20/05/2024
Karim Khan ya tsokano sama da kara.
Daga Shafin Abubakar Umar Abubakar
Karim Khan shine babban alkalin kotun laifukan yaki ta ICC da take birnin Hague, Netherland, a yau za'a iya cewa ya kafa tarihi ta hanyar bayyana kudurinsa na mikawa alkalan kotun mujallar sammaci zuwa ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant da Shugaban Kungiya Hamas Isma'il Haniyye da Yahya Sinwar da kwamanda Muhammad Deif!
Tare da kasancewar kudurin kotun ta ICC cike yake da siyasa da kokarin daidaita azzalumai (Isra'ila) da wadanda ake zalunta tsawon zamani (Falastinawa) acikin laifi iri daya, da kawar da kai daga wasu manya-manyan tuhumce-tuhumce da suke kan Gwamnatin Netanyahu na kisan kare dangi (Genocide), da kuma kawar da kai game da abinda yake faruwa a West Bank tare da kasancewar akwai kararraki da aka jima da shigarwa a kotun tasa akan wannan al'amari, sai dai hakan bai fishsheshi ba daga gargadi da barazanar Gwamnatin Amurka, dama Sanatoci kusan 12 sun lashi takobin sai sun kai shi kasa tare da iyalansa idan har ya kuskura ya bayarda sammacin k**a Netanyahu, to yau ya kekasa kasa ya daki kirji ya bayyana aiwatar da hakan a zahiri.
Amurka wacce ta taimaka wajen ganin an sanya Putin acikin wadanda kotun ta bada sammacin cafkewa idan ya taka daya daga cikin kasashen da suke da yarjejeniya da kotun, itace kuma yau ta yiwa kotun tofin alatsine akan kokarin k**a Netanyahu.
Ga wanda yake bibiyar yakin Isra'ila akan Mutanen Gazza, zai shaida cewa tabbas wannan kudurin na kotu yayi matukar yin rangwame game da adadin Mutanen da ya k**ata ace an k**a, ina Ministan cikin gida Itamar Ben-Gvir, ina Ministan kudi Smotrich? Kusan su sunfi kowa ma miyagun kalamai da kira zuwa ga yiwa Falastinawa kisan kare dangi.