25/06/2023
DATTIJO.
Marigayi Liman Yusuf Abubakar
✍🏻
COMRADE KABIRU AHMAD KWALLI
Marigayi Liman Yusuf Da ne ga Alhaji Abubakar Babba wanda yake shararren dan Kasuwa ne da yayi cinikayyar gyada a wancan lokachin, yana daga cikin wadanda s**a kafa garin Tsamiya Babba, kuma ya bayar da gudummawa kwarai wajen cigaban garin.
Garin Tsamiya Babba tsohon garine da ya kafu tun a zamanin Sarkin Kano Tsamiya.
An haifi Marigayi Liman Yusuf a garin Tsamiya Babba dake karamar hukumar Gezawa a yanzu, yayi karatun addini tsakanin Garin Tsamiya Babba da Garin Ringim ta jahar Jigawa a yanzu, yayinda dan uwan mahaifinsa ya tafi dashi chan, inda s**a zauna a gidan mahaifin shi Liman din kasancewar kamar yadda na fada mahaifinsa dan kasuwa ne hakan Tasa yayi gida a garin Ringim yadda idan yaje siyan gyada yakan sauka achan.
Liman Yusuf yaci gaba da neman ilmi a gaban dan uwan mahaifinsa mafi yawan masu yawan bada ilmi basa zama guri guda, daga nan s**an tafi zuwa wani garin Daban, hakan tasa wancan kanin mahaifi nasa, ya tashi zuwa Kasar Dutse Gadawur inda nan ma s**a zauna na wasu lokuta, haka yasa s**a dinga yawon karatu tsakanin Dutse, Jahun, Gwaram da Garin kila duk a jihar ta Jigawa a yanzu.
Liman Yusuf ya dawo gida Tsamiya Babba inda ya fara makarantar Elementary bayan gama yaci gaba da Gwagwarmayar neman ilmin Fikhu, Hadisai, Tauhidi da sauran Littattafan addinin Musulunci.
Liman Yusuf ya shafe shekaru a firamare har ya kammala.
Liman yanada abokai da s**a tashi tare a Garin Tsamiya Babba ga kadan daga ciki.
(1) Alhaji Abdulkadir Isa.
(2) Alhaji Magaji Jafaru kanine ga Mahaifinsa kuma shine yake Sarautar Garin Tsamiya Babba a yanzu.
Aiki da Hukumar Bada Wutar Lantarki ta Kasa.
Liman Yusuf ya fara aiki da hukumar bada wutar Lantarki ta Kasa wato Electricity Company of Nigeria dake Challawa a Kano, ya zauna tare da Turawa a waccan hukuma, Liman Yusuf Allah yayi masa baiwar iya lissafi.
Liman a zamansa da yayi a waccan hukuma sai da yazama duk wani sabon Maaikachi Dan Boko da za'a kawo ana hadashi da Liman Yusuf domin ya nuna masa yadda ake gudanar lissafi cikin sauki, ba tare da Na'urar lissafi ba, Liman Yusuf mutum ne jajirtacce akan duk abinda yasa a gaba gwani Wajen Lissafi domin bana mantawa akwai wani rabon gado da magadan s**ace basa bukatar aje kotu, liman shine ya jagoranci wancan rabon Gado kuma akayi lafiya cikin Aminci.
Liman Yusuf ya shafe shekaru goma sha biyu 12 yana aiki da waccan hukuma daga baya yabar aiki ne lokachin da ita waccan hukuma ta koma izuwa NEPA, shine yaci gaba da gudanar da harkokin gaban kansa yayinda ya fara harkokin agent na Alhazai tare da Alhaji Usman Jallaba.
Liman Yusuf manomi ne kasancewarsa ya fito daga gidan da ake aikin Noma tukuru, kuma Kasancewar sa ya gaji wasu gonaki a gurin mahaifinsa da kuma wadanda ya siya na kashin kansa. Hakan tasa bai ajiye wancan Gado nasu ba na aikin Noma.
Limanchi da hidima ga al'umma.
Tabbas Liman Yusuf jigo ne matuka wajen yiwa jama'a hidima a yankin Indabawa, Kurmawa, da Unguwar Gini domin ya kasance duk wani lamari na aure, Rasuwa, Rada suna za'a ga Liman Yusuf ne a gaba haka lamarin ya taho har ya fara Limanchi.
Liman Yusuf ya fara Limanchi ne tun a Masallachin waccan hukuma yayinda yake jan sallar Azhar da La'asar, haka yaci gaba da hidimar al'umma daga baya Marigayi Mallam Tukur Yakasai (Mahaifi ga su Shugaban jami'ar Wudil na yanzu) ya gayyace shi ya zama limami a Masallachin jikin gidansa, bayan rasuwar Mallam Uzairu Limamin Masallachin na Farko, haka Liman Yusuf yaci gaba da Limanchi.
Liman Yusuf ya kasance ya samu shakuwa da mafi yawan manyan Unguwar su wanda daga baya Wakilin Kudu na wancan lokachin yabashi umarni cewa duk wani Masallachi da za'ayi Liman toh ya kasance Liman Yusuf ne zai duba cancantarsa sai ya Sanarwa wakilin kudu,
sannan shine yake ajiye bayanai Record na dukkan Sunan da aka rada a masallatan yankin daga nan sai ya mika zuwa ofishin wakilin kudu.
Liman Yusuf yana daga cikin wadanda s**ayi fadi tashi wajen ganin ansamu filin wannan Masallachi da ya rasu yana Limanchi tare da taimakon wasu daga cikin mutanen Unguwa irinsu Marigayi Alhaji Umar Makaman Agaye mai Sarauta ne a jihar Neja wanda shine kakan Alhajin Ali Banufe, Wakilin Kudu, da Alhaji Usman Jallaba, da sauran wasu mutanen unguwa.
Mai karatu zai so yaji wani abin Al'ajabi daya faru a wancan lokachin wajen gina wancan Masallachi na filin Kurata, wanda yafara gina Masallachin har aka gama, a gidan Alhaji Mustapha yake Haya wato shine Alhaji Balan Uda saboda kyakkyawar zuciya da neman dumbin lada.
Hikimar bayyana irin wadannan Abubuwa shine domin muyi koyi da ayyukan magabata.
Wancan bawan allah Bai rasu ba sai da Allah yayi masa arziki mai yawa, yayinda ya cigaba da rayuwa a Unguwar Koki. Akwai Alhaji Shu'aibu Abdulkarim shima ya bada gudummawa sosai wajen kammaluwar wancan Masallachi, Alhaji Jazuli Gaya da sauran Jama'ar unguwa.
Bayan haka bayanai sun nuna Alhaji Muhammad Tara Gana shine mai kula da aikin wancan Masallachi da aka gina a tsakanin shekarar 1977 zuwa 1978. Allah yasaka musu da alherinsa.
Bayan wasu shekaru sai Jama'ar unguwa irinsu Alhaji Ibrahim Kurawa, (Saja Ibrahim) s**a ga cancantar fadada Wannan Masallachi daga bangaren gwamnati a shekara ta 2009 bayan gwamnati ta rushe domin fadada shi anfara gini ba'a kammala ba gini ya dakata . Amma daga baya sai Iyalan Gidan Alhaji Jazuli Gaya, Iyalan Gidan Gado da Masu, Iyalan Gidan Mallam Nura Alkali, da sauran bayin Allah sun dauki nauyin karasashi zuwa matsayin da yake a halin yanzu.
Liman Yusuf ya cigaba da bayar da karatu ga al'umma irinsu Fikhu, Hadisai, Tauhidi da sauran Littattafan addinin Musulunci a matsayinsa na Babban limami a wannan yanki.
Liman Yusuf ya kasance shugaban zauren Sulhu na yankin Indabawa, Kurmawa da wani yanki na Unguwar Gini haka akai ta fama hara bayan rasuwar sa daga baya zauren sulhu yakoma Wajen Marigayi Khadi Muhammad Umar.
Liman Yusuf yana da Abokai wadanda sun shaku kwarai da gaske ga kadan daga cikinsu.
(1) Alhaji Shu'aibu
Abdulkarim.
(2) Alhaji Attahir (Kawu)
(3) Alhaji Mahe Abdulkadir Yakasai
(4) Mallam Yusuf
(5) Mallam Usman Na'ibi
(6) Mallam Uzairu
(7) Alhaji Ilu.
(8) Alhaji Yahuza.
(9)Alhaji Lawan Adamu Babar bare
(10) Alhaji Mahe
Liman Yusuf ya shaku da yan uwansa matuka da gaske ga kadan daga cikinsu.
(1) Alhaji Amadu Mai yadi.
(2) Alhaji Shehu Tsamiya.
Liman Yusuf yayi zama na amana da makota kuma suna girmama juna ga kadan daga cikin su.
(1) Alhaji Barde Gaya
(2) Alhaji Ya'u Danbatta
(3) Alhaji Ibrahim Dutse (Dallatun Dutse)
(4) Alhaji Basiru Dutse (Galadiman Dutse)
(5) Alhaji Ibrahim Chanki Chas
(6) Alhaji Sule Ringim
(7) Alhaji Ibrahim Kurawa (Saja Ibrahim)
(8) Alhaji Jazuli Gaya (Katukan Gaya)
(9) Alhaji Bello Gada
Liman Yusuf yayi rayuwa cikin aminci da kaunar Jama'a Liman Yusuf duk yayinda ya fito zaije wani waje yana samun gaisuwa daga mafi yawan jama'a saboda girmawawa.
Liman ya rasu a ranar 25/5/2008 shekaru Goma sha biyar 15 da s**a gabata, tabbas rasuwar Liman Yusuf ya girgiza Mazauna waccan unguwa da wajenta wannnan Bawan Allah ya tara masuyi masa Jana'iza da yimasa addu'a, Tabbas rasuwar Liman wani babban gibi ne acikin al'umma, domin baya shakkar fadar gaskiya komai dacinta.
Liman Yusuf ya rasu yabar yaya da jikoki da dama.
Alhamdulilah Nasamu wadannan bayanai ta hannun Alhaji Shehu Tsamiya, da Alhaji Muhammad Tara Gana
da wasu daga cikin makotansa.
Muna addu'a Allah yajikansa da rahama ya gafartawa dukkan iyayenmu idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani.
✍🏻
COMRADE KABIRU AHMAD KWALLI
Alhamis.
22/6/2023 AD
4/11/1444 AH