06/06/2022
TAMBAYA GAREMU
A yanzu da ake tsaka da hada hadar siyasa a Nigeria, jam'iyyu suke ta fitar da Mutanen da zasuyi musu takara a kowanne bangare, su kuma al'ummar gari masu jefa kuri'a suke da shirin zabar wanda suke kauna ko suke ganin k**ar zaiyi musu abun da suke so.
A Nigeria babu wadataccen Tsaro, kayan masarufi suke kara hauhawa, ganin likita yake kara zama lamari na kudi, yan makarantar gaba da Secondary suke zaune a gida, karatu yayi tsada, abunci yake neman gagarar da yawa cikin al'umma.
GA TAMBAYAR......
Tsakaninka Da Allah, zaka yi zabe ne da cikekken tunanin wanda zaka zaba zaiyi maka aikin gyara kasarka, ko kuwa dai zakayi zabe ne saboda dan takarar yana jam'iyyarka ne, ko zakayi zabe ne saboda kana kaunar wanda zaka zaba..
Shin a zuciyarka kana da amincin yan siyasa suna neman mulki ne saboda jin dadinka, ko kuwa saboda kansu suke nema.