28/06/2024
Abu na uku, idan har sunsan tarihi, Galadima Yusufu da suke zagi ai shine gatan iyayen gidan nasu da suke karewa. Ba dan ya jagoranci yakin basasar da suke cewa an zubar da jini ba, da Sarki Abbas mahaifin Abdullahi bayero bai zama Sarki ba ballantana suma suzo suyi. Abbas wanda kanin Galadima yusufu ne shine ya taka rawa mafi girma a wannan yaki har a bangaren zubar da jini da suke fada, domin kuwa da shi da Barde Abdu Nagwangwazo sune s**a kashe Sarkin Kano Tukur da Galadima Ibrahim Malanta wanda shi ma dan uwansu ne kuma sirikin Abbas dinne ma, saboda shine mahaifin Mariyatu matar Abbas wacce ta haifi Sarki Abdullahi bayero. A lokacin ma Galadima Yusufun ya rasu kuma yayi wasiyya kada a kashe Tukur, amma a k**a shi a sa yayi mubaya'a. Abbas ya taka rawa a lokacin basasa da kuma bayan ta, da shirya tuggu iri iri na siyasar mulki a lokacin Sarki Alu wanda ya gaji Galadima Yusufu, har sai da shi Abbas din ya sharewa kansa hanyar zama Sarki bayan zuwan turawa. Saboda haka idan akwai wanda yayi barna a lokacin basasa kuma yaci moriyarta bayanta, to bai kai ya Sarki Abbas da zuriyar sa ba. Ku duba ku gani!
Daga karshe, duk da Abba gida gida bai dakko wani daga cikin zuri’arsu ya nada shi Sarki ba, amma ko yanzu ya cikawa Galadima Yusufu burinsa. “dukda cewa yanzu haka Kimanin Shekaru 60 babu ko Mai Unguwa" a cikin zuri'ar Galadima Yusufu, k**ar yacce jahilan s**a fada, amma ayau jininsa ne yake GWAMNAN KANO, kujerar da wani daga gidan sarautar Kano (gidan sullibawa dama sauran gidajen hijira da jihadi) bai taba hawa ba! Abba ya cikawa Galadima Yusufu burinsa, ya rushe illa da barnar da Ganduje (Abdu Danyen Kaso na wannan zamani) yayi wa Masarautar Kano! Abinda Abdu Danyen Kasko na wancan zamanin yake gani shine mai bayarwa (Sarauta) saboda haka ya hana Galadima Yusufu, to yau gashi Allah Ya damka silar bayar da ita (Sarautar Kanon gaba daya) a hannun jikan Yusufu. Abba Ya cire "Sarkin" Kano, ya nada Sarkin Kano mai cikakken iko. Sai yaya kuma?!!!