Taskar Jaridu

Taskar Jaridu Taskar Jaridu Shafin Samar da labarai Na Cikin Gida Har Da Kasashen Ketare, Kana Da Kuma Isar Da Koken Talakawa Zuwaga Shugabanni Cikin Gaggawa...

Labarin da wasu ke yaďawa akan cewa Kasar Saudiyya ta ďauki Farfesa Maqary Limanci ba Gaskiya bane, Daga Sheikh Mustapha...
21/08/2022

Labarin da wasu ke yaďawa akan cewa Kasar Saudiyya ta ďauki Farfesa Maqary Limanci ba Gaskiya bane, Daga Sheikh Mustapha Adinga

In akwai wanda yafi fir,auna zalinci dashi ya kamata a kwatanta buhari saboda shi fir,auna baya cutar da masoyansa Amma ...
25/07/2022

In akwai wanda yafi fir,auna zalinci dashi ya kamata a kwatanta buhari saboda shi fir,auna baya cutar da masoyansa Amma buhari kashe su ma yakeyi 🤧

Parfesa Suleiman Sanadi

Allah ya jikan Nura Mustapha Waye..
03/07/2022

Allah ya jikan Nura Mustapha Waye..

Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa ha...
03/07/2022

Ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya gargaɗi magoya bayansa da su rinƙa haƙuri da ra'ayoyi mabambanta na ƴan Najeriya don kada hakan ya hana yin maja da wasu jam'iyyu a nan gaba.

Mista Obi ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya gode wa magoya bayan nasa dangane da irin haɗin kan da suke ba shi.

Jan kunnen nasa na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa yunurinsu na yin haɗaka da jam'iyyar NNPP da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bai yi nasara ba saboda sun kasa daddalewa kan wanda za a mara wa baya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa duk da an san halin da ake ciki a Najeriya na fushi da takaici, "ya zama wajibi a yi amfani da kuzarin da ake da shi wurin samun goyon bayan wasu da kuma haɗin kai".

Obi ya yi kalaman ne bayan Rabiu Kwankwaso ya ce ba zai iya zama mataimakin wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba a babban zaɓen 2023.

Waɗannan kalamai na Kwankwaso sun jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda magoyan Obi s**a dinga s**arsa da kalamai marasa daɗin ji.

Gimbiya Online ✍

Dalibai yan asalin jihar Kano sun yi tur da tofin Allah tsine ga shugaban kungiyar daliban Comr Yahya Usman Kabo bisa si...
24/06/2022

Dalibai yan asalin jihar Kano sun yi tur da tofin Allah tsine ga shugaban kungiyar daliban Comr Yahya Usman Kabo bisa siyasantar da kungiyar daliban da yake yi da sunan neman kuɗi.

Daliban sun kara bayyana cewa shugaban nasu babu abinda yake yi sai son zuciya tare da nuna dalibai a matsayin kwadayayyu alhali miyarsa kawai yake wankewa da sunan dalibai.

Cikin fushi wani dalibi mai suna Muhammad Musa ya sake jaddada cewa duk abinda shugaban yake yi cin mutuncin dalibai yan asalin jihar Kano ne kuma suna Allah wadai da abinda yake yi.

Wannan duk yana biyowa ne bayan shirin da shugaban daliban yayi ma yin taron marawa APC baya a jihar Kano a ranar Lahadi mai zuwa.

Rahotan: Nigerian New's Hausa

"An gano wasu biliyoyin kudade a gidan buratai dake Abuja, kudaden da ake kaddara na makamaine da gwamnati ta bayar.
23/06/2022

"An gano wasu biliyoyin kudade a gidan buratai dake Abuja, kudaden da ake kaddara na makamaine da gwamnati ta bayar.

Musulmi Dan Shekara 30 Ya Auri Kirista Mai Shekaru 75 A Jamus Daga Barista Nuraddeen Isma'eel"Wani matashin balarabe Dan...
22/06/2022

Musulmi Dan Shekara 30 Ya Auri Kirista Mai Shekaru 75 A Jamus

Daga Barista Nuraddeen Isma'eel

"Wani matashin balarabe Dan asalin kasar Iraqi mai suna Muhammad, ya auri wata tsohuwa mai shekaru 75 ita kuma haifaffiyar kasar Jamus."

"Rahoton yacigaba da bayyana cewa! Ya hadu da baturiyarne mai suna Jessica a kasarsu ta jamus bayan sharfe shekaru 7 yana zaune a kasar."

"Majiyar bai boye Mana komaiba; inda Matashi Muhammad s**a kwashe wasu lokuta masu tsayin gaske suna soyayya da juna, bisani baturiya Jessica taji Kawai burinta ta auri wannan matashi, ba'ayi wata-wataba baturiyan ta fara bude masa ido da kudi, kanama hadda bashi mota ta miliyan "350" a domin ya fattama a gari."

Daga karshe dai Muhammad ya yarje an daura masa aure da Jessica."

2023 | Engr Abubakar Matazu  Yayi kira Ga kungiyoyi da Matasa cewa suyi structure tun daga mazaba {poling Unit} zuwa sam...
22/06/2022

2023 | Engr Abubakar Matazu Yayi kira Ga kungiyoyi da Matasa cewa suyi structure tun daga mazaba {poling Unit} zuwa sama, saboda kuri'a daga mazabu ake kirgata,

kuma yayi kira Ga Al'ummar Jihar Katsina kan Su Fito ƙwansu da Ƙwarkwata Suyi wa Dr Dikko Umar Raɗɗa Ruwan ƙuri'u a babban zaɓe Mai zuwa na 2023 Domin kawowa jihar Katsina Cigaba..

Kasan Cewar Gwagware Katsina Dr Dikko Umar Raɗɗa Kan kujerar Gwamnan Jihar Katsina Abun alfahari ne
Saboda zai tsaya a ko'ina a duniya ya kare martabar jahar shi ko a gaban waye ba zaaji kunya ba. Kuma zaka bugi gaba kace wannan Gwamna na ne.

Kuma in mukayi tawakkali ga Allah, to lallai Allah zai kawo mana Canje-canje Masu Yawa, Kamar Fannin Lafiya, Fannin Ilmi, Bunƙasa Tattalin arzikin Jiha, Fannin tsaro, da Raya Gari..

Injiniya Abubakar Matazu Ya ƙara Da Cewa" Tabbas a daidai Irin Wannan Lokacin Jihar Katsina tana Buƙatar Gwarzo, Jajirtacce Mai ilmin Islama da Boko wanda ya mika ma Allah tafiyar shi gabadaya kuma Allah ya shige mashi gaba kamar PhD Dr Dikko Raɗɗa.

Allah yayi mana jagora Duniya da lahira ameen

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN Babban Limamin Masallacin Juma'a Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna Ya RasuAllah Ya ...
22/06/2022

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN

Babban Limamin Masallacin Juma'a Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna Ya Rasu

Allah Ya Yi Wa Babban Limamin Masallacin Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna, Sheikh Dahiru Lawal Abubakar Rasuwa.

Ya Rasu A Asibitin Sojoji Ta 44 Bayan Yar Gajeruwar Rashin Lafiya.

Za'a Yi Jana'izarsa Da Misalin Karfe 1:00 Na Rana A Masallacin Juma'a Dake Titin Maiduguri A Jihar Kaduna.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Ƴan Najeriya Sun Gaji Da Jam’iyyun PDP Da APC, Cewar Gwamnan Jihar EdoGwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce ‘yan Nije...
22/06/2022

Ƴan Najeriya Sun Gaji Da Jam’iyyun PDP Da APC, Cewar Gwamnan Jihar Edo

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce ‘yan Nijeriya ba su da sha’awar manyan jam’iyyun siyasar kasar nan guda biyu – PDP da APC, kawai suna neman canji ne.

Obaseki yayin da yake hira da gidan Talabijin na AIT, bayan Kammala zaben gwamnan jihar Ekiti, ya bayyana cewa makomar siyasar kasar nan tana canzawa.

Gwamnan Edo ya ce, “Ta yaya PDP a tarihin ta na girma ace ba ta yi nasara Ba? Ba ta zo na biyu ba ma.

Don haka, za ku iya ganin cewa wani abu yana faruwa. Makomar siyasarmu a kasar nan tana sauyawa.

Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Karɓi Sunan Sanata Ahmed Lawan Wanda Bai Shiga Takara Ba, Maimakon Na Shariff Machina Wanda Ya ...
21/06/2022

Dalilin Da Ya Sa INEC Ta Karɓi Sunan Sanata Ahmed Lawan Wanda Bai Shiga Takara Ba, Maimakon Na Shariff Machina Wanda Ya Lashe Zaɓe, Inji Kwamishinan Zaɓe

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana dalilan da ya sa ta aikata abin da wasu su ka yi wa fahimtar cewa kamar ta yi son kai wajen karɓar sunayen wasu 'yan takara da ake ganin cewa ba su shiga zaɓen fidda gwani ba.

Sunan Sanata Ahmad Lawan, wanda shi ne Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayyana a jerin sunayen 'yan takarar da APC ta damƙa wa INEC alhali ko takarar zaɓen fidda gwani bai shiga ba.

Sai dai kuma INEC ta ƙi karɓar sunan tsohon Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, wanda shi ma takarar shugaban ƙasa ya tafi kamar Lawan, sai daga baya ya garzaya neman takarar sanata a makare.

Lawan dai bai shiga takarar sanata ba, takarar shugaban ƙasa ya shiga, amma sai ga sunan sa APC ta bayar ga INEC a matsayin halastaccen ɗan takarar da ya ci zaɓen fidda gwani.

Yayin da Kwamishinan INEC na Tarayya da ke Jihar Akwa Ibom Mike Igini ya haramta wa Akpabio shiga jerin 'yan takara, shi kuwa Lawal ya samu shiga kai-tsaye, duk kuwa da ƙorafi da barazanar da wanda ya lashe zaɓen ya yi.

Wannan ne ya sa masu sharhi, lauyoyi da 'yan siyasa ke cewa INEC ta nuna son kai, ta ƙi yi wa Machina adalci, sannan ta fifita Lawan kan Akpabio.

A martanin da Mohammed Haruna na INEC ya yi wa marubuci Farooq Kperogi, ya bayyana cewa, "INEC ba ta da ikon ƙin karɓar ko ma sunan wanene jam'iyya ta kai mata.

"Jam'iyya ce ke da ikon gudanar da zaɓe, ita kuma INEC doka cewa kawai ta yi ta je ta sa ido ta ga yadda aka gudanar da zaɓe, ta kai rahoto a hedikwata, idan an bi ƙa'ida ko ba a bi ba.

"Ƙarfin INEC a nan shi ne duk wanda ya kai ƙara kotu cewa an yi masa rashin adalci a zaɓen, to da rahoton mu zai yi amfani ya kai ƙara, kotu ta ƙwatar masa takarar sa."

Kafafen yaɗa labarai sun ba da labarin yadda Akpabio ya shiga zaɓe a makare, da kuma yadda kotu ta haramta wa INEC ta haramta wa APC shiga zaɓen gwamna a Jihar Akwa Ibom.

Sannan kuma an buga labarin da Machina ya ce canja sunan sa da na Sanata Lawan rashin mutunci ne, zai garzaya kotu.

Bashir Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin APC na Sanatan Yobe ta Arewa, ya bayyana cewa ya yi mamakin ganin yadda APC ta maye sunan sa da na Lawan a jerin sunayen da ta miƙa wa INEC.

Ya ce ya yi mamaki, amma dai ya na fatan kuskure aka tafka, kuma shi ne halastaccen ɗan takarar, wanda ya shiga zaɓen fidda gwani, kuma ya samu ƙuri'u 280, alhalin Sanata Lawan ko takara bai shiga ba.

Machina, wanda tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Harkokin Jiragen Ruwa ta Ƙasa ne, ya ce maye sunan sa da sunan Lawan rashin mutunci ne kuma tantagaryar rashin imani ne.

Lawan dai ya yi watsi da shiga takarar sanata, ya shiga takarar shugaban ƙasa. Sai bayan da ya janye a ranar zaɓen fidda gwani ne, bayan nasarar Bola Tinubu, sai ya zabura neman kujerar sanata, ko ta halin ƙaƙa, bayan an yi zaɓe, har Machina ya yi nasara.

Sashe na 31 na Dokar Zaɓe ya ce za a iya canja sunan ɗan takara idan ya mutu ko kuma ya janye don kan sa, ta hanyar rubuta wa INEC wasiƙar sanarwar janyewar.

Machina, wanda ya taɓa yin ɗan Majalisar Tarayya a Jamhuriya ta Uku, ya yi gargaɗin idan ba a mai da sunan sa ba, zai yi ƙara.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Jaridu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Taskar Jaridu:

Share