
13/09/2025
A cikin Gidan Rumfa, tsohuwar fadar da aka gina tun ƙarni na 15, akwai sassa masu yawa da jama’a ba sa ganin su.
Amma cikin waɗannan sassan akwai ɗaya da ake cewa “ɗakin da aka manta da shi”.
Wasu tsofaffin mazauna sun ruwaito cewa an taɓa amfani da wannan ɗaki wajen ajiye takardu da kayan gargajiya da s**a shafi masarautar Kano.
Amma shekaru da s**a wuce an rufe ƙofar ɗakin gaba ɗaya, kuma babu wanda ya sake shiga ciki — sai dai Sarkin Kano da waɗanda suke kusa da shi ƙwarai.
🕯 A lokacin da Eagle Shadow ya fara bincike, mun gano alamun da s**a nuna cewa ƙofar ɗakin ta sha gyara a lokuta daban-daban. Amma abin mamaki shine: babu wani littafi ko tarihi da ya bayyana dalilin rufe ɗakin gaba ɗaya.
👉 Shin me ke ɓoye a cikin ɗakin?
Takardun sirri?
Dukiyar gargajiya?
Ko wani abin da ba a taɓa faɗi ba?
Wannan shi ne Asirin Gidan Rumfa.
Eagle Shadow zai ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ke bayan ƙofar da aka kulle tun shekaru aru-aru.