07/09/2024
MENENE Web 3.0 TECHNOLOGY & CRYPTOCURRENCY?
---------------------------------------------------------------------
Ba mamaki idan aka ce maka nan gaba zaka shiga harkokin BlockChain Technology da CryptoCurrency a yanzu kace a'a, domin baka yarda dashi ba, kuma ba zaka taba yarda dashi ba, a tunanin ka na yanzu, amma bari na share maka hanyar da zata nuna maka cewa guguwar BlockChain Technology da CryptoCurrency zata tattara har da kai nan gaba kadan.
Duk da cewa haryanzu Web 3.0 bai gama zama da Ζafafunsa ba, amma an wuce Web 1.0 da Web 2.0, yanzu an tsallaka zuwa Web 3.0 da Metaverse.
Wanda suke cewa babu ruwansu da BlockChain Technology da CryptoCurrency, a yanzu haka da muke magana guguwar Technology na Web 1.0 da Web 2.0 ya tafi dasu, ko kasan haka?
Wadannan kimiyyar sun kasu kashi uku kamar haka:
1. Information Networks.
2. Social Networks.
3. Money Networks.
Menene Web 1.0? Web 2.0 da Web 3.0 a takaice?...
1) Web 1.0:
Information Networks...
Web 1.0 shine zamanin da muka baro a baya wanda Information Networks s**a bayyana, wato irin su Google da rumbun bayanan duniya na Wikipedia, Yahoo da Search Engines.
Technology din Web 1.0 ne yazo da Browsing a computer da waya, da kuma kiran wayar handset da sakwannin Email.
2) Web 2.0:
Social Networks...
Shine technology din da yazo da Social media Networks, Facebook, Twitter, WhatsApp, Instagram, Telegram, 2GO, Nimbuzz, YouTube, Reddit da sauran su.
Wen 2.0 Technology ne na sadarwa a duniya, da isar da sakon hoto ko videos ko murya cikin sauki, da rubutun takardar na'aura wato PDF.
3) Web 3.0:
Money Networks...
Shine Technology din da yazo da BlockChain Technology, CryptoCurrency, NFTs, Metaverse da kuma DeFi Project Technology.
Wadannan sune CryptoCurrencies, Bitcoin, Ethereum, Stable Coins, DeFi, DAOs, NFTs, Metaverse da sauran su.
Wannan technology na harkokin kudi, da samun kudi, da juya kudade, da zagawar su cikin gaggawa a duniya, sune "Money Networks" bayan Information Networks da Social Network