16/09/2026
WIKKI TOURISTS NA SHIRIN KULLA HULDAR KASA DA KASA
Wani kwararre a harkar tallata wasanni daga Barcelona a kasar Spain, Mr. Gene Joseph, ya isa jihar Bauchi domin tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Wikki Tourists FC kan yiwuwar kulla huldar kasa da kasa.
Gene Joseph ya ziyarci sansanin daukar atisayen kungiyar da ake gudanarwa a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa Stadium, inda ya bayyana fatansa na ganin an kulla kyakkyawar huldar da za ta amfani kungiyar.
Huldar na da nufin kara wa Wikki Tourists damar samun karbuwa a fagen kwallon kafa na duniya, tare da samar da damarmaki na kasa da kasa ga ’yan wasan kungiyar masu hazaka.
Yaya kuke ganin wannan yunkuri na Wikki Tourists ?
Ku yi follow din wannan shafi namu sannan ku yi share domin mutane su gani