Muryar Tofa

Muryar Tofa Shafin Muryar Tofa, shafine wanda zai dinga kawo muku a bubuwan dake faruwa a ciki da wajan karamar hukamar Tofa.

Matashin dan siyasa a karamar hukumar Tofa kuma Shugaban kungiyar APC youths movement, Abubakar Lawan Rabi'u Tofa, ya fi...
13/07/2025

Matashin dan siyasa a karamar hukumar Tofa kuma Shugaban kungiyar APC youths movement, Abubakar Lawan Rabi'u Tofa, ya fice daga jam'iyar APC, tare da magoya bayan sa.

Ku yi follow din wannan shafi namu domin sanin meke wakana a ciki da wajan karamar hukumar Tofa.

Muryar Tofa

Yadda aikin gyaran gadar watari ya ke gudana bisa sahalewar me girma gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, ta hannun mai ma...
08/07/2025

Yadda aikin gyaran gadar watari ya ke gudana bisa sahalewar me girma gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, ta hannun mai magana da yawun gwamnan Hon Sunusi Bature D/Tofa.

Wannan gada nada matukar muhimmaci a wannan yanki duba da tana kan babbar hanyar da ta hada Dawakin Tofa, Tofa, da Rimin Gado. Wannan hanya ta dan gane har karamar hukumar Gwarzo.

Al'ummar wannan yanki na cikin farin ciki bisa wannan aikin gyaran wannan gada a wannan lokaci na damuna.

Muryar Tofa

Yadda wasu ajujuwa suke a firamaren kofar arewa dake cikin karamar hukumar Tofa.Muryar Tofa
07/07/2025

Yadda wasu ajujuwa suke a firamaren kofar arewa dake cikin karamar hukumar Tofa.

Muryar Tofa

A kammala kofin da kansilan mazabar Yarimawa Hon Sagiru Abdullahi Ali, ya saka mai taken Yarimawa soccer competition.Ind...
06/07/2025

A kammala kofin da kansilan mazabar Yarimawa Hon Sagiru Abdullahi Ali, ya saka mai taken Yarimawa soccer competition.

Inda kungiyar kwallon kafa ta FC Gidan Telle ta samu nasarar lashe kofin bayan ta doke FC Kankale, da ci 3-0 a wasan karshe.

Ya yin rufe wannan gasa ta samu halartar shugaban karamar hukumar Tofa Hon Yakubu Ibrahim Adis, da yan tawagar sa.

Muryar Tofa

Kansilan mazabar Yalwa Karama dake karamar hukumar Tofa Hon Isma'il Abubakar Y Karama, ya kammala aikin gyaran ajujuwa 2...
02/07/2025

Kansilan mazabar Yalwa Karama dake karamar hukumar Tofa Hon Isma'il Abubakar Y Karama, ya kammala aikin gyaran ajujuwa 2 a firamaren Yalwa Karama bisa umarnin gwamnan jahar Kano Alh Abba Kabir Yusuf.

Idan an kammala wannan aiki a mazabarku ku tura mana domin sanarwa da duniya halin da yankinka yake ciki.

Muryar Tofa

Yadda al'ummar karamar hukumar Tofa, s**a fito gwanso da kwarkwata s**a domin kallon Mai martaba sarkin Kano Malam Sunus...
28/06/2025

Yadda al'ummar karamar hukumar Tofa, s**a fito gwanso da kwarkwata s**a domin kallon Mai martaba sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi II, lokacin da ya kai ziyara a yau.

Ziyarar ta sarki Sunusi Lamido Sunusi II, ta samu halartar shugaban karamar hukumar Tofa Hon Ibrahim Yakubu Addis, da mai magana da yawun gwamna Kano, Hon Sunusi Bature D/ Tofa, da hakimin Tofa , da dakatai da masu unguwanni na wannan yanki.

Ku yi follow din wannan shafi namu domin sanin meke wakana a yankin karamar hukumar Tofa da kewaye.
Muryar Tofa

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun...😭😭😭Allah yayiwa Alhaji Aminu Alasan Dantata rasuwa jiya juma'a a kasar Dubai, muna ...
28/06/2025

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun...😭😭😭

Allah yayiwa Alhaji Aminu Alasan Dantata rasuwa jiya juma'a a kasar Dubai, muna addu'ar Allah yajikansa yagafarta masa yayi masa rahama don alfarmar shugabanmu Annabi Muhammadu S A W Amin. 🀲🏽🀲🏽🀲🏽

LABARI DA DUMI DUMI.Mai martaba sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi II, zai kawo ziyarar wuni daya karamar hukumar To...
27/06/2025

LABARI DA DUMI DUMI.

Mai martaba sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi II, zai kawo ziyarar wuni daya karamar hukumar Tofa, a gobe asabar domin gaisawa da al'ummar wannan gari da kuma bude wasa ayyuka da shugaban karamar hukumar Tofa Hon Ibrahim Yakubu Addis, ya samar.

Muna kira da a fito a Kalli sarki cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Ku yi follow din wannan shafi namu domin meke wakana a yankin karamar hukumar Tofa da kewaye.
Muryar Tofa

Kana cikin masu sha'awar a sanar da duniya halin da yankinka na karamar hukumar Tofa, take ciki.To ga hanya daya tak ka ...
23/06/2025

Kana cikin masu sha'awar a sanar da duniya halin da yankinka na karamar hukumar Tofa, take ciki.

To ga hanya daya tak ka yi follow din wannan shafi namu sannan ka yi share na wannan shafi domin wasu su gani.

Muryar Tofa a ko'ina za'jimu.

Muryar Tofa

Kamsilan mazabar Yalwa Karama,dake karamar hukumar Tofa, Hon Ismail Abubakar Yalwa na ci gaba da aiwatar da umarnin mai ...
20/06/2025

Kamsilan mazabar Yalwa Karama,dake karamar hukumar Tofa, Hon Ismail Abubakar Yalwa na ci gaba da aiwatar da umarnin mai girma gwamnan jahar Kano Alh Abba Kabir Yusuf, na gyaran makaratu a fadin jahar.

Ku yi follow din wannan shafi namu domin sanin meke wakana a yankin karamar hukumar Tofa da kewaye.
Muryar Tofa

Matasa a karamar hukumar Tofa sun gudanar da taron sada zuminci mai taken Tofa Facebook contect.A wannan taro anci ansha...
12/06/2025

Matasa a karamar hukumar Tofa sun gudanar da taron sada zuminci mai taken Tofa Facebook contect.

A wannan taro anci ansha an kuma sada zuminci tsakanin matasan wannan yanki.

Ku yi follow din wannan shafi namu domin sanin meke wakana a yankin karamar hukumar Tofa da kewaye.
Muryar Tofa

Wannan itace babbar hanyar da ta tashi daga kwanar gidan baban kado zuwa yan sabo zuwa bugai ta hada da garin jobe ta wu...
12/06/2025

Wannan itace babbar hanyar da ta tashi daga kwanar gidan baban kado zuwa yan sabo zuwa bugai ta hada da garin jobe ta wuce ta kwami ta dangane da babban titin gwarzo road dake karamar hukumar Tofa.

Ko yaushe kuke sa ran za'ayi wannan babban aikin titin dake ciwa mutanan wannan yanki tuwu a kwarya.

Ku yi follow din wannan shafi namu domin sanin meke wakana a yankin karamar hukumar Tofa da kewaye.
Muryar Tofa

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Tofa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share