amdaz ya bayyana dalilin da yasa suke bukatar kawo karshen Gwamnatin APC da shugabanci nagari a Nigeriya.

Jam'iyar PDP ta mika sanarwar shirye zaben cikin gida na kujerar gwamna a gobe Talata a jihar Gombe.
28/09/2026

Jam'iyar PDP ta mika sanarwar shirye zaben cikin gida na kujerar gwamna a gobe Talata a jihar Gombe.

28/09/2026

Kaahi Na 2: Tattaunawa da matahi King Abdul dan TikTok dake wayar da kan masu zabe.

Matakin ya biyo bayan zargin cewa wasu ’yan siyasa na ƙoƙarin amfani da ita wajen haifar da hargitsi da rarrabuwar kai a...
28/09/2026

Matakin ya biyo bayan zargin cewa wasu ’yan siyasa na ƙoƙarin amfani da ita wajen haifar da hargitsi da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar APC ta Kano, musamman a Kano ta Arewa.

Rahotanni sun ce dakatarwar ta danganci wasu kalamai da ayyukan da ake dangantawa da Hajiya Rashida Mai Sa’a, waɗanda ake zargin za su iya haifar da rashin fahimta tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.

Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga Hon. Sh*tu Madaki Kunchi, Mai Magana da Yawun Sanata Barau Jibrin.

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakane a wani sako daga wallafa a shafinsa na Khalin Nertwork. Ku bayyana mana ra'ayinku...
28/09/2026

Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakane a wani sako daga wallafa a shafinsa na Khalin Nertwork.

Ku bayyana mana ra'ayinku a comment section.
I

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar NDC Peter Obi da Mataimakinsa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun ziyarci sarkin musu...
28/09/2026

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar NDC Peter Obi da Mataimakinsa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun ziyarci sarkin musulmi Sa’ad Abubakar na III a fadar sa dake Sokoto.

Fadi ra'ayinka a comment section.

Mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara kan yaɗa labarai, Hon. Ahmed S. Aruwa, ya ce a shirye yake ya sadaukar da duk abin da ...
28/09/2026

Mai ba Gwamnan Jihar Kano shawara kan yaɗa labarai, Hon. Ahmed S. Aruwa, ya ce a shirye yake ya sadaukar da duk abin da yake da shi wajen ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma kan kujerarsa.

Aruwa ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ga Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, jim kaɗan bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin kwamishinonin jihar a Abuja.

A yayin ziyarar, an tattauna batutuwa da s**a shafi harkokin yaɗa labarai da sadarwa, da kuma hanyoyin inganta haɗin gwiwa wajen isar da bayanai kan ayyukan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ga al’ummar Kano.

Ziyarar ta kuma kasance wata dama ta nuna goyon baya ga ƙoƙarin Kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya wajen gudanar da ayyukan ma’aikatar, tare da inganta hanyoyin yaɗa manufofi da ayyukan gwamnatin jihar ga jama’a.

Ba tsoro bane yasa ake kau da kai Kanon kawai ake kallo, idan mutun rashin kunya ce ko tsageranci, ba a kusa da gida za'...
28/09/2026

Ba tsoro bane yasa ake kau da kai Kanon kawai ake kallo, idan mutun rashin kunya ce ko tsageranci, ba a kusa da gida za'ai ba, ayi mahada a wani dajin - Comrd Abdullahi Wayya Kwamishinan yada labarai na jihar Kano.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya gana da ɗa...
28/09/2026

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya gana da ɗaya daga cikin manyan masu shirya gangamin Tinubu Must Go (TMG), Barista Abba Hikima.

Atiku Abubakar ya bayyana ganawar da kuma goyon bayansa ga yunƙurin neman sauyin siyasa na gangamin TMG a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ganawar tasu ta gudana ne bayan kammala wani zaɓen jin ra’ayin jama’a da masu gangamin s**a gudanar a shafukan sada zumunta, inda aka bayyana cewa ɗimbin mahalarta sun nuna goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

Bayan fitar da sakamakon zaɓen jin ra’ayin jama’ar, Barista Abba Hikima ya bayyana goyon bayansa ga Atiku Abubakar da takararsa ta shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.

28/09/2026

"Nayi Tunanin Peter Obi da Kwankwaso sun janye takararsu, Atiku kuwa tun ana gobe zabe yake faduwa zaben sa. - Sheikh Sani Isah Kano.

Address

Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AMC HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share