27/04/2024
18+
*Dalilan Dayasa Wasu Mazan Keson Mata Masu Manyan Ɗuwawu*
Kutiri, Ɗuwawu ko Mazaunai kamar yadda akafi saninsa da suna, wani ɓangare na halittar mace dake banbance ta da namiji.
A kuma tsakiyar marabar ɗuwawun ne Allah Yayi dubura domin tace najasar da mutum ya samar ta hanyar cin abinci da muke kira bahaya a sirrance ko kashi a bayyane.
Wasu daga cikin alamomin da ake bambamta mace dana miji Ɗuwawu yana daga ciki, duk kuwa da ana samun wasu mazan da sukeda manyan ɗuwaiwuka kamar na mata wanda hakan a cewar masana akwai matsala.
Ɗuwaiwukan mace yana daga cikin alamun ƙosawarta ta isa haihuwa bayan tabbatar da bagalagarta.
Don haka yana da wuya mace a ganta da manyan ɗuwaiwuka a lokacinda take da ƙarancin shekaru.
Duk kuwa da akwai yaran da suke tasowa da shi.
Ɗuwaiwuka suna gaba-gaba cikin manyan halittun mace dake fito da kyau dirin halittanta da kyaun siffanta duk kuwa da ba kowacce mace bace ake samunta da ɗuwawu kuma da kyaun fuska ba, sai dai akasarin mata masu ɗuwawu suna da kyaun diri kamar yadda bincike ya tabbatar.
Su dai mazaunan matan Allah Yayisu dabam-dabam.
Akwai masu tudun da ake musu lakabi da "Kilimanjaro," da akwai "Ɗuwawun kura" da dai sauransu.
Sai dai babu siffar mace mai ɗuwawun daya fi ɗauke hankalin maza harma a da mata irin mace mai ɗuwawun da siffar da ake cewa 'Coca-cola shape".
Siffa ne da maza suke sha'awar ganin mace dasu.
Duk kuwa da siffar mazaunar mace yana da alaƙa da asalinta idan danginta suna da shi, sai kuma ikon Allah da yake yin halittar wasu daban da mahaifansu
Mazan da aka zanta dasu akan dalilansu na son mata masu ɗuwawu sun nunawa cewa ita mace mai ɗuwawu tana kwantar da zuciyar mai kallonta.
"A gaskiya ina matuƙar sha'awar naga mace da ɗuwawu musamman ina zaune a gida ana juyaminisu ina samun natsuwa da kwanciyar hankali, shi yasa dukkannin matana uku babu laifi sunada mazaunai".
Cewar Ibrahim Aliyu.
" Aini banama sanin mace na kusa dani muddin banga ɗuwawunta na motsawa ba, a gaskiya babu ma yadda za a haɗa siffar mace mai ɗuwawu da marashi ko a yanayin kwalliyarsu".
Cewar Habibu Tahir.
"Ita mace mai baiwar ɗuwawu Alhaji tayi, domin ko rungumarta kayi ta baya ka wadata, don haka bani da wani buri a yanzu irin na samu mata mai irin wannan siffar na aura don ko ƙofa bazan leka sai nayi bakwai, (dariya)".
Musa Hamidu.
Shi kuma Aminu Alkali yace" Mata masu manyan kuturi kamar yadda kace basuma cika tsufa ba, ko da sun haura shekaru tsufansu baya nunawa.
Haka kuma duk yadda s**a maka kwalliya sai kaga dabam Wallahi. Nidai a gaskiya zuciyata tana cike da son naga mace da baya (ɗuwawu)".
Har ila yau bincike ya ƙara tabbatar da cewa duk wata ƙabila ta duniya da suke da al'adar sawa a yiwa sarakunansu rawa, tsarin gudanar da rawar bai wuce ko dai a kada kirji yadda nonuwa zasu riƙa rawa ba, ko girgiza da kuma a kaɗa ƙugu yadda za a juya ɗuwaiwu.
Hakan yasa mata masu manyan ɗuwawu sune ake zaɓe domin zuwa gaban manyan baƙi ko nishaɗar da sarakuna a lokutan taruruka ko zaman nishaɗi.
Ko da yake shi shan koko daukan rai ne, ba dukkannin maza bane suke son mace da ɗuwawu ba, ana samun wasu mazan babu siffar macen da suke so da sha'awa irin matan nan masu ɗuwawun raƙumi, su a wajensu irin wannan matan suke kwanta musu a zuciya kuma sune abunda zuciyarsu ke kewar ganin matsayin matarsu.