Umar Sobeka

Umar Sobeka Madubin hasko gaskiyya da bayyanata ga Al,umma

Wasu Mataye Kenan Da S**a Sauya Halitta Su Zuwa Mazaje An Cire Musu Nonuwa Tare da Aske Musu śuma Kansu. Wani Fata Kuke ...
28/04/2023

Wasu Mataye Kenan Da S**a Sauya Halitta Su Zuwa Mazaje An Cire Musu Nonuwa Tare da Aske Musu śuma Kansu.

Wani Fata Kuke musu ?

YANZU-YANZU: Kotun majistiret dake kumo karamar hukumar Akko Jihar Gwambe ta yankewa wani matashi hukuncin tarar N2.6 mi...
28/04/2023

YANZU-YANZU: Kotun majistiret dake kumo karamar hukumar Akko Jihar Gwambe ta yankewa wani matashi hukuncin tarar N2.6 million sak**akon yaudarar wata budurwa har na tsawon shekaru bakwai

Matasan unguwa sun haɗu sun ɗaure wannan bawan Allah sunyi mashi dukan tsiya.Saboda kullum bashida aiki sai dukan matar ...
28/04/2023

Matasan unguwa sun haɗu sun ɗaure wannan bawan Allah sunyi mashi dukan tsiya.

Saboda kullum bashida aiki sai dukan matar shi.
Kullum sai sunji matar tana ihu Yana dukan ta k**ar wata baiwa hakan ya tunzura matasan unguwar daga jaridar KHN hausa.

Babban abun da yake bani mamaki a gurin namij mai dukan matar shi bayan ka gama dukan ta idan ta girka abinci zakazo kaci kuma idan kana neman saduwa da ita bai hana ka rarrafo ka same ta bayan ka biya buƙatar ka gobe bai hana ka sameta ka doketa ba.

Wannan wane irin rashin lissafi ne na mazaje masu dukan matan su?

Bafa a kasuwa kasayeta ba a cikin gidan su ka aurota tayaya zaka mayar da ita k**ar wata dabba

Mazaje masu wannan ɗabi'ar Allah ya ganar dasu idan basu da niyya Allah ya cigaba da haɗasu da fushin matasan unguwa Amin.

.

Mafi Yawan Mata Masu Amfani Da “Sha-Ka-Fashe” Ƴan “Lesbian” Ne... Cikin ikon Allah na samu damar gudanar da wani bincike...
27/04/2023

Mafi Yawan Mata Masu Amfani Da “Sha-Ka-Fashe” Ƴan “Lesbian” Ne...


Cikin ikon Allah na samu damar gudanar da wani binciken sirri a matsayi na na Likita, kuma wanda ke wayar da kan al’umma kan harkar lafiya. Na samu zarafin zantawa da mata da dama wanda dayawan su ƴan maɗigo (le****ns) ne kuma daga mabanbantan jahohi na Arewacin Nigeria.


Babban dalilin gudanar da wannan bincike na ƙwaƙƙwafi shi ne, ganin yadda al’umma s**a damu da yadda ƴan mata suke yawan amfani da wannan magani na “Sha-ka-fashe”. Haka-zalika, sanin illolin wannan magani da nayi a Likitance ya sa ni dole na tashi tsaye wajan gano bakin zaren. Domin ta haka ne kaɗai zan iya samun damar bada shawarwari da faɗakar da masu amfani da shi domin su daina. Dalili kuwa shi ne idan baka san dalilin yin abu ba to ba za ka iya bada maganin wannan abu ba.


Da farko dai ya zama wajibi na miƙa godiya ta musamman ga dukkan ƴan madigo (le****ns) da s**a taimaka s**a shiga cikin wanna bincike da nayi ta hanyar amsa tambayoyin da na yi musu da kuma ƙara haɗa ni da s**a yi da abokanan su daga shiyya-shiyya. Tabbas su ma waɗanda ba ƴan le***an ba da suke amfani da wannan magani suma ina miƙa godiya ta gare su domin samun dama da s**ai wajan amsa tambayoyin mu.


Babban abun da ya ke sa mata shan maganin “Sha-ka-fashe” shi ne domin kara girman mazaunai (hips), cinyoyi (thighs), da kuma nonuwa (breasts). K**ar yadda na samu bayani, wannan su ne manyan dalilan su. Kuma wannan buri na su ya samo asali ne daga yadda a cikin harkar maɗigo (le***anism) ake daukar su da muhimmanci domin idan mace a rame take, ba'a fiya sha’awar ta ba. Amma sun tabbatar mun da cewa buƙatuwar hakan yafi yawa wajan waɗanda suke zama k**ar mace (feminine role) ba wacce take zama 'namiji' (masculine role) ba.

Sak**akon binciken ya nuna cewa mafi yawan mata suna amfani da kala-kalar magunguna da dama, amma akwai wasun su da suke amfani da “allura” ba magani ba. Dalilin su na amfani da allura shi ne, ba sa iya jimirin haɗiye ƙwaya kullum. Haka-zalika, sun karkata ga amfani da allura ne saboda a tsammanin su, allura na da ƙarancin illoli idan aka kwantanta ta da magani na sha
Sun tabbatar mun da cewa waɗannan magunguna suna fara nuna tasiri a jikin su cikin wata ɗayan farko da s**a fara amfani da su, inda kuma wasu suke cewa sati biyu. Amma dai mafi yawan su wata ɗayan farko suke cewa. Sun tabbatar mun da cewa suna masifar samun cigaba da kuma samun kuɗi a rayuwar su matuƙa sosai a yayin da s**a fara samun canjin yanayi. Wannan kuɗi suna samu ne ta wajan yawan abokanai na harkar su ta mu’amalar arziƙi ta maɗigo k**ar yadda s**a bayyana min.


Amma a inda gizo ke sakar shi ne, mafi yawa daga cikin su sun tabbatar mun da cewa gaskiya sun dan haɗu da wasu ƙalubale da dama yayin da suke shan magungunan wanda s**a hadar da matsanancin ciyon kai, rashin bacci, jiri, da yanayin damuwa. Waɗannan alamomin suna samun sune a farkon fara amfani da maganin ne. Akwai wacce tace min sak**akon shan magani da allurar “Sha-ka-fashe” duk sati sai tayi zazzaɓi kuma taje asibi amma ance mata garkuwar jikin ta tayi rauni saboda amfani da maganin ƙiba. Kuma gaskiya ne haka abun yake ko a likitance tabbas jinsin wadannan magunguna (wanda aka fi sani da ‘steroids’) suna kawo raunin garkuwar jiki!


Babu abin da yafi ɗaure min kai sama da wacce tace min yanzu haka ba ta gani sosai sak**akon amfani da waɗannan magunguna. Kuma gaskiya ne suna kawo lalurar rashin gani. Wata kuma ta samu matsalar taruwar ruwa a jiki (water retention) wanda da gaske waɗannan magunguna suna kawo hakan. Wannan kaɗan daga cikin illolin da wasu s**a bayyana min sun samu kenan.


A ƙarshe ina mai cewa wannan bincike da muka yi ba munyi ne domin tozarta wasu ba ko kuma nuna rashin dacewar yadda wasu suke rayuwa ba, face munyi ne domin gano wasu muhimman abubuwa, wanda insha’Allah za mu wallafa wannan bincike a cikin harshen ingilishi tare da saka duk wasu alkaluma da duk ma abun da ba mu saka anan ba. Dalilin yin hakan kuma shine domin mu isar da saƙo gurin mutanen mu na Arewacin Najeriya. Har kullum dai muna cewa “rigafi yafi magani.”


Dr. Khalid Sunusi Kani
Likita Kuma Me Wayar Dakan Al’umma Kan Cututtuka Da Dama.

Eunice Winstead, mai shekara 9, tare da mijinta mai shekara 22, Charlie Johns, a garin Tennessee, shekarar 1937. Kafin a...
27/04/2023

Eunice Winstead, mai shekara 9, tare da mijinta mai shekara 22, Charlie Johns, a garin Tennessee, shekarar 1937.

Kafin amincewa da bikin daurin auren, mai martaba sarkin tennessee ya bincika lasisin aurensu da sauri kuma ya amince da shi duk da bambancin shekaru.

Babu shakka daga baya an gano cewa ma'auratan sun yi ƙarya game da ainihin shekarun su a cikin takardar neman auren da s**a yi a kotu, kuma da yaudara yarinyar ta yi nasarar tserewa daga gidan iyayenta, don haka ta yi bikin aure ba tare da sanin iyayenta da danginta ba.

Wani ɓarawon shanu mai suna “Crazy Tex Hazel” ya ƙirƙiro kuma ya yi amfani da wannan takalmin a shekarun 1920 don ɓoye s...
27/04/2023

Wani ɓarawon shanu mai suna “Crazy Tex Hazel” ya ƙirƙiro kuma ya yi amfani da wannan takalmin a shekarun 1920 don ɓoye sawun sa yayin satar shanu.

Museum of Northeast Nevada

Sarki Leopold || Makashin  Baƙaƙen Fata Ƴan Afirka Miliyan Goma..."Ku sare kawunan mazajen, ku rataye su a cikin kauyuka...
27/04/2023

Sarki Leopold || Makashin Baƙaƙen Fata Ƴan Afirka Miliyan Goma...

"Ku sare kawunan mazajen, ku rataye su a cikin kauyuka, ku yi jima'i da matan gida, ku rataye yara da mata a kan giciye."

-Inji Sarki Leopold ||

Sarki Leopold II na Belgium ga hafsan hafsoshinsa, yana nufin mutanen da ya yi wa mulkin mallaka a Kongo.

Ga hoton wani yaro nan da Ƴan Mishan turawan mulkin Mallaka s**a Guntulewa hannu a zaluncin da s**a dinga tafkawa a ƙasar ta congo ƙarƙashin jagorancin Matsiyaci Sarkin Belgium na wancan loƴaci Leopold ||.. Shekarar " 1890-1910 " Shekara ɗari da sha biyu..

Mai martaba Sarki Leopold II.

Bayani:

Ƙasar Kongo ƙasa ce a Afirka ta Tsakiya Wadda ƙasar "Belgium" ta ƙwata da ƙarfin soja zamanin Sarki Sarki Leopold II Belgium wanda taron Berlin na 1885 ya kafa kuma ya amince da shi. A cikin shekaru 23 (1885-1908)
Leopold II ya mulki Kongo, ya kashe 'yan Afirka miliyan 10 ta hanyar Yanke hannaye da al’aura, da yi musu bulala har lahira, yunwa ta kashe su da aikin tilastawa, Ƙwacen yara da karɓar kudin fansa da kona Ƙauyuka. Wani abin ban mamaki na wannan labari shi ne cewa Leopold na biyu ya aikata wadannan ta'asa Batare da ko da taka kafarsa a ƙasar Kongon ba. A karkashin gwamnatin Leopold II.

Hoton dake Ƙasa na wani Mutumine da ke Kallon yadda aka yanke ƙafar ƴarsa , Saboda bai Yi aiki tuƙuru ba a kamfanin da yake aiki mallakin turawan mulkin mallaka na belgium Mai suna "ABIR Company" Cikakken Sunan kamfanin shine ( the Anglo-Belgian India Rubber Company daga baya aka canjawa kamfanin suna zuwa Compagnie du Congo Belge) ..

K**ar Yadda Shahararriyar Marubuciyar nan "Alice Seeley" Ƴar Ƙasar Amurka mazauniyar birnin Los Angeles " ta Rubuta a Littafinta Mai suna "Don’t Call Me Lady: The Journey of Lady Alice Seeley Harris:"

"Sun Yankewa ƴar Ma'aikacin Hannu Sunan Yarinyar Boali daga baya kuma matarsa sannan s**a yankewa matar tasa al'aura daga baya ta Mutu... inji baturiya "Alice Seeley wadda ta kai ziyarar gani da ido a wancan loƙacin da abubuwan suke faruwa".

Wani limamin Katolika Mai suna "Tswambe" Ya faɗa cewa Shugaban Sojojin Sarki "Leopard || Mai Suna
" Léon Fiévez" Ya bawa Sojojin nasa Umarni Cewa "

"Duk gawarwakin da aka Kashe dole ne ku datse hannayensu.. Yana so ya ga adadin hannayen da kowane soja ya yanke, ya kawo su cikin kwanduna...Kauyen da ya ƙi ba da roba da Cocoa za a share shi gaba daya daga doron Ƙasa...

Ba cire ni sarautar Kano ne abinda ya ban takaici ba, sai ganin yadda mutuminnan ya keta alfarmar gidanmu, kuma ba zan d...
27/04/2023

Ba cire ni sarautar Kano ne abinda ya ban takaici ba, sai ganin yadda mutuminnan ya keta alfarmar gidanmu, kuma ba zan dawo sarautar Kano ba matuƙar ba'a haɗe masarautu wuri guda ba—Sanusi Lamiɗo

27/04/2023

Kwana da lafiya yafi kwana da miliyan dubu.

~Binciken Masana

Kafin Kayi aure a wannan loƙaci Ya k**ata kasan da wannan ..Kwanon Shinkafa ƴar Hausa Naira 1800 Ne Gwangwani Man gyaɗa ...
27/04/2023

Kafin Kayi aure a wannan loƙaci Ya k**ata kasan da wannan ..

Kwanon Shinkafa ƴar Hausa Naira 1800 Ne Gwangwani Man gyaɗa 250 Maggi ɗaya Naira 10 Biredi Wanda Mutum biyu zasu iya Ci Naira 250 Taliya 450 ..

Sabulun Wanka 200 Na Wanki 200 Kuɗin Ruwa Jarka ɗaya naira 50 a ƙalla ka sayi jarka biyu kullum naira ɗari..

Sai Ka Buga a sati ɗaya Kai da amarya da ƴan ƙannen amarya masu kawo ziyara zaku iya lashe Kwano Huɗu na shinkafa Kuɗinta Zai K**a naira 1850 ×4 Zai k**a Naira 7400..

Biredi 250 a ƙalla ku siya sau biyar a sati Kuɗinka Zai K**a 1250..

Taliya a ƙalla ka sayi Guda Uku a satinnan kuɗinka zai k**a 1350..

Kuɗin Ruwan sha na wanki dana wanka a ƙalla jarka biyu a rana naira ɗari sau 7 ya k**a ɗari bakwai a sati..

Sabulun wanka da na wanki ,Maggi , Kayan Miya, Gas ko gawayi , Man girki Kuɗinsu zai K**a Naira 6000 A sati..

Shinkafar Sati Ɗaya - 7400
Biredi na Sati Ɗaya- 1250
Taliyar Sati Ɗaya-1350
Kuɗin Ruwa-700
Su kayan miya da sabulun wanka da wanki, gawayi ko Gas , Man girki -6000

Total ɗin Sati ɗaya duka- 16,700
Total ɗin wata ɗaya-66,800

Wannan lissafi kada ka manta ba'a saka wasu abubuwa ba da yawa k**ar kuɗin magani na rashin lafiya, kuɗin kayan kwalliya, auduga ta mata yayin Al'ada, Kuɗin taransifot na zuwa wajen aiki ko kasuwa na maigida, Ƴar madara ta watsawa a shayi, ɗan naman miya, gasu nan dai birjik..

Shi yasa Muke gayawa samari da babbar Murya idan baka samun a ƙalla dubu hamsin a wata ka haƙura da aure kaga dai lissafin dubu sittin ma tayi kaɗan, wannan kuma shine ƙarshen lissafi wanda ba kowacce mace ce zata iya yadda ta zauna a haka ba...

Nayi Nan 🚶🚶

Adam Husaini Abubakar

WATA SABUWA: Na shirya tsaf domin na rataye kaina idan ban samu soyayyar Hadiza Aliyu Gabon ba".  Inji Muhd King Shameer...
23/04/2023

WATA SABUWA: Na shirya tsaf domin na rataye kaina idan ban samu soyayyar Hadiza Aliyu Gabon ba". Inji Muhd King Shameer.

Me zu ce?

~RCN HAUSA

Address

Northwest
Kano

Telephone

+2348092292212

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Umar Sobeka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Umar Sobeka:

Share