Latest Post

Latest Post Latest news from Nigeria

Kowa yana da damar shiga jam'iyyarmu - APC Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan rade-radin da ake yi na cewa tsohon gwa...
01/07/2025

Kowa yana da damar shiga jam'iyyarmu - APC

Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan rade-radin da ake yi na cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso na shirin shiga jam’iyya mai mulki ta APC gabanin zaben 2027

Me za ku ce?

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Barau I. Jibrin da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta A...
01/07/2025

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Barau I. Jibrin da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun isa birnin Madina na kasar Saudiyya domin gudanar da jana’izar dattijo kuma hamshakin dan kasuwa Marigayi Alhaji Aminu Dantata.

Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai ga mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ismail Mudashir, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ko me hakan ke nufi da jarumi Mustapha Badamasi Nabraska ya bayyana?
01/07/2025

Ko me hakan ke nufi da jarumi Mustapha Badamasi Nabraska ya bayyana?

Shugaban riko na jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya tabbatar da Sam...
01/07/2025

Shugaban riko na jam’iyyar PDP na kasa, Umar Damagum, ya bayyana cewa kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa

Damagum ya bayyana hakan ne a Abuja bayan kammala babban taron ta na kasa da ya gudana a hedkwatar jam’iyyar

Za'a fita sallar roƙon ruwa a KatsinaBabban limamin masallacin juma'a na unguwar rahamawa dake cikin birnin Katsina Mala...
30/06/2025

Za'a fita sallar roƙon ruwa a Katsina

Babban limamin masallacin juma'a na unguwar rahamawa dake cikin birnin Katsina Malam Bilyaminu Balarabe Muhammad, ya bukaci al'ummar musulmai a jihar da suyi ta neman tuba da istigfari domin samun ruwan sama.

Ya bayyana cewa idan har ba,a samu ruwan sama ba za,a fita sallar istisqa,I watu sallar rokon ruwa a ranar Laraba da karfe 8:00 na safe a masallacin GRA da ke jihar

An hallaka shugaban jam’iyyar APC a KatsinaRahotanni sun bayyana cewa an hallaka shugaban jam’iyyar APC dake a kauyen Gu...
30/06/2025

An hallaka shugaban jam’iyyar APC a Katsina

Rahotanni sun bayyana cewa an hallaka shugaban jam’iyyar APC dake a kauyen Guga a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Majiyar Latest Post ta ruwaito cewa wani dan jarida mai suna Bakatsine ya wallafa hakan a shafinsa na X yana mai cewa an hallaka shugaban jam'iyyar na APC bisa zargin taimakawa 'yan fashin daji a yanki.

An Dage Jana'izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Zuwa Gobe Talata Saboda Rashin Isowar Gawar Da Wuri A Kasa Mai Tsarki
30/06/2025

An Dage Jana'izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Zuwa Gobe Talata Saboda Rashin Isowar Gawar Da Wuri A Kasa Mai Tsarki

Da Dumi-Dumi:Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar da za'a gudanar ranar 24 ga watan Yul...
30/06/2025

Da Dumi-Dumi:

Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar da za'a gudanar ranar 24 ga watan Yuli a Abuja.

Mace mai kamar maza!A tsakiyar samarinnan wata hazikar mace ce daga cikin jami'an tsaron al'umma na jihar Katsina da ake...
30/06/2025

Mace mai kamar maza!

A tsakiyar samarinnan wata hazikar mace ce daga cikin jami'an tsaron al'umma na jihar Katsina da ake shiga daji da ita domin farautar yan fashin daji a yankin karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina

Wane fata za ku yi mata?

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugabancin ...
30/06/2025

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya tabbatar da cewa zai tsaya takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027

Jirgin karshe na mahajjatan jihar Kebbi sun dawo gida bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2025 a kasar SaudiyyaJirgin da...
30/06/2025

Jirgin karshe na mahajjatan jihar Kebbi sun dawo gida bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2025 a kasar Saudiyya

Jirgin da ya dawo da alhazai 418, ya sauka a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello a yammacin ranar Lahadi bayan kammala aikin jigilar alhazai a jihar.

Wata sabuwa I ji yan......... Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa nan gaba kadan gwamnonin Kano da Rivers, Plateau har ma ...
30/06/2025

Wata sabuwa I ji yan.........

Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa nan gaba kadan gwamnonin Kano da Rivers, Plateau har ma da Bayelsa za su fice daga jam'iyyun su su koma APC

Me za ku ce?

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Latest Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Latest Post:

Share