03/12/2024
Kaushin Kafa/Faso
Kowa yana iya yin fason kafa musamman a dunduniya. A lokacin sanyi anfi samun wannan matsalar, wani ba zai san ya fara kaushi ba sai yaji kafar sa tana yankar bargon sa zai yagashi sannan zai fahimta
✋ Ba wani abu mai ta da hankali bane kaushi a kafa, saboda yana da hanyar kariya kuma yana da magani mai sauki in an dauki mataki da wuri mai kyau.
In kafa ta bushe ko don saboda rashin mai ko tsayuwa sosai, tafiya da kafa ba tare da takalmi ba sai kafan ta fara tsagewa. Ga Masu ciwon sugar yana yin tsanani sosai, musanman in cuta ta shiga ciki. Ya na kai ga gyambon kafa na masu ciwon suga.
❌ Kuskuren da wasu keyi shine amfani da razor wurin kankare kaushin ƙafa,
Wani lokacin s**an ji ciwo wa kansu, ya shiga ciki sosai, ya dawo ciwo/faso wanda zai dinga musu zafi a lokacin tafiya.
Hanyoyi masu sauki wurin kawar da kaushi sun hada da...
👉 Jika kafa a ruwan ɗumi ya kai minti 15 zuwa sama. Waton kafar ta jika sosai. Sai a yi amfani da abun gogewa. a goge kafar da kayau.
👉 Sai A tsantsame kafar a share da towel ta bushe tsaf.
👉 Ayi amfani da mai (vaseline, man kwakwa, olive oil/man zaitun) a shafa a kafar.
👉Ayi amfani da safa ko sau ciki.
👉 Ga wanda ta tsage sosai ta na zugi, suna bukatan maganin zugin da ya dace da su.
👉 Akwai wanda kwayar cuta take shiga ya kumbura, wannan sai sun ga likita kwararre a asibiti ya basu maganin da ya dace.
In har za'a bi a hankali za'a rabu da wannan matsalar ta kaushi a hankali..
Ayi haƙuri kar ayi gaggawa