12/01/2026
Gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta Kasa ASUU za su gudanar da wata sabuwar yarjejeniya da za ta inganta tsarin ilimin jami’o’in Kasar.
A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar a ranar Lahadi, ta ce za a gudanar da taron a ranar Laraba 14 ga watan Junairu a dakin taro na Asusun Tallafawa Manyan Makarantu TETFund da ke Maitama Abuja.
Ministan Ilimi Dakta Maruf Tunji Alausa, da Karamar Ministan Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmad ne za su jagoranci taron.
Hakan dai na zuwa ne biyo bayan wa'adin kwanaki 14 na baya-bayan nan da kungiyar ta yi, na shirga yajin aiki.
Sai dai daga baya kungiyar ta dakatar da yajin aikin kafin ta tsunduma bayan kungiyar da gwamnatin tarayya sun gudanar da wata tattaunawa.
Daraktan yada labaran Ma’aikatar Folasade Boriowo ce ta bayyana ta cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu, ta ce an tsara yarjejeniyar ne bayan shafe shekaru da dama ana tattaunawa tsakanin gwamnatin da ASUU don magance matsalolin kungiyar.
A cewar ma’aikatar, yarjejeniyar ta yi daidai da shirin sabunta fatan na Shugaba Bola Tinubu, wanda ya amince da ilimi a matsayin dabarun ci gaban kasa, ci gaban al'umma, da tattalin arziki.
Haka kuma ana sanya ran yarjejeniyar za ta kara inganta zaman lafiya a makarantu, samar da ingantaccen yanayin ilimi, da kuma karfafa amincewa tsakanin dalibai, ma'aikatan jami'a, da sauran jama'a.
A cewar ma’aikatar kaddamar da yarjejeniyar za ta hada manyan jami’an gwamnati, wakilan kungiyar ASUU, shugabannin manyan makarantu, da ‘yan jarida.