03/01/2026
ƊAN-ƘASHIN-GWIWA
Wata rana an yi wata mace mai yawan roƙon haihuwa. Ran nan sai wani đan kurji ya fito mata a kan gwiwarta. Sai ta ce, "Allah ka ba ni da ko da na ƙashin gwiwa ne ma mana?"
Shi ke nan, take sai ta ɓincine ƙurjin nan na kan gwiwarta. Sai kuwa ta ga ɗa ya fito subul. Sai ta yi murna.
Bayan ta gama murna, sai ta ce, "To, yau kuma ina zan sami itacen wanka?"
Sai Ɗan-Ƙashin-Gwiwa ya ce, "ya ba ga ni ba?"
Sai kuwa ya je ya yiwo mata itace mai yawa, ya kawo mata.
Ta kuma cewa, "Ko ina zan sami abincin da zan ci?"
Sai ya ce, "Iya ba ga ni ba?"
Sai ya je gidan namun dawa ya ɗebo mata alk**a da shinkafa da dai hatsi iri iri ya kawo mata.
Kullun sai ya je ya debo mata hatsi himi, har daKullu nan namun dawa s**a gane cewa ana yi musu satar hatsinsu.
Sai s**a yi shawara s**a bar kura jiran Barawon don in ya zo yin sata ta k**a shi, ta đaure, kafin su dawo.
Shi ke nan. S**a bar kura jiran. Tana zaune sai Ɗan-Ƙashin-Gwiwa ya zo.
Sai ta ce, "To, da ma ashe kai ne ka ke zuwa kana yi mana sata?"
Sai ya ce, "Au, ke aka bari jira yau?"
Sai kuwa ya ɗauki kura ya ɗaga ta sama ya raɗa ta da ƙasa tim. Ya ciro gashin kansa guda daya ya đaure ta ya jefa sama. Ya debi kayan abinci ya yi tafiyarsa
abinsa.
Can sai ga namun dawa sun dawo. S**a samu kura a sama a ɗaure. S**a sauko đa ita s**a tambaye ta yadda aka yi.
Kura ta ce, "Ai wannan ɓarawon ya fi ƙarfina."
Sai s**a ce, To wannan sai zaki ne zai iya ke nan,"
Aka bar zaki jira. Zaki yana zaune yana jira sai ga Ɗan-Ƙashin-Gwiwa ya zo.
Sai zaki ya ce, "To, ashe da ma kai ne ka ke zuwa kana yi mana sata? To yau Allah ya sa na k**a ka."
Sai Dan-Kashin-Gwiwa ya ce, "Au, yau kuma kai aka bari jira?"
Sai ya ɗauki zaki ya fyada da ƙasa. Ya ciro gashin kansa guda daya ya ɗaure zaki da shi. Ya debi kayan abinci yadda ya ke so ya tafi abinsa.
Da namun dawa s**a dawo s**a samu zaki a wannan hali, sai s**a ce, "Yaya aka yi haka kuma zaki?"
Sai ya ce, "Ai wannan ɓarawon ya fi karfina.'"
Sai s**a ce, "Ai wannan sai dai giwa ce kawai za ta iyar masa."
Sai s**a tafi s**a bar giwa jiran ɓarawo. Tana cikin jira sai ga Ɗan-Ƙashin-Gwiwa ya zo. Sai ta ce da shi, wato da ma kai ne ka ke zuwa kana kwashe mana kaya ko? To na ritsa ka yau."
Sai ya ce, "Af, yau kuma ke aka bari iira
Sai ya dauke ta ya damfara da kasa. Ya ciro gashin kansa daya ya daure ta da shi. Ya yi tafiyarsa abinsa.
Can sai sauran namun dawa s**a zo. Da s**a ga giwa a wannan hali, sai s**a ce, *Me kuma ya faru giwa?"
Sai ta ce da su, "Ai wannan ɓarawon ya fi ƙarfina."
Sai s**a ce, "To tun da ya ke abin ya fi ƙarfin giwa ma ai sai mu gudu.'"
Sai s**a shiga haɗa, kaya. Suna ta shirin gudu. Kafin su gama sai Ɗan-Ƙashin-Gwiwa ya ji labari ya rugo da
gudu ya shiga tandun mai. Namun dawan ba su gan shi ba.
Da s**a gama shiri, sai kura ta ce ita ce Za ta dauki tandun man. Sai aka yarda ta dauka.
Sai s**a dauki kaya s**a k**a hanya. Suna cikin tafiya sai kura ta ce, "Ni zan ba da waƙa, ku kuma kuna amsawa,"
Sai s**a ce, "To, bisimilla."
Sai kura ta fara sa waka:
Mun rarrabo da Ɗan-Ƙashin-Gwiwa;
Ɗan shegiya.
Ana cikin wannan hali, sai kura sarkin kwaɗayi ta ce za ta fitsari. Su kuwa sai s**a ce da ita ta ba su tandun màn. Sai ta ce, "Au, zan sha muku ne?"
Sai ta tafi yin fitsari da tandun man. Ta je ta bude tandu za ta saci mai sai ta ga Ɗan-Ƙashin-Gwiwa a ciki yana yi mata daƙuwa yana cewa, '"Uwaki. ldan kuwa
kika faɗa, to kisanki zan yi."
Ta ce, To. Ba zan fada ba.'"
Ta dauki tandu ta tafi wurin abokan tafiyarta jikinta rawa saboda tana jin tsoron Dan-Kashin-Gwiwa.
Sai ta ce, "Oho. Ba kome."
Sai s**a ce, "To ai sai ki ci gaba da sa mana waka. Kura ta ƙi."
S**a ce, "Ai ke ce kika fara, kuma ke za ki ci gaba da yi."
Sai kura ta ce, "To "
Sai ta fara sabuwar waka:
Mun rarrabo, mun rarrabo,
Da Ɗan-Ƙashin-Gwiwa,
Mai ɗan zanko, ɗan arziki.
Sai s**a ce, "A'a, ai da ba haka ki ke fada a cikin waƙar ba."
Da ta ga sun gane ta, sai ta yi wuf ta jefar da kuttun man ta ce, shi ne a cikI."
Sai kowa ya k**a gabansa.
S**a yi watsi da kayan, s**a ruga da gudu gaba daya.
Dan-Kashin-Gwiwa kuwa sai ya yi ta jidon kaya yana kai wa babarsa. Ya jide tsaf. S**a sami abin da za su daɗe suna ci.
Shi ke nan..
Kurunkus kan kusu. Ba don Gizo ba da na yi karya. Dama karyar na shirga.
Littafi: Ibrahim Yaro Yahaya, Tatsuniyoyi da wasanni na 4.