Ordinary Sheik

Ordinary Sheik We are here for you and with you....

03/09/2026

China, Russia and Turkey

03/09/2026

Karshen Kudi

In 1890 there was a greek philosopher called Zerecptachiebonoateh... since you skip the name I'm not telling you the sto...
03/09/2026

In 1890 there was a greek philosopher called Zerecptachiebonoateh... since you skip the name I'm not telling you the story again 🧑‍🦽
‎

To fa!
29/08/2026

To fa!

Sanya mana Kalmar ``Tsula`` a Jumla
24/08/2026

Sanya mana Kalmar ``Tsula`` a Jumla

بسم الله الرحمن الرحيم
23/08/2026

بسم الله الرحمن الرحيم

21/08/2026
BAYANI GAME DA HAƊIN FRUIT SALAD..................................................................Dangane da haɗin Fruit...
19/08/2026

BAYANI GAME DA HAƊIN FRUIT SALAD..................................................................

Dangane da haɗin Fruit Salad da ake sayarwa gefen tituna a robobin takeaway), wanda na fara magana a kwanakin baya ga abin da nake son haska mana.

Gaskiya ne likitoci na bada shawarar a riƙa shan kayan marmari, toh amma fa bisa ka'ida. Ko a fruits kwai wanda za'a ce idan da matsala kaza kar asha. Hakazalik koda ba matsalar komi akwai haɗin da kaima kasan abin yai yawa idan akayi, ance ido ba mudu ba yasan kima.

Shi wannan haɗin mixed fruits salad yana da ɓangarori guda biyu generally:

1. Yana da amfani ga jiki saboda natural ƴaƴan itatuwa dake ciki

2. Kuma yana da babbar illa ko hatsari ga lafiya sakamakon yadda ake sarrafa shi da kuma sinadaran zaƙin da ake ƙarawa ciki.

_______________________________________

1. AMFANIN HAƊIN

Bangaren ƴa'ƴan Itatuwa a tsarin halittar jiki, waɗannan sinadaran suna da matukar amfani idan aka ci su a tsaface kuma ba tare da an haɗa su da abubuwan zaki ba.

Kamar su;

Kankana🍉, Apple🍏, Abarba🍍, da Dabino: Suna ɗauke da tsantsar ruwa da Vitamins (kamar Vitamin C da A), da sinadaran antioxidants dake wanke jiki, ƙarfafa garkuwar jiki, da taimakawa fata.

Ayaba🍌: Tana ɗauke da sinadarin potassium da ke taimakawa zuciya da daidaita hawan jini, gami da bada kuzari nan take.

Kwakwa🥥 da Gyaɗa🥜: Suna ɗauke da maiƙo mai kyau na halitta (healthy fats), protein (gina jiki), da fiber wanda ke gyara ciki da sanya ƙoshi.

_______________________________________

2. RASHIN AMFANI DA HATSARIN HAƊIN

Bangaren lafiya yadda ake haɗa fruits salad ɗin abin damuwa ne kwarai, domin duk da irin amfanin ƴaƴan itatuwan can, hanyar da ƴan kasuwa ke bi wajen haɗawa tana maida wannan haɗi ya zama mai hatsari ga lafiya sakamakon waɗannan abubuwan:

🔲 Yawan sukari da hatsarin kamuwa da ciwon sugar wato excess sugar & diabetes risk. Domin suna amfani da MADARA condensed wacce ke ɗauke da tsantsar sikari mai yawa.

Idan aka haɗa wannan madara mai zaƙi tare da ɗan itace me natural zaƙi na halitta kamar Ayaba, Abarba, Kankana, da Apple, zaƙin abincin yana tsallake ka'ida zuwa matakin da yake da hatsari ga jiki. Karku manta kwanaki na faɗa muku adadin zaƙin da jikin kowa ke buƙata a rana, inda na haska muku cewa zaƙin dake cikin robar soft drinks ɗaya ya wuce ka'ida na daily requirement, toh zaƙin condensed milk yai ma na lemon roba fintinkau sau da sau shurin masaƙi.

A ƙarshe wannan na janyo matsananciyar ƙiba da hauhawar sikari a cikin jini (wanda ke janyo ciwon sugar/diabetes), da lalacewar haƙora...................................................................

Sannan yana janyo cutukan ciki da hanji kamar su taifot, ulcer, gudawa, ciwon hanji na enteritis saboda gurɓacewar abin da bacterial contamination.

🔲 Ƙanƙara (Ice Block): da suke amfani da ita da yawanta wacce suke sayowa suna amfani da ita zaka ga bame cikakkiyar tsafta bace irin ta pure water. Kurum ƙanƙara ce da ba'a san irin ruwan da aka yi amfani da shi ba.

Galibi ruwan pampo ne wanda ba'a tafasa ba, wani borehole, wasu ba rijiya, kai wani ruwan yai kwana da kwanaki tare cikin roba....ita kanta robar ba murfi ba cikakkiyar tsafta, haka kuma masu ɗurawar suna yi suna wanko hannunsu ciki, wasu suna maganganu miyau na komawa ciki.

Infact naga ƙankarar da aka sayo aka sami ɓera cikin ruwan ya sandare, ku duba a comment section ba AI bane, sannan ga videos nan suma na aje a comments na yadda wasu matasa keta faman ƙulla ruwan da ake sakawa a mayar dashi ƙanƙara kusan wanke hannunsu da fallatsar miyau din bakinsu zuwa ciki ne kurum keta faruwa.

Kunga wannan yana sa ruwan ya zamto ɗauke da ƙwayoyin cuta irin su Salmonella (mai haifar da zazzaɓin Taifot/Typhoid) da E. coli (mai haifar da zafin ciki da gudawa/diarrhea).
..................................................................

🔲 Madara gari na buhu: Madarar buhu da ake ajiye wa a buɗe a shaguna tana saurin tara ƙura, ƙwari, da ƙwayoyin cuta kafin a zuba muku.


🔲 Wasu lokutan ana samun lalacewar ƴaƴan Itatuwa (Spoilage) kafin ma akai ga amfani dasu. Domin da zarar an yanka kankana, abarba, ko apple aka bar su a buɗe ko a cikin roba a waje batare da sasu cikin fridge mai sanyi sosai ba, suna saurin rubewa da tara ƙwayoyin cuta masu guba (food poisoning).

🔲Ga gubar robobi (Microplastics & Chemicals): Domin barin wadannan robobin na takeaway a cikin rana ko sanya sinadarai masu tsami (kamar abarba) a cikin robobin marasa dacewa da wannan amfanin, yana iya sa abincin ya tsotsi chemicals na sinadaran robobin da zai zamo hatsari ga jiki...................................................................

SANNAN A DUNƘULE BAKI ƊAYA

Komi sabunta da freshness na fruits mu sani, kwai fruits din ba'a haɗa sa da wani asha lokaci guda, idan ba haka ba, bazai aiki ba, saide asha ai kashi.

Kamar maganin asibiti ne ba'a haɗa wani da wani, likita zaka ji yana jan kunne, saboda in aka haɗu toh kode dukkansu kowanne yaqi aiki, ko kuma guda yai aiki ya bar ɗaya, ko duk su zamo matsala ga jiki wato DRUG TO DRUG INTERACTION..................................................................

To haka ma ƴaƴan itatuwa akwai NUTRIENT TO NUTRIENT INTERACTION kamar magunguna.

1- Misali; Hada abarba🍍 da madara kuskure ne, ka riga ka kashe protein tun kafin jiki ya tsotsesa ballantana ma ya shiga.

2- Madarar gari + kankana 🍉+ Ayaba🍌 wannan shima antagonistic effect kenan, ka hana jikinka ya amfana da sinadarin iron tare dana zinc, ina zaka shekara kana shan wannan hadin saide matsalar karancin jini, da rashin ƙarfin azzakari ta baibayeka, sannan sugar ta farma

3- Haɗa kwakwa 🥥+apple 🍏+ayaba 🍌 wannan shi syngergistic ne zai sa jikinka qara azama wajen tsotsa vitamins masu maiko a jika wato vitamin A,D,E,K toh amma ba ko yauhse hakan keda muhimmanci ba.

4- Haɗa Kankana 🍉 + Madara shima kuskure ne, Domin kankana tana cike da ruwa kuma tana sarrafa kanta da wuri inta shiga ciki. Amma idan ka haɗata da madara (powder milk ko creamer), sinadarin protein dake cikin madara yana ɗaukar lokaci mai tsawo kafin jiki ya iya sarrafa shi...
Wannan nasa narkewar kankana yai jinkiri har ya zamto ta fara tsami ko tsumuwa wato fermenting a cikin ciki kafin madarar ta bi jiki, wanda hakan ke haifar da kumburin ciki, iska (gas) ai ta tusa da gudawa.

5- Hakazalik kwai tauye darajar Ayaba da Kankana idan an haɗasu da Madara: Ayaba da kankana suna dauke da sinadarin Iron (mai gina jini da samar da jini) da Zinc (me taimakawa er****on ko sha'awa)... Amma MADARA tana ɗauke da sinadarin Calcium mai yawa.

Calcium ɗin yana toshe hanyar da jiki ke amfani da ita wajen shan Iron da Zinc, saboda haka jikinka ba zai samu cikekkiyar darajar Iron dake cikin ayabar ko kankanar ba.

6- Samun ƙaruwar Sikari da kitse (High Sugar & Fat Content); Domin madara condensed sweet creamer + powder Milk + Ayaba: Sweet creamer tana da sikari da kitse mai yawa, haɗa ta da powdered milk da ayaba (ita ma tana da sikari na halitta) yana sanya abincin yai nauyi sosai da sanya teɓa (weight gain) ko hauhawar sikari a jini lokaci guda.

Ballantana kuma ce ancakuɗesu duk guri guda Ayaba + Kankana + Kwakwa + Abarba + Apple + Sweet creamer + Powder milk + Ice blocks..... Just wow
..................................................................

SHAWARWARI DON TSARE LAFIYA

1. Haɗawa a Gida shine mafi a'ala, gara ku sayo waɗannan ƴaƴan itatuwan ku wanke su da tsaftataccen ruwa da gishiri ko tsami, ku yankasu daban-daban da kanku kusha a gida.

2. Zai fi kyau ka rarraba su, ya zamo haɗi na ƴa'yan itatuwa kawai: Kankana + Ayaba + Kwakwa (+ ƙankara). Wannan yana da kyau kuma yana taimakawa jiki shan sinadirai cikin sauki.

3. Ko haɗi na biyu me (Madara): Ayaba + Kwakwa + Powdered Milk/Creamer (+ Ƙanƙara - ice block). Domin Ayaba da kwakwa suna tafiya da madara sosai idan babu kankana🍉 a ciki.

4. A Guji zuba Condensed Milk ko madarar buhu mai yawa. Maimakon haka, zaka iya cin su a haka, ko ka zuba plain Yogurt (kindirmo marar zaƙi).

5. A Guji Ƙanƙarar waje: Musamman manyan nan ko ƴar ɗiba, Kada ku yadda a zuba muku ƙanƙara (ice block) na kasuwa. Idan kana buƙatar sanyi, sa haɗin a firijin gida ko ƙanƙarar pure water ko bottle water.

Irin wannan haɗin na kasuwa yana da daɗi kwarai a baki, amma yawan cin sa yana janyo matsalar hanta, ciwon sugar, da cututtukan kayan ciki.

Fatan an ilmantu

✍🏻
©Dr. Ibrahim Yakubu Yusuf

Mujiyar ABU
18/08/2026

Mujiyar ABU

Za'a Rina ai
17/08/2026

Za'a Rina ai

Address

Kiru Kofar Arewa
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ordinary Sheik posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ordinary Sheik:

Shortcuts

Share