Taskira - H Online Tv

Taskira - H Online Tv Mun samar muku da Taskira Online TV domin samun Ingantattun labarai, rahotanni da kuma sharhuna kan

HOTUNA: Yadda ’yan sanda s**a fara kamen takardun motoci a wasu sassan Najeriya.Daga yau ne doka ta ba jami'an damar bin...
03/02/2025

HOTUNA: Yadda ’yan sanda s**a fara kamen takardun motoci a wasu sassan Najeriya.

Daga yau ne doka ta ba jami'an damar bincike kan takardun ababen hawa don tabbatar da cewa takardun sun cika.

📷 Aminiya:

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta ce ta k**a wani matashi ɗan shekara 22 da laifin yiwa wata yarinya ƴar shekara 15 f...
03/02/2025

Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta ce ta k**a wani matashi ɗan shekara 22 da laifin yiwa wata yarinya ƴar shekara 15 fyade a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Ngurore, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce wanda ake zargin mai suna Luka James da ke ƙauyen Gwalantabal a ƙaramar hukumar Song, an k**a shi ne a Michicka, biyo bayan rahoton da wani mazaunin garin Yohanna Begie ya yi wa ƴan sandan ƙauyen Nkafa.

Tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Sh*ttu, ya ce ƙarin kuɗin kira da data da Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, ta amince d...
01/02/2025

Tsohon Ministan Sadarwa, Adebayo Sh*ttu, ya ce ƙarin kuɗin kira da data da Hukumar Sadarwa ta Najeriya, NCC, ta amince da shi ba ƙaramin kawo ci gaba zai yi ba a harkar tattalin arzikin kasar nan.

Izala Ta Gayyaci Tinubu Da Atiku, Taron Neman Taimakon Naira Biliyan Ɗaya Da Miliyan Ɗari BiyarƘungiyar Izala (JIBWIS) ƙ...
01/02/2025

Izala Ta Gayyaci Tinubu Da Atiku, Taron Neman Taimakon Naira Biliyan Ɗaya Da Miliyan Ɗari Biyar

Ƙungiyar Izala (JIBWIS) ƙarƙashin jagorancin Sheikh Yahaya Jingir ta gayyaci al’ummar Musulmi zuwa babban taron ƙasa da za a gudanar a Abuja.

Za a gudanar da taron a ranakun Asabar da Lahadi, 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2025, a dakin taro na Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da Babban Masallacin Abuja.

Kungiyar za ta kaddamar da asusun neman taimako kudi domin tallafawa harkokin ilimi da ilimantarwa da ya kai har Naira biliyan 1.5 a yayin taron.

Kwankwaso na shirin komawa APC saboda Abba ya ci zaɓe a 2027 – Musa Iliyasu Kusa a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso...
01/02/2025

Kwankwaso na shirin komawa APC saboda Abba ya ci zaɓe a 2027 – Musa Iliyasu

Kusa a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi zargin cewa Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran dariƙar Kwankwasiyya na yunkurin daidaitawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya samu nasarar yin wa'adi na biyu na mulkin jihar a 2027.

Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis, Iliyasu, tsohon kwamishina kuma daraktan kudi na hukumar raya kogin Hadejia Jama’are, ya yi ikirarin cewa Kwankwaso na yunkurin komawa jam’iyyar APC ne domin buƙatar sa ta siyasa.

Ya kuma gargadi Tinubu da kada ya amince da Kwankwaso, domin “zai ci amanar sa a siyasa” k**ar yadda ya yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a baya.

~ Daily Nigerian Hausa

ANA WATA GA WATA: Ina ganin zan dakatar da Shirin da na ke yi a harshen Hausa  - Inji mai gabatar da shirin Brekete Fami...
01/02/2025

ANA WATA GA WATA: Ina ganin zan dakatar da Shirin da na ke yi a harshen Hausa - Inji mai gabatar da shirin Brekete Family, bayan cece-kucen da ya ɓarke game da abin da ya faru tsakanin sa da Seaman Abbas da Matar sa Hussaina.

AYAR TAMBAYA: Duk Arewacin Nigeria ba dan siyasa da ba dan Kasuwa ba yake da irin gidan da Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso yak...
01/02/2025

AYAR TAMBAYA: Duk Arewacin Nigeria ba dan siyasa da ba dan Kasuwa ba yake da irin gidan da Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso yake dashi a Abuja.

Sannan duk jihar Kano, har Wanda yafi kowa kudi a Afirika ma, gidansa bai kai na Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da yake dashi a Mila Road ba.

Muna so ya fito yai mana bayanin yadda ya samu kudi, dan mun san ko kamfanin sabulu bashi da dashi."

Cewar ~ Hon. Sale Kala Kawo dan Jam'iyyar APC

01/02/2025

SIYASAR KANO SAI KANO: Tsohon kwamishina a jihar Kano Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, Ya bayan gaskiyar magana akan satar Agwagwa da ƴan Kwankwasiyya ke fada min.

Ya ƙara da cewar maganar na saci Agwagwa ni ɗan ƙauye ne, amma su Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a shekara 50 baya Awaki suke k**awa su ci ba da niyyar sata ba - Inji Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso

HOTUNA: Yadda gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, Ya ƙaddamar da Titin Fulatan zuwa Zarewa da Danguzuri, mai tsa...
31/01/2025

HOTUNA: Yadda gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, Ya ƙaddamar da Titin Fulatan zuwa Zarewa da Danguzuri, mai tsawon kilomita 9 a yankin ƙaramar hukumar Rogo, wanda ma’aikatar bunƙasa noma da kiwo ta Jihar (KSADP), ta yi tare da haɗin gwuiwa da Bankin Musulunci da sauran abokan hulɗa.

Kazalika, Gwamnan ya yi amfani da damar wajen sanar da amincewar sa na bayar da aikin titin Rogo zuwa Bari da Falgore da Mahangi, Domin sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyakin gona da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziƙin yankin.

Hukumar Hisbah a Katsina ta k**a wasu samari da su ka yi shigar mata za su je neman aure.
31/01/2025

Hukumar Hisbah a Katsina ta k**a wasu samari da su ka yi shigar mata za su je neman aure.

HOTUNA: Yadda Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, ya yi Sallar Juma'a tare da Khalifan Tijjaniyya na Duniya, Sheikh Ibrahim...
31/01/2025

HOTUNA: Yadda Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, ya yi Sallar Juma'a tare da Khalifan Tijjaniyya na Duniya, Sheikh Ibrahim Inyass, Sheikh Mahi Inyass a Masallacin Fadar Shugaban Kasa.

Bayan idar da sallar, Khalifan ya yi wa Nijeriya addu'ar zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, Kana ya yi wa Shugaba Tinubu, fatan nasara a ayyukan raya ƙasa da yake.

Rundunar ƴan Sanda ta yi bajakolin ɓarayi da kayan da s**a sata a babban birnin tarayya Abuja mafi yawancin su matasa ne...
31/01/2025

Rundunar ƴan Sanda ta yi bajakolin ɓarayi da kayan da s**a sata a babban birnin tarayya Abuja mafi yawancin su matasa ne.

Cikin Hotuna: Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi holan bamabaman da ta ce ta k**a a Kano.Idan za a iya tunawa tun da f...
31/01/2025

Cikin Hotuna:

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi holan bamabaman da ta ce ta k**a a Kano.

Idan za a iya tunawa tun da farko rundunar yan sandan jihar Kano ta fitar da sanarwa cewa a kwai barazar tsaro, A ranar da za a gudanar da biki Maulidin lamarin ke nan da ya haifar da cece kuce musamman a tsagin gwamnatin jihar da al'umma s**a ringa ƙaryatawa.

📸 SP Abdullahi Haruna Kiyawa

Abin da aka yi wa Sheikh Bin Othman k**ar mutum ne yana da tsohuwar motarsa kiya-kiya yana lallaɓawa, sai wani attajiri ...
30/01/2025

Abin da aka yi wa Sheikh Bin Othman k**ar mutum ne yana da tsohuwar motarsa kiya-kiya yana lallaɓawa, sai wani attajiri ya ce zai siya masa sabuwar Hayis fil fisabilillahi.

Bayan Mallam ya sadakar da tsohuwar motarsa, kuma sabuwar mota ta zo, sai wannan attajiri ya ce yanzu sabuwar motar nan fa direbobi 4 ne za su ke aiki akanta; kuma shi (attajiri) ne zai dauki kwandasta da mai karɓar balas; kuma dole manaja ne yanzu zai riƙa sallamar direbobi.

Wasu na yin yan ƙorafe-ƙorafe a kan Bin Othman. Ni dai na san mutum tara yake bai cika goma ba, kuma duk matsalar Bin Othman tunda ba canja aƙida ya yi ba, kuma ba alfasha yake yi ba, ban ga dalilin kawar da shi daga jagorancin gudanarwa da limancin masallacin Sahaba ba.

Dan mutum ya biya an yashe wa mutane rijiya, bai k**ata ya ce shi zai zaɓi kalar guga da mai janyo ruwa a rijiyar ba.

Daga Ja'afar Ja'afar

GWANIN SHA'AWA: Dattijo Alhaji Aliyu Shattiman Jega kenan tare da ƴaƴansa maza biyar cikin kakin hukumomin tsaron Najeri...
30/01/2025

GWANIN SHA'AWA: Dattijo Alhaji Aliyu Shattiman Jega kenan tare da ƴaƴansa maza biyar cikin kakin hukumomin tsaron Najeriya daban-daban da su ke yi wa aiki.

Ku saka musu albarka.

📸Jafar Aliyu

Umar Garba (Omer Can) Daya Daga Cikin Sabbin Yan Sandan Da Sukayi passing out a ranar alhamis din Data Gabata ya rasu.Mu...
30/01/2025

Umar Garba (Omer Can) Daya Daga Cikin Sabbin Yan Sandan Da Sukayi passing out a ranar alhamis din Data Gabata ya rasu.

Muna addu'a Allah ya jiƙan sa

Wani ɓatagari kenan da jama'ar gari su ka k**a a ƙauyen Watuolo da ke ƙaramar hukumar Ado ta jihar Benue yayin da su ke ...
30/01/2025

Wani ɓatagari kenan da jama'ar gari su ka k**a a ƙauyen Watuolo da ke ƙaramar hukumar Ado ta jihar Benue yayin da su ke ƙoƙarin lalata turakun wutar lantarkin Najeriya na Unguaji-Makurdi, A ranar Asabar da ta gabata.

AN KIRA NI DAGA SAMA: Ku je kawai za mu haɗu a gaban Allah a yi mana Hisabi – Martanin Jamila Ibrahim ga waɗanda s**a di...
30/01/2025

AN KIRA NI DAGA SAMA: Ku je kawai za mu haɗu a gaban Allah a yi mana Hisabi – Martanin Jamila Ibrahim ga waɗanda s**a dinga zagin ta kan badaƙalar Seaman Abbas a kwanakin baya.

Jamila ta ce yanzu haka jama'ar da s**a dinga zagin ta a lokacin saboda ta ce an kira ta daga sama akan ɗabi'un Seaman Abbas suna ta tagging ɗin ta suna neman ta yafe musu.

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskira - H Online Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Taskira - H Online Tv:

Share