24/06/2025
GA WASU TAMBAYOYI GUDA (10) MASU MUHIMMANCIN GASKE.
Kataimaka Dan Allah Ka Karanta Ka Turawa Mutane Dan su Anfana Kai ma Kayi sadakatul Jariya Lada Mai Gudana.
Wani mutum yazo wajen Manzon Allah (ﷺ) yace : Yah Manzon - Rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.
1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane ?
Sai MANON ALLAH yace "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa.
2. Ina son in zama mafi arziki a cikin mutane ?
Manzon Allah ya ce : Ka zama mai wadatar zuci.
3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane ?
Sai ya ce : Ka zama mai amfanarwa.
4. Menene zai kare ni daga wuta ?
Sai ya ce : Ka zama mai yawan yin Azumi.
5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane ?
Sai ya ce : Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka.
6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah ?
Sai ya ce : Ka yawaita tuna Allah.
7. Ina son imanina ya zama ingantacce ?
Sai ya ce : Ka gyara halayen ka.
8. Menene yake huce fushin Allah (SWT.) ?
Sai ya ce : Ba da zakka A ɓoye da kyautata wa 'yan uwa.
9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah ?
Sai ya ce : Mummunar hali shine rowa
10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah ?
Sai ya ce Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah.
Ina roqon Mai karatu dan girman Allah dan son Annabi kayi ƙokari ka tura koda A group 1 ne domin tunasarwa.
Manzon Allah (ﷺ) yace : " Idan Allah ya shiryar da mutum guda ta dalilinka, yafi Alkhairi gareka fiye da abaka jajayen raqumma"
Allah yabamu ikon yin aiki da abinda mukaji . Ameen 🤲
Al-sherkwey ✍️