Jaridar Kannywood

Directions

Jaridar Kannywood Journalist
(1)

Daga ƙarshe Samha M. Inuwa ta fara aiki da sabuwar wayar da Baby ya kawo mata. IPHONE 18.
21/09/2026

Daga ƙarshe Samha M. Inuwa ta fara aiki da sabuwar wayar da Baby ya kawo mata. IPHONE 18.

Da ɗumi-ɗumi: An naɗa mahaifiyar tsohuwar jarumar Kannywood Rahama Sadau a matsayin Sarauniyar Kadaure.An naɗa mahaifiya...
15/09/2026

Da ɗumi-ɗumi: An naɗa mahaifiyar tsohuwar jarumar Kannywood Rahama Sadau a matsayin Sarauniyar Kadaure.

An naɗa mahaifiyar tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, a matsayin Sarauniyar Unguwar Kadaure da ke yankin Millennium City, cikin garin Kaduna, a jiya Asabar.

Me za ku ce?

Tirkashi G Fresh ya taro Amaryarsa Sadiya Haruna a Airport bayan ta dawo daga Umarah.Wata sabuwar alaqa ta sake kunnuwa ...
08/07/2026

Tirkashi G Fresh ya taro Amaryarsa Sadiya Haruna a Airport bayan ta dawo daga Umarah.

Wata sabuwar alaqa ta sake kunnuwa tsakanin G Fresh da Sadiya Haruna, kamar yadda kuke gani a wannan hoton G Fresh ne ya taro Sadiya Haruna daga Filin tashi da saukar jirage bayan dawowarta daga Umarah, inda ya dafata tare dayi mata barka da zuwa.

Shin me zaku ce?

Ramadan Booth Ya Fice Daga Triple R, Ya Bayyana Dalilan Da S**a Sa Ya Dauki MatakinFitaccen jarumin Kannywood, Ramadan B...
03/07/2026

Ramadan Booth Ya Fice Daga Triple R, Ya Bayyana Dalilan Da S**a Sa Ya Dauki Matakin

Fitaccen jarumin Kannywood, Ramadan Booth, ya sanar da ficewarsa daga kungiyar Triple R, yana mai bayyana cewa daga yanzu ba shi da wata alaka da kungiyar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ramadan Booth ya ce ya shiga kungiyar ne da kyakkyawar niyya domin tallafa wa talakawa, kare adalci da kuma taimakon marasa galihu.

Sai dai ya bayyana cewa bayan nazari da kuma shawarwari daga na kusa da shi, ya yanke shawarar ficewa daga tafiyar saboda abin da ya fahimta game da kungiyar.

Jarumin ya kuma yi kira ga abokan aikinsa na Kannywood da su rika yin nazari sosai kafin shiga kowace kungiya ko tafiya, tare da duba manufarta da irin amfanin da za ta kawo wa al’umma.

A karshe, Ramadan Booth ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa fahimtarsa da kuma abin da ya gani, yana addu’ar Allah Ya sanya alheri a cikin lamarin.

Na rabu da Amani saboda bata da mafaɗa - Bilal VillahMatashin mawaƙi a masana'antar nishadi ya bayyana cewa abinda yasa ...
03/07/2026

Na rabu da Amani saboda bata da mafaɗa - Bilal Villah

Matashin mawaƙi a masana'antar nishadi ya bayyana cewa abinda yasa ya rabu da tsohuwar budurwa Amani shi ne bata da mafaɗa, an saba ganinsu tare musamman lokacin da suke soyayya.

Hakan ya fito ne bayan hira da akayi da shi.

Shim me zakuce?

Tsohuwar jaruma Zainab Booth mahaifiyar Maryam Booth ta cika shekara 5 da rasuwaKuyi mata addu’a
02/07/2026

Tsohuwar jaruma Zainab Booth mahaifiyar Maryam Booth ta cika shekara 5 da rasuwa

Kuyi mata addu’a

02/07/2026

Fati KK itama ta fice daga Ƙungiyar Triple R

Ficewarta ta zama a jerin mutane huɗu da s**a fice daga ƙungiyar.
Mansurah Isah, Ibrahim Birniwa, Yusuf Saseen dukkansu sun fice daga ƙungiyar.

Shin kome Yayi Zafi

Ƙungiyar Triple R ta kori Yusuf Saseen daga cikin ƙungiyarShin me zaku ce?
02/07/2026

Ƙungiyar Triple R ta kori Yusuf Saseen daga cikin ƙungiyar

Shin me zaku ce?

Mutane 2 a Kannywood da s**a yi abin alheri amma aka caccake suA cikin 'yan kwanakin nan, an ga wasu fitattun mutane a K...
30/06/2026

Mutane 2 a Kannywood da s**a yi abin alheri amma aka caccake su

A cikin 'yan kwanakin nan, an ga wasu fitattun mutane a Kannywood sun yi ayyukan alheri da s**a yi zaton za su amfani al'umma, amma sai s**a fuskanci s**a daga wasu mutane.

Na farko akwai Abdurrazaq Sultan, wanda ya gina Film House a unguwar Dorayi da nufin samar da guraben aiki da kuma taimakawa matasan yankin. Sai dai wasu daga cikin mazauna unguwar s**a nuna rashin amincewarsu da shirin, lamarin da ya kai ga fitowarsa ya sanar da janye aikin.

Na biyu kuma ita ce Mome Gombe, wadda ta gina masallaci a garinsu tare da waƙafa ladan ga iyayenta. Duk da kyakkyawar manufarta, ta fuskanci s**a daga wasu mutane, har ma wani malami ya yi mata kalamai da s**a jawo ce-ce-ku-ce.

Tambayar ita ce: Shin idan mutum ya yi abin da yake ganin alheri ne, amma wasu s**a ƙi karɓarsa ko s**a soke shi, hakan yana nufin ya yi kuskure ne? Ko kuwa ba za a taɓa rasa masu s**a ba komai kyawun niyya?

Menene ra'ayinku kan wannan batu? 🤔

Address

Kano
700104

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Kannywood posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share