
22/04/2025
MENENE GWAGWARMAYA ?
Nidai Umar Muazzam Lawan da farko idan kayi min tambayar menene GWAGWARMAYA kai tsaye zan baka amsa da cewa GWAGWARMAYA shine tsayuwa kan gaskiya da rikon amana gamida son tallafawa al'ummar dake bukatar taimako ta kowani janibi musamman masu bukata ta musamman.
Sannan ya zamo ka sadaukar da gabaki daya rayuwarka gurin aikin al'umma da kokarin yayewa al'umma wata damuwa data addabe su ko wayar wa da matasa kai gameda abunda zai iya zamowa illa garesu ayanzu ko anan gaba tareda dorasu a hanyar da zata inganta rayuwar su.
A takaice dai a kuma guntuwar fahimtata wannan shine GWAGWARMAYA.