The HausaTimes

The HausaTimes Your go-to source for authentic news
& Uncovering fascinating and unbelievable facts from astronomy and cosmology, alongside history and geopolitics.
(1)

MAHANGAR GASKIYA: Matsalar Hausa-FulaniCikin kwanakin nan, akwai Matasan Hausawa da ke; Sukar Alaƙar Hausa-Fulani, Sukar...
03/09/2026

MAHANGAR GASKIYA: Matsalar Hausa-Fulani

Cikin kwanakin nan, akwai Matasan Hausawa da ke; Sukar Alaƙar Hausa-Fulani, Sukar Yaƙin Ɗanfodio 1804, tare da rajin kare Tarihin Hausawa matsayin Kabila (Ethnicity).
Hakan ya kawo ka-ce-na-ce har da muhawara a shafin Prof. Kperoogi tare da Prof. Tijjani Imam kan yanayin lamarin.
Wasu su ce abin Kwangilar yahudawa ne, Maguzanci da Kafirci ko Tada Husuma don raba kan Al'umma.
⚠️ABIN LURA
Babu Bukatar sanin, Wa ke da gaskiya ko waye bai da shi?
Waye Azzalumi ko kuwa wa aka cuta?
💥Tambaya Mafi Muhimmanci;
Me ke sa Mutane su zauna lafiya ko su samu ɓaraka?
Me ke tilastawa mutane tuno baya ko binciko abin da ya shuɗe?
Me yake taimakawa Haɗin kai da mantar da mutane kaifin matsalolin baya?
🌍 AMSA GA MAI HANKALI
Abin da mafi yawan mutane ba su ganewa shi ne:
Hausawa suna cewa "Fatara Shi ka tada tsohon bashi......"
Babu wata al'umma a doron duniya da babu zalunce-zalunce na tarihi da bas**a tsakanin dangogin cikinta ko abokan zamanta a cikin kasarta ko makwabtanta.
K**a daga Saxons Vs Normans, Arabs Vs Turks, Greeks Vs Turks, Persians Vs Arabs, Armenians and Azerbaijans, Yoruba Vs Nupe, Oworo Vs Ijebu, Jukun Vs Tiv
Amma Managarciyar Al'umma ita ce wacce ta iya tsallake matakan gaba da Ƙiyayya kan batutuwa da s**a gabata, don gyara maslahar yau da ta haɗa su ta zamantakewa.
Mun ga yadda mutanen Faransa da Ingila s**a haɗa hannu s**a samu daidaito don samarwa juna cigaba duk da tarihin yaƙe-yaƙe da ke tsakaninsu a baya, haka ma sun mori maslahar Colonisation tare, ba su bari gaba da tsana ya sa sun kasa ganin maslaharsu ta bai ɗaya a wannan yayin ba.
Duk da haka, Tsoffin batutuwan tarihi (Gaba da Yaƙi) suna rasa muhimmanci ne ko tasiri idan ya kasance babu mak**antan waɗannan matsalolin na baya tsakanin Kabilun biyu a rayuwarsu ta yau, sannan ya kasance akwai bayyananniyar maslahar rayuwa a haɗuwar kai ba tare da barazana ga rai, dukiya ko mutunci ba tsakaninsu.
Akasin haka kuwa, Duk wata zumunta, Tarihin Dangantaka ko Addini da Makwabta duk za su rushe
Mun ga yadda Kusancin jini, al'adu, tarihi da addini s**a kasa wanzar da salama tsakanin kabilun Banu Wa'il (Baku Bin Wa'il da Tagliba Bin Wa'il) har Mawaki Tarfa yake cewa:
والظلم فرّق بين حيي وائل # بكر تُساقيها المنايا تغلب
Haka ma tsakanin Kabilun Ghatafan wato Absu da Zibyaan.
Hallau ko bayan Musulunci, Rikici irin na Ƙabilanci ya yi ta samuwa tsakanin Qaisu Ailan da Yemeni Tribes.
Duk wannan zai nuna maka gaskiya guda:
Wato, Kusanci ko Addini ba ya haɗa kan mutane muddin maslaharsu ta kasa daidaituwa.
Don Haka nake gani cewa, Ba wai batun Addini, Auratayya ko Mu'amala ta haɗa mu ba, Zance ne na:
1. Meye amfanin da tarayyar ta mu take yiwa kowanne ɓangare a yau?
2. Shin dukkanmu mun iya gamsuwa cewa babu cuta babu cutarwa a wannan Gambizar?
3. Me yasa mu ke tado irin wannan batutuwan a yau?
4. Me ya k**ata mu yi don samar da cigaban wannan haɗin kai?
5. Shin zargin Kwangila ko Agenda mai ɓulle ne kuwa?

NB: Mu sani cewa, Masarautar Ingila a yau, Galibin Title Holders ɗin ta zuriyar Norman Conquerors ne, Haka Gidan Sarautar House Windsor (Gotha Saxe-Coberg), Asalinsu Germans ne.
Amma shin kana jin tashin zantuka mak**ancin irin wannan?
A'a, Saboda kuwa Talakawan Ingila (Galibi zuriyar Saxons) ba su da wata matsala ko barazana da za ta tilasta masu irin wannan tone-tonen don kuwa tsarin ya iya tsayawa maslahar Tsaro da mutuncin kowa ba tare da wariya ba.
Nicholas Micheavelli yana cewa a littafin THE PRINCE:
"MUTUM YANA IYA MANTA WANDA YA KASHE MAHAIFINSA, AMMA BA ZAI TAƁA MANTA WANDA YA JEFA RAYUWARSA CIKIN TASKU BA"
⚠️Ka tambayi kanka,
Shin haka abin yake a Matsalolinmu na Arewa a yau?
Hala ba kariya ake ba wa Yan Bindigan nan ba, cewa An zalunce su ne a baya?
Marasa kunya cikin shugabanni ma cewa su ke wai Ƴan uwansu ne, Ta ya Ba za a fassara abin a haka ba?
Eh, Zance ne na cewa:
TA'ADDANCI BAI DA KABILA
AMMA DAGA RANAR DA ADALCI YA FARA TANTANCE KABILA, TABBAS TA'ADDANCI MA ZAI SAMU KABILA.
GWAMNATI TANA WANZAR DA HADIN KAI NE TSAKANIN MUTANE, AMMA FA MUDDIN TA KASA YIN HAKAN, KOWANNE BANGARE ZAI ƊAU MASLAHARSA A HANNUNSA.
BA ZANCEN YA KAMATA BA NE WANNAN
BA ZANCEN HAUSA ACTIVISM DAIDAI NE KO KUSKURE BA, ZANCE NE NA CEWA "THESE ACTIVISTS ARE ACTING AS HUMANS DO"
IT IS BEYOND GOOD AND EVIL
ZANCEN RAYUWA AKE!!!

Aruwa
02/09/26

"A Arewacin Najeriya duk wani yare da ba Hausa ba saidai ka yi a gidanku ko iya layinku" cewar malamin soro me za ku ce?
29/08/2026

"A Arewacin Najeriya duk wani yare da ba Hausa ba saidai ka yi a gidanku ko iya layinku" cewar malamin soro me za ku ce?

"Yau rana ce muhimmiya ga ƴan'uwa Hausawa.Ina yi mana addu'ar Allah yai mana maganin ƴanta'addan Bandits da masu goya mu...
26/08/2026

"Yau rana ce muhimmiya ga ƴan'uwa Hausawa.
Ina yi mana addu'ar Allah yai mana maganin ƴanta'addan Bandits da masu goya musu baya"
~prof Tijjani imam

Shugaban Nigeria ya taya Al'ummar Hausawa murnar ranar Hausa ta duniya."Hausawa manyan turaku ne da ke taka muhimmiyar r...
26/08/2026

Shugaban Nigeria ya taya Al'ummar Hausawa murnar ranar Hausa ta duniya.
"Hausawa manyan turaku ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen tsayuwar
Najeriya da cigabanta. Harshen Hausawa kuwa tabbas ya gawurta ya kuma zama babban harshen hadin kai da tattalin arziki a duniya baki daya.
Ina taya dumbin al'ummar Hausawa murnar Ranar Hausa wadda ake
gudanarwa a fadar Daura mai tarihi"

ʼYan'uwa Hausawa,ku tashi ku kare kan ku da dukiyoyin ku; kowane addinin da dokar Kashashe sun sahale Haka, Allah ya bam...
17/08/2026

ʼYan'uwa Hausawa,ku tashi ku kare kan ku da dukiyoyin ku; kowane addinin da dokar Kashashe sun sahale Haka, Allah ya bamu sa’a, akan ‘yan ta’adda".

Suna cewa ba 'yan ta'adda da ke kashe wasu kabilu ke son raba kawunan 'yan Arewa ba mu da muke kukan ana kashe namu ne k...
17/08/2026

Suna cewa ba 'yan ta'adda da ke kashe wasu kabilu ke son raba kawunan 'yan Arewa ba mu da muke kukan ana kashe namu ne ke son raba kawunan al'umma. Akwai hankali a nan?"

Fuullannii_Bandits sun kashe mutum biyu tare da jagorantar Sallar Juma’a a Babban Masallacin Izalah da ke ƙauyen "Kaya",...
17/08/2026

Fuullannii_Bandits sun kashe mutum biyu tare da jagorantar Sallar Juma’a a Babban Masallacin Izalah da ke ƙauyen "Kaya", a Ƙaramar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sokoto.

Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Juma’ar da ta gabata, inda s**a shafe kusan sa’o’i bakwai suna gudanar da ayyukansu ba tare da wata turjiya ba.

A cewarsa, ’yan bindigar sun tilasta wa mazauna ƙauyen zama a cikin gidajensu, yayin da suke shiga gida-gida suna satar shanu.

Ya ce lokacin da lokacin Sallar Juma’a ya yi, maharan sun nufi Masallacin Izalah, inda s**a yi kiran sallah sannan s**a jagoranci Sallar Juma’ar.

Bayan kammala sallar, sai ’yan bindigar s**a shiga shaguna tare da satar kayayyaki, sannan s**a kai hari ga masu sana’ar POS, inda s**a kwashe kuɗaɗe da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Majiyar ta ƙara da cewa maharan sun bar ƙauyen da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, amma s**a sake dawowa da safiyar Asabar, inda s**a sake kwashe wasu shanu.

Lamarin ya jefa mazauna ƙauyen cikin fargaba da rashin tabbas, yayin da suke ci gaba da nuna damuwa kan tsaron rayukansu da dukiyoyinsu.

"Shugaban ƙungiyar Hausawa ya bayyana cewa a ranar Litinin 17 ga watan Agusta, 2026, ƙungiyar ta kai ziyara gidan gyaran...
17/08/2026

"Shugaban ƙungiyar Hausawa ya bayyana cewa a ranar Litinin 17 ga watan Agusta, 2026, ƙungiyar ta kai ziyara gidan gyaran hali (prison) na Gwauron Dutse a Kano.

A cikin bayaninsa, shugaban ya ce an kai tallafin kayan abinci ga daurarru. A gaban su ne aka raba kayan, inda sama da mutane 400 – mata da maza – s**a amfana da tallafin.

Ya kuma bayyana cewa ya zagaya wani ɓangare na gidan yari don ganin yanayin da yake ciki. A cewarsa, gaskiya akwai bukatar sababbin gine-gine a cikin gidan.

Ƙungiyar ta yi nasarar aiwatar da biyan tarar mutane biyar da ke da ƙananan laifi.
Shugaban ya yi fatan Allah ya saka da alkhairi ga duk waɗanda s**a ba su gudummawa ta hanyar shawarwari da kuɗi. Ya kuma yi addu’ar Allah ya ba daurarru mafita, kuma ya tsare su da shiga irin wannan gida.

"An shigo kasar Hausa da rigar musulunci, an samu karbuwa saboda rigar musuluncin da aka shiga. Ashe, da wata manufa aka...
17/08/2026

"An shigo kasar Hausa da rigar musulunci, an samu karbuwa saboda rigar musuluncin da aka shiga. Ashe, da wata manufa aka shigo. Aka yi wa Kakan nin mu yankan rago, aka kwace masarautan mu da dukiyoyin mu da sunan jihadi" Barr. Ahmed Musa

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya yi kira ga al’ummar Fulani da su gargadi ‘ya’yansu da ke cikin dazuka su dawo...
13/08/2026

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya yi kira ga al’ummar Fulani da su gargadi ‘ya’yansu da ke cikin dazuka su dawo gida su daina aikata laifuka, yana mai cewa satar mutane domin neman kuɗin fansa ta jefa al’ummar cikin zargi da fushin jama’a.

Ya ce:

“’Yan uwana, ba zan ji tsoron faɗa muku gaskiya ba. Duk wanda aka sace a daji, daga baya aka sake shi, zai ce Fulani ne s**a sace shi.

“Saboda haka, ku faɗa wa ‘ya’yanku da ke cikin daji su dawo gida domin mu zauna lafiya. Ba zai yiwu ana sace mutane, ana karɓar kuɗin fansa daga gare su, sannan a ce ba za su yi fushi da ku ba.

“Mutane sun fusata da Fulani. Babu wanda yake hana ku kiwo, ko zuwa makaranta, ko zama cikin lumana. Amma kun san cewa wasu daga cikin ‘ya’yanku suna aikata munanan laifuka ga jama’a. Ko da ba a k**a su ba a yau, wata rana za su fuskanci sak**akon abin da suke yi.”

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The HausaTimes posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category