08/05/2025
An bayyana wannan mataki ne a wani taron tattaunawa da ake yi duk bayan lokaci wanda ya gudana a Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, tsakanin jami’an gwamnati da shugabannin kafafen yada labarai. Kwamishinan Yada Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagoranci taron.
A cewar wata sanarwa da Sani Abba Yola, Daraktan al'amura na musamman na ma’aikatar ya sanya wa hannu, an dauki wannan mataki ne “domin hana yaduwar kalaman da ka iya tayar da rigima” da kuma kare hadin kan addini da al’adun mutanen jihar.
“Ba ma kokarin takura ‘yan adawa ba,” in ji Kwamared Waiya a yayin jawabi ga shugabannin kafafen yada labarai. “Burinmu shi ne kare al’adu da dabi’u da addini na Kano.”
An cimma wasu matsayai na daban a yayin zaman. “Duk wanda zai bayyana a kafafen yada labarai domin tattaunawa dole ne ya rattaba hannu a wata takarda da ke nuna alkawarin kin amfani da kalaman batanci, cin mutunci, ko na cin zarafin,” in ji sanarwar.
An kuma umurci masu gabatar da shirye-shirye da su kauce wa tambayoyi masu tayar da hankali ko “nuna alamu da ka iya janyo amsoshin da za su bata suna ko kuma su kaskantar da martabar Jihar Kano.”
Kwamared Waiya ya ce an rage yawan amfani da kalaman batanci a shirye-shiryen rediyo da talabijin, yana mai danganta hakan da ci gaba da tuntuba da fahimtar juna da ke gudana tsakanin ma’aikatar da kafafen yada labarai.
Ya kara da cewa gwamnati ta kaddamar da shirye-shiryen wayar da kai ga masu gabatar da shirye-shiryen siyasa, masu sharhi a kafafen yada labarai, da mambobin Majalisar Limaman Juma’a.
“Muna son ganin sakonni suna zuwa cikin natsuwa da gaskiya, ba tare da cin zarafi ko wani abu da zai tauye mutuncin jiharmu ba,” in ji Waiya.