03/10/2026
A wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman, ANIPR, ya fitar a madadin Shugaban Hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, ta bayyana cewa wajibi ne ga duk wani mawaki ko marubuci ya gabatar da wakarsa ko rubutunsa ga Hukumar kafin sakin su ga al’umma, domin gudanar da tantancewa da tabbatar da cewa babu kalmomi ko abubuwan da za su iya haifar da tashin hankali ko tada zaune tsaye a cikin al’umma.
Sanarwar ta kara da cewa dokar da ta kafa Hukumar ce ta ba ta hurumin tantance wakoki da sauran ayyukan da s**a shafi harkar fina-finai da dab’i. Hukumar ta ce ba za ta ci gaba da kallon wasu mutane suna karya dokokinta ba da sunan ‘fadin albarkacin baki’, tana mai jaddada aniyarta ta tabbatar da bin doka da oda tare da yin adalci ga dukkan masu ruwa da tsaki ba tare da nuna wariya ko son kai ba. A saboda haka, Hukumar ta bukaci Tijjani Gandu da ya mutunta kansa tare da girmama doka ta hanyar amsa gayyatar da aka yi masa.
Hukumar ta kuma bayyana cewa kin amsa gayyatar na iya tilasta mata daukar matakan da s**a dace bisa tanadin doka. Haka kuma, ta yi kira ga dukkan mawaka, marubuta da sauran abokan hulɗarta da su ci gaba da bin dokoki da ka’idojin Hukumar domin tabbatar da zaman lafiya, daidaito da ci gaban harkar nishadi da adabi a Jihar Kano.