Abdallah Amdaz

Abdallah Amdaz π„π±πœπžπ₯π₯𝐞𝐧𝐜𝐲 πŸŒπŸ•ŠοΈπŸ’° Singer β€’ Actor β€’ Writer β€’ Brand Ambassador β€’ Crypto analyst
(9)

13/11/2025

Absheer πŸ’ πŸ’ πŸ’Ž πŸ‘°

12/11/2025

A kowacce rana rayuwa Tana koyar da sabbin darasi, Allah ya bamu ikon koyon su cikin sauki, tare da aiki da su..

11/11/2025

Duk Wanda yasan darajar iyayensa bazai zagi wani ba, duk banbancin dake tsakaninsu, babu mai wulakanta iyayen wani sai Wanda ya wulakanta da nasa iyayen!

Idan kuna tunanin ta hanyar zagin iyayen juna zaku huce takaicin ku na kungiyoyin son zuciya go ahead the world is watching…

And also Allah is watching yana da sakamakon kowa, sannan mutuwa dai gaskiya ce koka yarda ko kada ka yarda dole zaka mutu.

I don’t care idan wani ya zageni coz kuna zagin wanda s**a fini daraja har a gurin Allah, gaskiya daya ce duk wanda zai zagi uban wani a raye ko a mace ko waye shi ba malami ko jahili ko mabiya ba, wallahi iyayensa da s**a haife shi yake zagi, sannan fasiki ne inji Manzon Allah SAW, ko ta muku dadi ko kar tayi muku zabin ku ne!

Allah yasa mu cika da imani, ya jikan wanda s**a rigamu gidan gaskiy, na daga iyaye da sauran yan uwa musulmi…

Life is not about waiting for the storm to pass, it's about learning to dance in the rain.
11/11/2025

Life is not about waiting for the storm to pass, it's about learning to dance in the rain.

TABBAS ABUL FATAHI BAUCHI BAYA KYAUTAWA!πŸ’”Amma hakan bai bada lasisin zagin mahaifiyarsa bayan ta mutu ba.Tabbas abubuwan...
11/11/2025

TABBAS ABUL FATAHI BAUCHI BAYA KYAUTAWA!πŸ’”Amma hakan bai bada lasisin zagin mahaifiyarsa bayan ta mutu ba.

Tabbas abubuwan da Abdul Fatahi Bauchi yakeyi yayin da bayin Allah s**a mutu, yaita surutai da fusata masoyansu, tare da nema musu mummunar makoma, hakan ba abu ne mai kyau ba, kuma abu ne wanda duk musulmin kwarai ya gani zai taba masa zuciya, indai kana da cikakken hankali.

To amma hakan bazai bude kofar fada masa haka ba, yayin da mahifiyarsa ta rasu, duk da cewa Dan Kuka shike janyowa Uwatai jifa, amma wannan ba koyarwar Annabi bace, kuma yin hakan ya sabawa musulunci, domin yin hakan shiga hurumin Ubangiji ne.

Muna addu’ar Allah ya gafartawa mahaifiyarsa, ya basu hakurin jure rashinta, shi kuma Allah yasa wannan ya zame masa darasi, wanda nan gaba bazai sake aikata abinda yayi ba, don nasani duk yanda wannan abun yakai ga bata min rai bai kai ya shida ya rasa mahaifiyarsa ba.

Lallai iyaye wani bango ne mai girma a gurin Allah Wanda rasasu kan taba zuciya matuka, wannan tasa muke ganin roko musu mummunar makoma ya saba da abinda Allah yayi mana Umarni…..

Suma masu biyewa maganganunsa suna ramuwa, Allah yasa su gane ba’a rama kuskure da kuskure, sannan mutum baya sabawa dokar Allah don ka fusata shi kaima ka saba.

Allah ya kyauta!

10/11/2025

Keda angonki ku zauna zama na amana πŸ’“βœŒπŸ»

09/11/2025

Ni Ina da wata tambaya data tsaya min a rai kuma nake ganin yakamata nayi, mai yiwa a samu wanda zasu karar dani ilimi.

Wai menene jahilci?, shin shi jahilcin da Mallam Bahaushe yake fada yana da babanci da asalin jahilci dani na sani ko guda biyu ne.

Saboda sai naga malami mai ilimi, wanda baki daya rayuwarsa ta tafi akan karantarwa da kokarin yada ilimi amma sai ace masa jahili, ko kaga wani mutumin da rubutun Hausa wannan wahala yake masa, b***e aje larabci ko turanci daka iya zama kishiyar Yaren Hausa, amma saiya kalli Professor ko Doctor sai yace masa jahili.

Wasu lokutan har zakalkalewa yake kai kace shi din wani Tammin mai ilimi ne a harkar addini ko a zamantakewa ta rayuwa.

Shin wai menene jahilcin nan Ina bukatar wani ya sanar dani, tunda dai yanzu Ina ganin kalmar jahilcin itama ta koma wani cin mutunci ba wai magana ake ta Mutumin da bashi da ilimi ba, Inkuma nine nayi kuskure sai a ganar dani.

Wata rayuwa matasan mu s**a dauka Indai kana da banbancin akida dasu ko malumansu, to kome zaka fada karyane bazasu taba yarda da shi ba, Babban illar shi ne duk tarin iliminka duk shekarunka a gurin su baka wuce aci mutuncinka ba.

Baka wuce karamin yaro ya zageka ba, wani ma ubanda ya haifeshin dalibinka ne , amma a gunsa kai jahili ne saboda kare muradun Wanda yakewa biyayya.

Allah ya shirya mana matasan mu su.

08/11/2025

Zagi, kazafi, cin mutunci shi ne babbar hanyar isar da nasu sakon, ai mai hujja a hannu bashi aibata kowa🀣 a sake tunani dai!

08/11/2025

Allah ya yarda rakumi yaci kayaβ€¦πŸ˜βœŒπŸ»

07/11/2025

Ina yi mana barka da wannan rana ta Juma’a ranar karatun Alqur’ani da Salatin Annabi Muhammad SAW musamman a wannan lokaci dake gabatowa na Karbar Addu’a Ubangiji yasa muna daga cikin bayi Nagari.

Wanda Allah ke farinciki da su!

Madallah da Web3 Madallah da zuwan lyrAI, wanda suke cikin wannan sabga ne zasu fahimta.Kwanaki sha tara 19 kacal s**a r...
06/11/2025

Madallah da Web3 Madallah da zuwan lyrAI, wanda suke cikin wannan sabga ne zasu fahimta.

Kwanaki sha tara 19 kacal s**a rage a gama wannan contest kada kayi wasa da damarka, gara ka danna linnk din kafara yanzu.

https://app.lyraxis.io?join=excellencyaamdaz241VC

Allah yaba mai rabo sa’a

Address

Abuja
900211

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abdallah Amdaz posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Abdallah Amdaz:

Share