31/01/2025
Karramawar Shugaban Asibiti Mafi Ƙwazo ta Jihar Kano.
Shugabar Asibitin Sheikh Muhammad Jidda (Asibitin Kuroda) kuma Shugabar Shiya ta Tara karkashin Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dr. Fatima Ibrahim Hamza PT, MNSP, ita ce ta lashe Karramawar Gwarzuwar Shugabar Asibiti Mafi Ƙwazo ta 2024 wace Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta gudanar a kwanakin baya a harabar hukumar da ke nan Kano.
Karramawar ta samu halartar Maigirma Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf da Maigirma Shugaban Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dr. Mansur Nagoda.
Karramawar tata na zuwa ne duba ga irin jajircewarta wajen kawo sauya-sauye na cigaban asibitin, kyautata aiki, tare da kyautata walwalar marasa lafiya da ma'aikatan asibitin bakiɗaya.
© Physiotherapy Hausa