19/11/2024
"Digital Nomading…"
As always, translating certain English terms can be tricky, but let me explain this one the way I know best—through storytelling!
Someone might say, “This term sounds more like it’s meant for traders, travelers, or perhaps merchants!”
But actually, "Digital Nomading" refers to someone who works from anywhere—whether it’s from their bed, their shop, or even a relaxing spot somewhere. If you’re a digital nomad, you could be working from your bedroom, a famous café in Zaria, or even Dubai—wherever the internet can reach, you can make your money!
So, if you prefer, you could work from your bed (in whatever position you like 🙈), from a local masallaci, or even from a cramped room somewhere in Kano. It doesn’t matter, as long as you’ve got internet and a laptop.
Whether it’s at the office or from your bed at home, once you’ve got internet access and the skill to make things happen, success will follow you wherever you go—straight-up Digital Nomad life!
_______
"Digital Nomading..."
Kamar yadda aka saba, duk kalmomin turanci suna da wuya wajen fassara, amma bari in kawo wannan ta yadda na saba, cikin labari—Storytelling!
Wani zai ce, “Ai wannan kalmar ta fi dacewa da ƴan kasuwa ko wanda yake matafiyi, ko kuma wani mai fatauci!”
Amma ka san fa, wannan "Digital Nomading" yana nufin wanda yake gudanar da aikin sa daga kowanne wuri—ko daga kan gadon sa, ko daga shagon sa, ko kuma daga wani wurin da yake shaƙatawa. Idan ka zama digital nomad, zaka iya zama cikin daƙin ka na kwana, ko a cikin wani shahararren café a Zaria ko Dubai—duk inda intanet zai bi, zaka tattaro dukiya abinka!
Saboda haka, idan ka ga dama zaka iya aiki daga kan gado, duk yadda kaso 🙈, ko cikin massalacin yankin ku, ko kuma cikin matsatsen ɗaki kamar na cikin garin Kano, babu wani bambanci idan har da intanet da laptop kake nema.
Ko dai a wurin aiki ko gidan ku na gado, idan ka samu intanet da damar sarrafa basirarka, to, tabbas daukaka zata bika ta ko'ina—Digital Nomad kai tsaye!