12/04/2025
Kana Fama da Zafin Talauci? Da Rashin Ci Gaba a rayuwa?
Shiga ɗaki. Ka rufe ƙofa. Ka Kalli Madubi, Waye Ka gani cikin Madubin?
Wannan da kake kallo, shi ne wanda ke da alhakin mafarkin da bai cika ba. Shi ne mai laifin faduwar burin ka, ɗan lalaci, ɗan fargaba, wanda yake gaza tsayawa ya fuskanci rayuwa.
Dole Ka zage ka gaya masa maganganu kamar haka
"Na gaji da zama a haka. Idan ba zaka tashi ba, to zan bar ka a baya."
Dole Kabar Gida, Kabar Danginka kuma kayi Watsi da Abokanka.
Ka nemi inda babu wanda ya san kai. Ka hau t**in da babu fuskokin da s**a saba dakai,
Saboda gaskiyar magana ita ce:
“Ɗan Adam baya samun cikakken kuzari sai idan ya yi nesa da harshen da ya saba yi masa dariya, Sai a loƙacin zaka gane Dalilin da yasa Mai kuɗin Afirka "Aliko Dan-Gote" yabar Garinsa Kano kuma Yabar Mahaifiyarsa "Mariya Sunusi ɗantata, kuma Yabar danginsa Alasawa Masu tarin dukiya ya tafi Lagos don gina kansa.
Kamar yadda Ibn Khaldun ya ce:
“Rayuwa tana canjawa daga wuri zuwa wuri; wanda ya tsaya a wuri ɗaya, zai tsaya da cigaba.”
Kaje ka yi faɗa da rayuwarka a wajen da ba kowa ya san ka ba.
Ka yi aikin da baka taɓa tunanin zaka iya yi ba. Ka wanke mota, ka shara t**i, ka ɗauki kaya, ka zauna kasuwa – duk saboda makomar da kake so.
“Man is condemned to be free.” – Jean-Paul Sartre
(Mutum an haife shi da alhakin zabar makomarsa.)
Babu laifi a ƙasa, amma laifi ne ka zauna a ƙasa har ka ji daɗin zama, Kana jin Daɗin Zama Amma Aljihunka yana ƙonewa Kamar Kara a cikin Gobara.
Ka yi ta tattakawa akan wahalhalun da na jikin madubin nan bai so, Ka kakkarya shakkunsa. Idan ya ce "ka gaji", kai ce masa "gajiya ba naku bace".
Idan ya ce "za su yi min dariya", ka ce masa "to su yi tayi Har su Gaji.
Saboda:
> “The cave you fear to enter holds the treasure you seek.” – Joseph Campbell
(Ramin da kake tsoro shiga, shine ke ɗauke da dukiyar da kake nema.)
Mun fi aiki idan muka fita waje, saboda babu wanda ya san mu.
Babu ido, babu tsoron abin da za a faɗa. Muna zama kamar Ronaldo a cikin gasar Champions League – muna aikin da zai saka mu haskaka.
To me zai hana mu daina fargabar ido?
Ka tambayi zuciyarka: Shin kana rayuwa ne don jin daɗin mutane, ko don gina kanka?
Kafin ka fita daga madubin, ka ɗauki alkawari:
"Zan dawo nan in sake kallonka – amma da kyau da girma. Kai da nake gani a yau, zan sa ka zama abin da kowa zai so ya gani a gobe."