
11/04/2025
Gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗin cewa za a samu mamakon ruwan sama a jihohi 30 da babban birnin tarayya A buja, wanda ambaliya za ta iya biyo bayansa.
Jihohin da za su fi fuskantar barazana su ne: Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Bayelsa da Benue da Borno da Kuros Riba da Delta da Ebonyi da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kebbi da Kogi da Kwara da Legas da Nasarawa da Neja da Ogun da Ondo da Osun da Oyo da Rivers da Sokoto da Taraba da Yobe da Zamfara da Abuja, k**ar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftace muhalli, Joseph Utsev ya bayyana a ranar Alhamis cewa za a fara ne da fuskantar mamakon ruwan sama a jihohin.
Ministan ya ce mamakon ruwan ne zai yi yawan gaske da zai jawo ambaliya a jihohin na Najeriya.
Ya bayyana cewa garuruwa 1,249 a ƙananan hukumomin 176 a jihohi 30 da babban birnin tarayya Abuja ne suke cikin barazanar.